An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan ya jaddada cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da tsayin daka da kuma kokarin da take yi na taimakon al’ummomin da gwamnatocin Gabas tsakiya wajen fada da ta’addanci da kuma mamaya.
Published in Iran
Dubun dubatan al’ummar kasar kasar Yemen a garuruwa daban-daban na kasar ne suka fito kan tituna don gudanar da wata gagarumar zanga-zangar Allah wadai da ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya take kai wa kasar bugu da kari kan tofin Allah tsine da takunkumin da MDD ta sanya wa ‘yan kungiyar Ansarullah.
Published in Latest
Gwamnatin Rasha ta fara tuntubar gwamnatocin wasu kasashe domin neman hanyar warware rikicin kasar Yemen.
Published in Top News
Daruruwan ‘yan kasar Yemen suna ci gaba da kwarara gudun hijira zuwa kasar Djibuti domin tsira da rayukansu daga hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya da kawayenta.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Tun bayan da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya fitar da kudiri mai lamba 2216 kwanaki uku da suka gabata dangane da rikicin kasar Yemen, bangarorin siyasa da masana a kasar ta Yemen suke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu dangane da wannan kudiri.
Published in Sharhi
Jiragen yakin masarautar Al-Sa’oud na ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar kasar Yemen. Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ya habarta cewa a jiya Laraba jiragen yakin saudiya sun yi lugudar wuta kan gidajen fararen hula a yankunan Karitar, Khur makasar da kuma wasu anguwani na garin Adan, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma  jikatta fararen hula da dama,har ila yau sun  kai hari kan guraren ma’ajiyar Man fetur, shaguna, gidagen fararen hula, da kuma babbar asibitin garin sa’ada,lamarin da ya janyo mutuwar fararen hula da dama.
Published in Gabas Ta Tsakiya
      Masarautar Saudiyya tare da taimakon Amurka, na ci gaba da kaddamar da hare-hare na kan mai uwa da wabi a kan birane da kauyuka  akasar Yemen, da sunan yaki da 'yan kungiyar Alhuthi
Published in Gabas Ta Tsakiya
Kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi da ke kasar Yemen ta yi Allah wadai da kudurin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan kasar ta Yemen.
Published in Top News
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin da kasashen Larabawa da suke yankin tekun Pasha suka gabatar kan kasar Yemen.
Published in Top News
Dubun dubatar mutane na gudanar da zanga-zanga a dukkanin birnanan kasar Yemen a yau, domin yin tir da Allawadai da hare-haren da masarautar Al Saud ke kaddamarwa a kansu.
Published in Gabas Ta Tsakiya
Page 19 of 19