An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jiragen yakin kasar Amurka wadanfa ake sarrafasu daga nesa sun kai hare hare a wasu wurare a kudanci da
Published in Top News
Dakarun tsaron kasar yemen sun mamaye yankin Arrubu’a dake kudancin kasar Saudiya. A wani rahoto da gidan telbijin din Almasira na kasar ta Yemen ya fitar a yau, ya ce a matsayin mayar da martani kan hare-haren wuce gona da iri da kasar saudiya ke kaiwa kan Al’ummar kasar Yemen, Dakarun tsaro gami da Dakarun sa kai sun kai hari kan sananin Sojin Saudiya na Kashba, Hasan, wafaya, da kuma Sahwa dake yankin Arrubu’a na jihar Asira, inda suka hallaka Sojojin Saudiya tare da mamaye yankin na Arrubu’a, har ila yau sun sanar da tarwatsa tankokin yaki na Dakarun Tsaron Saudiyar 17 a yankin na Arrubu’a.
Published in Gabas Ta Tsakiya
A dai dai lokacinda manzon majalisar dinkin duniya na musamman kan rikicin kasar yemen yake bada sanarwan
Published in Latest
Jiragen yakin Saudiyya sun kaddamar da wasu munanan hare-hare a kan yankin Dal’a da ke cikin gundumar Ta’iz a kasar Yemen, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula akalla 45, tare da jikkatar wasu da dama.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya kan garin Ibb da ke kudancin kasar Yeman sun yi sanadiyyar shahadar mutane akalla 12 tare da jikkata wasu 54 na daban.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tsananin damuwarta kan yadda hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya da kawayenta suke ci gaba da rusa gidajen jama’a a kasar Yamen.
Published in Top News
Dakarun tsaron kasar Yemen sun samu narar rusa wani shirin ta’addanci na kungiyar IS a birnin Sana’a fadar milkin kasar Tashar telbijin Al’alam wacce ke watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a ci gaba da kokarin da dakarun tsaro, dakarun sa kai,da hukumar leken asirin kasar ke yi , a yau Alkhamis hukumar leken asirin kasar sun gano wani shirin ta’addanci da ‘yan ta’addar dake samun goyon bayan saudiya suka shirya a birnin sana’a fadar milkin kasar.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa cewa da Red cross ta sanar da dakatarda ayukan ta na wani dan lokaci a birnin Aden na kasar Yemen bayan wani hari da wasu mayaka da ba’a san ko suwa ne ba suka kaiwa offishin na ta na Aden. Kamar yadda Kakakin kungiyar ta red cross Rima Kamal ta sanar ga kanfanin dilancin labaren faransa na AFP ta ce wasu mutane ne daukeda makami suka farmawa offishin nasu a Aden inda suka kwashe masu kayan aiki da kuma kudade. Hakan a cewar ta ya cilasta masu dakatarda aiki na dan wani lokaci A Aden din birni na biyu mafi girma a kasar ta Yemen. Hakazalika jami’ar ta kara da cewa tuni aka kwashe dukkan ma’aikatan kungiyar 14 wadanda ‘yan asalin kasashen waje ne, inda aka nufi dasu wasu biranen kasar saboda kare lafiyar su.
Published in Gabas Ta Tsakiya
 Masarautar Al sa’oud na ci gaba da kai hare-haren ta’addanci kan Al’ummar kasar Yemen. A wannan talata jiragen yakin saudiya sun kai jerin hare-hare a yankunan jahohin Marib da Sa’ada da kuma tsibirin Alhadida, lamarin da ya yi sanadiyar fashewar wani abu a tsibirin, inda lamura suka tsaya cik a wannan tsibiri.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Akalla Mutane 10 ne suka rasa rayukansu sanadiyar hare-haren wuce gona da iri da jiragen yakin saudiya ke kaiwa kan Al’ummar kasar Yemen Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habarta ce a jiya Assabar jiragen yakin saudiya sun yi lugudar wuta kan gidajen fararen hula a garin Harad dake jihar Hajjah, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutane 10 tare da jikkata wasu da dama na daban.bayan haka jiragen yakin na masarautar Al sa’oud sun kai wasu jerin hare-haren har so uku a yankin Sakka dake jihar Ib, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 4 tare da jikkata wasu da dama na daban.
Published in Gabas Ta Tsakiya