An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 14:26

Kasashen Da Suka Amince Da Kotun Duniya Mai Shari'ar Manyan Laifuffuka

Kasashen Da Suka Amince Da Kotun Duniya Mai Shari'ar Manyan Laifuffuka
Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

 

Yanzu kuma bari mu je ga tambayarmu ta gaba wacce ta fito daga mai saurarenmu Abubakar Musa daga kasar Sudan wanda ya ce sakamakon irin ci gaba da kace-nacen da ke gudana tsakanin kungiyar Tarayyar Afirka da kotun kasa da kasa mai shariar manyan laifuffukan yaki (ICC a takaice), yana son sanin kasashen nawa ne na duniya suka amince da ita wannan kotun,sannan kuma shin dukkanin kasashen Afirka sun amince da kotun ne wanda hakan ya ba ta damar cin kashi ga shubannin Afirkan kamar yadda ya ce:

 

To Malam Abubakar Musa daga Sudan mun gode kwarai da gaske da wadannan tambayoyi naka da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu a daidai lokacin da muke kokarin amsa maka wadannan tambayoyi naka. Sai ka biyo mu don jin abin da muka tanadar maka.

 

Da farko dai dangane da kasashen da suka amince da wannan kotu ta kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuffukan yaki, to muna iya cewa kasashe 121 ne suka amince da ita sakamakon sanya hannu kan yarjejeniyar birnin Roma wanda ita ce ta kafa kotun da wadannan kasashen suka yi sannan kuma suka ci gaba da girmama yarjejeniyar don kuwa akwai wasu kasashen da sun amince da yarjejeniyar Roma amma kuma sun ki su amince da kotun. Daga cikin irin wadannan kasashen kuwa da suka amince da yarjejeniyar Roman amma suka ki amincewa da kotu sun hada har da Amurka, wacce ta rattaba hannu kan yarjejeniyar birnin Roman amma kuma ta ki amincewa da kafa kotun bayan da majalisar kasar ta ki kada kuri’ar amincewa da kafa kotun.

 

Haka nan kuma daga cikin kasashen da ba su amince da kotun ba har da kasar Rasha da China da kuma HKI.

 

Idan kuma muka koma ga bangaren nahiyar mu ta Afirka wacce a hakikanin gaskiya ita ce kotun ta fi yi mata dirar mikiya sannan kuma shugabannin nahiyar Afikan suke ci gaba da korafi kan hakan, kasashe 33 daga cikin 54 na Afirkan ne suka amince da kotun sauran kuma da suka hada da Sudan da Ivory Coast da Libiya da Mauritaniya da sauransu ba su amince da kotun ba.

 

Malam Abubakar Musa daga Sudan wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wannan tambaya taka da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. Ka huta lafiya.

 

---------------------------------------/

 

END

Add comment


Security code
Refresh