An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan wasu yankunan kasar Yamen lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 19 tare da jikkatan wasu fiye da 30 na daban.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Babban sakataren majalisar duniya Ban Ki Moon ya yi Allawadai da hare-haren da jiragen yakin saudiyya suka kai kan asibitin kungiyar likitoci na kasa da kasa a garin Ta’iz na kasar Yemen.
Published in Top News
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na Lijanus-Sha’abi na mabiya Huthi sun kwace iko da Tsaunin Jablu-Majbur da ke gabashin Babul-Mandab na kasar Yamen.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Fararen hula 16 ne suka rasa rayukansu a jiya 14 daga cikinsu mata, a hare-haren da jiragen yakin kasar Saudiyyah suka kai kan biranan Ta’iz da San’a na kasar Yemen.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Jiragen yakin Saudiyya suna ci gaba da kai hare-hare akan kasar Yemen. Tashar Telbijin din almasirah ta ‘yan Huthy ta  bada labari a jiya laraba cewa; Jiragen yakin Saudiyyar sun kai hare-hare akan yankunan fararen hula da ke gundumar al-Baidhaa a kudancin kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar da dama. A yankin Sa’adah ma dai jiragen yakin na Saudiyyar sun kai hare-haren da su ka dauki rayukan farafen hula masu yawa. A gefe daya sojojin kasar ta Yemen tare da hadin guiwar mayakan Ansarullah sun maida martani akan mayakan da Saudiyyar ta ke goyon baya a gundumar Lahaj tare da kashe 20 daga cikinsu. Watanni 8 kenan a jere da Saudiyyar ta bude yaki da al’ummar Yemen, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka masu yawa.
Published in Top News
Mayakan kungiyar Ansarullahi ta kasar Yamen sun yi nasarar halaka sojojin mamayar Saudiyya da na kawayenta masu yawa a sansanin al-Omari da ke arewa da mashigar Bab al-Mandeb a jiya Litinin.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Kwamitin Kolin Juyin Juya Halin Yamen ya bukaci gudanar da zanga-zangar gama gari a duk fadin kasar domin yin Allah wadai da makircin Mahukuntan Saudiyya na hada kai da Yahudawan Sahayoniyya wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yamen.
Published in Top News
Dakarun tsaron yemen sun samu nasarar tarwatsa wani jirgin ruwan yaki na kasar Saudiya dake kai hare-haren cikin kasar Kamfanin dillancin Labaran Saba na kasar yemen ya nakalto wata majiyar tsaro na cewa dakarun tsaro sun halba wani makami mai lizzami a kan wani jirgin ruwan yaki na kasar saudiya dake tekun Almakha a jiya Lahadi tare da samun nasarar tarwatsashi.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Rahotanni daga kasar Colombia sun ce masarautar Saudiyya ta dauki hayar wasu sojojin kasar domin taya ta yaki kan al’ummar kasar Yemen.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Gwamnatin kasar Mauritania ta musanta zancen cewa tana shirye shiryen tura sojojin kasar zuwa kasar Yemen don tallafawa sojojin saudia a
Published in Top News