An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jiragen yakin Saudiya na ci gaba da kai hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na kasar Yemen A yau lahadi jiragen yakin hadin gwiwa kalkashin jagorancin saudiya sun lugudar wuta a  kan gidajen fararen hula  a yankin Ali makna’a dake jihar Sa’ada, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutane 19 tare da jikkata wasu mutane wasu yawa. Har ila yau jiragen yakin saudiyan su kai hari a barikin soja na Ashu’ula da kuma bututun iskar gaz na yankin Marib dake tsakiyar kasar ta yemen A bangare guda dakarur kasar yemen gami da na sa kai na ci gaba da kwobza fada tare da mayakan ‘yan ta’addar IS masu samu goyon bayan saudiya a kusa da garin Adan dake kudancin kasar Majiyar tsaron yemen ta tabbatar da cewa dakarun tsaron kasar sun halba rokoki kimanin guda 10 a barikin sojin malaha dake yankin Jizan na kasar saudiya a jiya Assabar
Published in Gabas Ta Tsakiya
Sojojin kasar Yamen da suke samun tallafin mayakan kungiyar Huthi sun yi nasarar halaka ‘yan kungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida da masu goya musu baya kimanin 180 a cikin daren jiya.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Dakarun tsaron kasar yemen sun ce za su mayar da martaki matukar kasar Saudiya ta karye yarjejjeniyar tsagaita wuta da aka cimma. Tashar telbijin ta kasar Yemen Almasira ta gwado kakakin dakarun kasar Sharaf Lukman na cewa mun yi na’am da yarjejjeniyar tsagaita wutar da aka cimma, amma matukar Gwamnatin ta saudiya ta karya yarjejjeniyar za mu mayar da martani mai karfi.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Kungiyoyin bada agaji suna gaggauta shirin isar da taimako ga miliyoyin mutanen kasar
Published in Top News
Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya koka kan matsalar ci gaba da take hakkin bil-Adama a kasar Yeman.
Published in Top News
A ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da kasar Saudiya ke kaiwa kan al’ummar kasar yemen fiye da mutane 70 suka yi shahada a jiya litinin. Tashar telbijin Almanar ta kasar Lobnon ta gwado yadda jiragen yakin na masarautar Al sa’oud suka yi lugudar wuta a wata kasuwa dake kudu maso gabashin garin Imran a daren jiya Litinin, lamarin da yayi sanadiyar shahadar Mutane 35 da kuma jikkata wasu 50 na daban
Published in Gabas Ta Tsakiya
Duk da cewa babban saktaren MDD Banki Moon ya sanar da cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta  na kwanaki 5 a kasar Yemen, amma jiragen yakin saudiyar sun ci gaba da lugudar wuta kan gidajen fararen hula a kasar ta yemen A yau lahadi, jiragen yakin saudiya sun kai wasu jerin hare-hare kan gidajen fararen hula a yankin Sufyan dake jihar Imran na arewa maso yammacin kasar ta yemen
Published in Gabas Ta Tsakiya
Sojojin kasar Yemen sun cilla makaman linzami kan wasu sansanonin sojojin kasar Saudia a jiya Laraba.
Published in Top News
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban ki Moon ya bayyana cewa bin hanyoyin tattaunawa da sulhu ne kawai zai kawo karshen rikicin da ake fama da shi a kasar Yemen.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Mutane 16 suka yi shahada a wasu sabbin hare hare wadanda jiragen yakin kasar saudia suka
Published in Top News