An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jiragen yakin masarautar Al sa’oud na ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Al’ummar kasar Yemen. Wata majiyar Asibitin kasar yemen ta habarta cewa akalla fararen hula 10 ne suka rasu daga cikinsu 6 iyalan gida guda ne sakamakon hare-haren wuce gona da irin da jiragen yakin saudiya suka kai a garin Sa’ada. Har ila yau jiragen yakin na masarautar Al sa’oud sun tsananta kai hare-hare a gariruwan Alhadida dake yammacin kasar da kuma yankin Ab dake kudancin kasar.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Majalisar dinkin duniya ta yi gargari ga kasashen saudia da kawayenta kan mummunan sakamakon killace kasar Yemen da suka yi.
Published in Top News
Za a yi masayar fursunar yaki tsakanin kungiyar Ansarulla ta kasar Yemen tare da magoya bayan hanbararen shugaban kasar Abdu Rabahu Mansur Hadi dake rike da yankin Adan na kudancin kasar. Wannan shiri zai gudana ne kalkashin jagorancin shugaban kwamitin kungiyar Bada Agajin gaggawa wato Red Cross Mr Peter Maurer. Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto wani jami’in kungiyar gwagwarmaya ta kasar Yemen a yau Litinin na cewa za su bayar da firsinoni 7 ne daga cikin magoya bayan na tsohon shugaban kasar, inda suma za a sako masu mutanan 7 da aka kame a kudancin kasar. Rahoton ya ce wani jirgin kungiyar Red Cross ne zai kwashe magoya bayan tsohon shugaban kasar daga birnin Sana’a zuwa yankin Adan dake kudancin kasar.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Dakarun tsaron kasar Yemen sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 40 a jihar Lahaj. Kamfanin dillancin labaran kasar Yemen Saba ya nakalto Ma’aikatar tsaron kasar na cewa dakarun tsaron sa kai sun hallaka ‘yan ta’addar Alka’ida da kuma masu goyon bayan saudiya 14 tare da jikkata 25 na daban daga cikinsu a jihar Lahaj.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Sojojin gwamnatin Yemen da mayakan kungiyar Ansarullahi ta mabiya Houthi sun halaka ‘yan ta’adda akalla 30 a yankin Kudu maso yammacin kasar Yeman.
Published in Top News
Makiya mutanen yemen ne a karshe zasu yi asara a yakin da kasar saudia da kawayenta suka dorawa mutanen kasar.
Published in Top News
Jakadan babban saktaren Majalisar dinkin duniya a kasar yemen ya gana da sakateren kungiyar kasashen larabawa kan yakin na Yemen.
Published in Top News
Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun kaiwa Sojin kasar Saudiya hari a garin Najran dake iyaka da kasar ta yemen A wani hari dake a matsayin mayar da martani na karya yarjejjeniyar tsagaita wuta na kwanaki biyar daga kasar Saudiya , dakarun gwagwarmayar yemen sun cinna rokokin kirar Katiyusha a guraren sojojin saudiyar dake cikin garin Najran mai iyaka da kasar ta Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Sojin saudiya guda tare da jikkata wasu biyu na daban.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Mahukuntan Saudiyya suna ci gaba da kai hare –haren wuce gona da iri kan kasar Yamen duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta na bangare guda.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Ministan tsaron kasar saudiya ya ce za su tsananta kai hare-hare a kasar yemen Bayan wata ganawa da ya yi tare da manyan jami’an tsaron kasar a yau, ministan harakokin tsaron saudiya Muhamad bn Salman ya ce za su tsananta kai hare-hare a kasar ta yemen ko da kasar za ta shafe daga doron kasa. Ministan ya ce kasarsa za ta yi amfani da dukiyarta domin tabbatar da siyasar masarautar Al’sa’oud, kuma yanzu za su bukaci taimakon wasu kasashe domin samun karin sojojin sama musaman ma wadanda suka kware wajen kai hare-hare ta sama.
Published in Gabas Ta Tsakiya