An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 14:12

Bayani Dangane Da Katangar Berlin

Bayani Dangane Da Katangar Berlin
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa muku tambayoyin da kuka aiko mana ta hanyoyin da kuka saba saduwa da mu wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi, da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

Ba tare da bata lokaci ba, tambayar mu ta farko a cikin shirin ta fito ne daga wajen mai saurarenmu Abubakar Yahaya Geidam jihar Yobe wanda ya aiko da tambayarsa ta hanyar adireshinmu na email kamar haka: Don Allah ku ba ni tarihin katangar Berlin da ke Tarayyar Jamus.

 

------------------------------------------/

 

To Malam Abubakar Yahaya Geidam jihar Yoben Nigeria mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu musamman a daidai wannan lokaci da muke kokarin amsa maka wannan tambaya. Sai ka gyara zama don jin abin da muka tanadar maka.

 

Da farko dai yana da kyau a san cewa batun tarihin katangar Berlin da ma batun gina ta yana komawa ne ga abin da ya faru a yakin duniya na biyu da kuma abubuwan da suka biyu bayan wannan yakin da aka gwabzashi na tsawon shekaru shida wato daga 1939 zuwa 1945 sakamakon yadda manyan kasashen duniya da suka yi nasara a yakin suka yi watandar kasar Jamus din. Wadannan kasashe kuwa sun hada da Amurka Da Birtaniya da Rasha (wato Tsohuwar Tarayyar Sobiyeti) da Faransa. Wadannan kasashen dai sun yi tunanin cewa bayan gamawa da kasar Jamus karkashin shugabanta Adolt Hitler wajibi ne saboda wasu dalilai su rarraba wannan kasar. Daga cikin dalilan akwai akidarsu ta fadada ikonsu da kuma watakila tsoron da suke da shi na cewa barin Jamus din a hade zai iya zama musu barazana don mai yiyuwa ne wani daga cikin ‘yan siyasan Jamusawan yayi tunanin sake kaddamar da wani yakin. Don haka suka raba kasar Jamus din zuwa gida hudu a tsakaninsu. Duk kuwa da cewa wasu bayanan suna nuni da cewa kasashen Amurka da Birtaniya da Tarayyar Sobiyetin ne suka fara raba Jamus din a tsakaninsu sai kuma daga baya ne suka shigo da Faransa ciki inda suka raba ta gida hudu maimakon uku na farko. Har ila yau kuma shi ma birnin Berlin a matsayin helkwatar wadannan yankuna da wadannan kasashe suke gudanar da mulkinsu, shi ma an kasa shi gida hudu duk kuwa da cewa yana bangaren da aka ware wa Tarayyar Sobiyetin ne.

 

Tun ba a je ko in aba aka fara samun rikici da Baraka tsakanin wadannan kasashen musamman tsakanin Tarayyar Sobiyeti a bangare guda a daya bangaren kuma sauran kasashe ukun. Kasashe ukun dai suna zargin Tarayyar Sobiyeti  da kin amincewa da wani tsari da suka gabatar da zai sanya Jamus ta zamanto mai dogaro da kanta. Don haka aka ta samun sabani tsakanin Rasha da sauran kasashe ukun, wato Amurka, Birtaniya da Faransa. Hakan ne ya sanya kasashe uku suka yanke shawarar hade yakunansu uku wuri guda suka zama Jamus ta Yamma. Hakan kuwa ya faru ne a shekarar 1949.

 

Ganin hakan kuma ita ma Tarayyar Sobiyeti sai ta maida nata yankin Jamus ta Gabas. To sai dai ta fuskanci wata matsala. Wannan matsala kwua ita ce cewa mazauna Jamus ta Gabas din sun kasance cikin matsalolin rayuwa lamarin da ya tilasta musu gudu zuwa Jamus ta Yamma. Wasu bayanai sun bayyana cewar tsakanin 1949 zuwa 1961 (wato lokacin da aka gina wannan Katanga ta berlin sama da mazauna Jamus ta Gabas miliyan uku ne suka gudu zuwa Jamus ta yamma. Hakan ya sanya mahukuntan Jamus ta Gabas din tunanin cewar matukar ba su dau mataki ba, to kuwa mutane gaba dayansu za su gudu saboda mawuyacin halin da suke ciki. Wannan yanayi ne ya sanya Rashawan karkashin jagoransu Joseph Stalin fara tunanin hanyoyin da za a bi wajen hana wannan kwararar da mutanen Jamus ta Gabas din suke yi zuwa Jamus ta Yamma.

 

A daya daga cikin irin zaman da suke yi ne don tattaunawa hanyoyin magance wannan matsalar, ministan harkokin wajen Tarayyar Sobiyeti Vlacheslav Molotov ya ba da shawarar cewa mutanen Jamus ta gabas din su fara tunanin shata kan iyakansu da Jamus ta Yamma sannan kuma wajibi ne su ci gaba da gadin wajen. Da haka ne aka fara shata wannan kan iyakan da kafa shingen karfe don hana ‘yan gudun hijirar fita. Annan shi ne mafarin gina wannan Katanga ta Berlin.

 

Haka dai lamarin ya ci gaba har zuwa lokacin da aka fara gina wannan Katanga ta Berlin a shekarar 1961 da nufin hana kwararar mutanen Jamus ta gabas zuwa ta Yamma. Tsawon lokaci dai an ta yi wa wannan katangar kwaskwarima. Don kuwa katangar ta fara ne da sanya shinge na waya a shekarar 1961. Daga nan kuma daga shekarar 1962-1965 aka kara sanya wani shingen wayan mai karfin gaske. Daga shekarar 1965-75 kuma aka gina Katanga ta kankare. Sannan daga 1975-89 kuma aka kara karfafa wannan katangar.

 

Sai dai kuma duk da an gina wannan katangar an yi mata mashiga tara don wucewar mutanen da aka ba su izinin wucewa.

 

Mai yiyuwa ne wani yayi tambayar cewar mutanen da ba a ba su izinin wucewa ba, ya ya suke yi sannan shin an samu mutanen da suka yi kokarin wucewa kuwa. To za mu amsa wadannan tambayoyin bayan mun dawo. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

--------------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

To dangane da wadannan tambayoyi lalle tsawon wadannan shekaru da wannan katangar ta yi an ce an sami kimanin mutane 5000 da suka ketare katangar zuwa bangaren Yammacin musamman yammacin Berlin. Har ila yau kuma an samu wani adadi na mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kokarin da suka yi wajen ketarewan. Babu wani takamammen adadi, to amma dai wasu sun kama daga mutane 100 zuwa 200, duk kuwa da cewa an hukumance an ce mutane 98 ne suka rasa rayukansu wasu ta hanyar bindige su da aka yi saboda gwamnatin Jamus ta gabas din ta ba da umurnin bude wuta kan duk wanda ya yi kokarin tsallakewa. Da farko dai mutanen da suke son tsallakewar suna amfani da tagogin gidajen da suke makwabtaka da katangar ce ko kuma wayar da aka kafa wajen fadawa daya bangaren, to amma daga baya dai hakan ta gagara saboda kara fadada katangar da aka yi da kuma hana yin gine-gine a kusa da ita.

 

Mutum na farko da ya fara rasa ransa a yayin gudun ita ce wata mace mai suna  Ida Siekmann, ta mutu ne bayan ta fado daga gidanta mai hawauku. Sannan mutum na farko da aka harbe a yayin gudun shi ne wani tela mai suna Gunter Litfin. Har ila yau wasu kuma sun yi amfani da ramuka da suke tonawa wajen gudu.

 

Wannan katangar dai ta ci gaba da wanzuwa har zuwa shekarar 1990 lokacin da aka rusa katangar gaba dayanta sannan kasashen Jamus biyun, wato Jamus ta gabas da ta yamma suka hade waje guda. Hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon zanga-zangar jama´ar dake zaune a bangaren Jamus ta Gabas suka ta yi na neman ‘yancin kansu da damar walwalawa ta kai da komo tsakanin Jamus da ta Gabas da ta Yamma. An ta gudanar da irin wadannan zanga-zangogi ne kuwa a birane da garuruwa daban-daban. Hakan ya tilasta wa yin sassauci da bude kan iyakoki.

 

Wannan zanga-zangar dai ta tilasta wa gwamnatin Jamus ta Gabas yin murabus ranar 8 ga watan Nuwamba 1989. A bangare guda kuma an kara sassauta matakan hana tafiya zuwa Jamus ta yamma daga Jamus ta gabas din.

 

A ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1990 kuma aka shirya zaben 'yan Majalisar Dokoki a Jamus ta Gabas inda bayan watanni sabuwar Majalisar ta rattaba hannu kan dokar sake hadewar Jamus. Hakan ya share fagen taron da aka gudanar a birnin Mosko na kasar Rasha, tsakanin kasashen da suka ci yakin duniya na biyu da kuma shugabanin Jamus ta Gabas da ta Yamma domin rattaba hannu kan yarjejeniyar hadewa ranar 12 ga watan Satumban 1990. Sannan kuma a ranar 3 ga watan Oktoba na shekara 1990 ne aka tabbatar da hadewar.

 

----------------------------------------------/

 

To a takaice malam Abubakar Yahaya Geidam jihar Yobe wannnan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wadannan tambayoyi nata da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. Ka huta lafiya.

 

Masu saurare da haka ne kuma muka kawo karshen shirin na mu nay au sai kuma a mako na gaba.

 

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuku.

Add comment


Security code
Refresh