An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 14:17

Tarihin Kungiyar Al-Shabab Ta Kasar Somaliya

Tarihin Kungiyar Al-Shabab Ta Kasar Somaliya
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa muku wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako. Da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya, kuma za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

Tambayarmu ta farko ta fito ne daga mai saurarenmu Haladu Hamidu, kakuri, Kaduna-Nigeria wanda ya ce yana son sanin tarihin kungiyar nan ta Al-Shabab na kasar Somaliya da take yaki a kasar da kuma kasar Kenya.

 

---------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa da fatan kuna cikin koshin lafiya, sannan shi ma mai tambaya din Malam Haladu Hamidu daga Kaduna yana tare da mu musamman a daidai lokacin da muke kokarin amsa masa wannan tambaya tasa.

 

Ga abin da muka tanada dangane da wannan tambayar:

 

Ita dai wannan kungiya ta Harakat al-Shabab al-Mujahidin (wato kungiyar Matasa Mujahidai) da aka fi sani da sunan Al-Shabab (wato matasa a larabce) kungiya ce ta wasu matasa a kasar Somaliya da suke da alaka da kungiyar nan ta Al-Qa’ida wasu ma suna bayyana ta a matsayin bangaren kungiyar ta Al-Qaida a kasar Somaliya.

 

Kungiyar kuwa ta samo asali ne sakamakon rikicin da ya barke a kasar Somaliyan tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Mohammed Sa'id Bare a shekara ta 1991inda kasar ta ta fada cikin yakin basasa da ke ci gaba da janyo hasarar rayukan jama'a a kasar. Tun dai bayan barkewar wannan rikicin kungiyoyi daban-daban na kasa da kasa musamman MDD sun yi kokarin shiga cikin rikicin da magance shi amma dai sun gagara lamarin da ya sanya al’ummar kasar komawa ga hukumomin addini domin warware takaddama da ta shafi harkokin kasuwanci da na zamantakewa da sauransu ta hanyar bullo da wasu kotuna na shari'a da ke kula da wadannan batutuwa. Su dai masu gudanar da wadannan kotuna sun hada kansu waje guda inda suka kafa abin da suka kira Ittihad al-Mahakim al-Islamiyya (Islamic Courts Union – ko kuma hadin gwiwan kotunan Musulunci) karkashin jagorancin Sharif Sheikh Ahmad, wanda daga baya ya zamanto shugaban kasar, don fada da gwamnatin rikon kwarya da aka kafa a kasar ta Somaliya. Har zuwa shekara ta 2006 kuwa sun sami nasarar rike madafan ikon mafi yawa daga cikin garuruwan kudancin kasar da suka da garuruwa Jawhar, Kismayo da sauransu. A karshe-karshen shekara ta 2006 ne dai gwamnatin kasar Ethiopian wacce take samun goyon bayan kasashen yammaci ta sami nasarar fatattakan ‘yan kotunan Musuluncin daga yankunan da suke rike da su ciki kuwa har da babban birnin kasar Mogadishu inda suka koma garin Kismayo a can din ma an kore su.

 

Irin wannan kashin da ‘yan kungiyar Kotun Musuluncin suke ci gaba da sha ne ya haifar da rikici a tsakaninsu inda wasu suka balle suka kafa kungiyoyi masu tsaurin ra’ayi da suka hada da Al-Shabab din da kuma Hizbul Islam.

 

Wannan shi ne mafarin kafa kungiyar ta Al-Shabab a wajen shekara ta 2007.

 

Kungiyar ta ci gaba da wanzuwa a dunkule har zuwa shekara ta 2009 lokacin da sojojin kasar Ethiopia suka fice daga Somaliyan inda aka fara samun rarrabuwan kai a cikinta musamman tsakanin masu tsaurin ra’ayi da masu sassauci na cikin kungiyar lamarin da ya kai masu sassaucin ficewa daga cikin kungiyar. Bayan ficewar ta su wadanda suka rage din, mayaka ne da ke da akidu irin na kasa da kasa, wadanda ke karban umarni daga kungiyar al-Qa'ida.

 

 Irin yadda kungiyar ta rungumi akidar Al-Qa’ida da kuma fadar da ta kaddamar kan sauran kungiyoyi na musulmi na kasar musamman masu ra’ayin sufanci bugu da kari kan hare-hare da sace mutane da dai sauran ayyukan ta’addanci da ake zargin kungiyar ta aikatawa, wadanda wasu daga cikinsu ita kanta kungiyar ce take sanar da cewa ita ce ta aikata su da suka hada da irin hare-haren da take kai wa kasar Kenya da Ethiopia dukkanin wadannan abubuwan sun sanya kasashen duniya kaddamar da wani shiri na ganin bayanta da kuma bayyana ta cikin kungiyoyin ta’addanci na duniya.

 

Ita dai wannan kungiyar ta kumshi kabilu daban-daban na kasar Somaliyan ne wanda ake zargin shugabanninta sun fito ne daga wasu ‘yan kasar da suka sami horo a kasar Afghanistan ko Iraki a wajen kungiyoyi masu tsaurin ra’ayi. Duk kuwa da cewa mafi yawan kungiyar ‘yan kasar Somaliyan ne amma ana zargin akwai wasu ‘yan kasashen waje musamman wadanda suka fito daga kasashen larabawan Tekun Fasha cikin dakaru da kuma shugabannin kungiyar.

 

Kungiyar dai tana amfani da hanyoyi sadarwa musamman na sada zumunci irin su facebook da twitter wajen yada ayyukanta da kuma janyo hankulan matasa zuwa shiga kungiyar, kamar yadda kuma take amfani da irin matsalar da kasar Somaliyan take ciki da suka hada da fari wajen janyo hankulan mutane zuwa gare ta. A ranar 9 ga watan Fabrairu 2012 ne kungiyar, ta bakin daya daga cikin jagororinta Mukhtar Abu Al-Zubair Godane, ta sanar da shigarta kungiyar Al-Qa’ida a hukumance da kuma yin mubaya’a ga Ayman Al-Zawahiri shugaban kungiyar bayan kashe Usama Bn Ladin. Wannan sanarwar dai ta janyo rikici cikin kungiyar musamman bayan da Godane ya bukaci a saura sunan kungiyar daga Al-Shabab zuwa kungiyar al-Qa’ida a gabashin Afirka. Lamarin da ya raba kungiyar zuwa gida biyu, wato bangaren Godanen da bangaren sauran jagororin kungiyar. Wannan rikici dai ya haifar da zubar da jinni tsakanin ‘yan kungiyar. Bangaren Godanen dai ya yi ta kokarin kame jagororin daya bangaren da yanke musu hukumcin kisa lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wasu jagororin daya bangaren ciki kuwa har Ibrahim Afghani da dai sauransu. Wasu ma suna ganin harin da aka kai wa cibiyar kasuwanci na Westgate na birnin Nairobin Kenya yana daga cikin irin rikicin da ke cikin kungiyar inda kowa yake kokarin tabbatar da ikonsa a kan dan’uwansa. Kamar yadda kuma aka sami rarrabuwan kai tsakanin kungiyar da babbar kawarta ta Hizbul Islam saboda sauyin siyasa da kungiyar ta Al-Shabab ta yi inji jagororin kungiyar ta Hizbul Islam.

 

Kasashen duniya daban-daban irin su Amurka da Australiya da Kanada da Norway sun sanya kungiyar cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya.

 

Wasu rahotannin sun ce mayakan kungiyar sun kai mayaka dubu 400 zuwa 600 sannan kuma wajajen da kungiyar ta fi gudnar da ayyukanta su ne kasashen Somaliya, Uganda da Kenya.

 

Malam Haladu Hamidu wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wannan kungiyar  da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. ka huta lafiya.

 

Masu saurare kafin mu je ga tambayarmu ta gaba ga abin da ke bisa inji.

Add comment


Security code
Refresh