An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 14:05

Tarihin Mullah Muhammad Umar

Tarihin Mullah Muhammad Umar
To Malam Sani daga kasar Cote’D’Ivore mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu a daidai lokacin da muke amsa maka wannan tambaya taka.

 

 

To ga abin da muka tanadar maka dangane da wannan tambaya taka da kake son sanin tarihin shugaban kungiyar Taliban Mullah Muhammad Umar:

 

Cikakken sunansa dai shi ne Muhammad Umar Mujahid bn Maulawi Ghulam Nabi Akhund, ya fito ne daga kabilar Hootak wadanda suke garin Khandahar. An haife shi ne a shekarar 1960 a kauyen Nuri dake yankin Kandahar. Mahaifinsa, wato Maulawi Ghulam Nabi, ya kasance malami ne na addini kana kuma limamin masallacin garin Noorin.

 

Mulla Umar ya tashi ne a matsayin maraya don kuwa tun yana shekaru uku mahaifinsa ya rasu don haka ya tashi ne a wajen baffansa Maulvi Muhammad Anwar bayan da ya auri mahaifiyar Mulla Umar din. Mulla Umar ya fara karatunsa na firamare ne a wajen baffansa wanda ya kasance limami ne na garin inda ya karanci Alkur'ani mai girma, hadisai da kuma fikihu. Daga baya kuma ya ci gaba da karatu a wajen wasu malaman na daban. A shekarar 1978, a lokacin da tsohuwar tarayyar Sobiyeti ta shigo cikin kasar Afghanistan, Mulla Umar ya kasance daga cikin matasan kasar da suka fito don fada da dakarun Sobiyetin da nufin fatattakarsu daga kasar. A yayin wannan gwagwarmaya dai sojojin Sobiyetin sun raunana Mulla Umar har sau biyu, inda a na farkon suka lalata masa kafa sakamakon harbin da suka yi masa, a na biyun kuma ya fuskanci ruwan albarusai ne inda suka ji masa munanan raunuka. Bayan da ya samu sauki Mulla Muhammad Umar ya koma fagen daga, a nan ma dai sojojin Rashan sun sake ji masa ciwo inda har ya rasa idonsa guda daya. Bayan korar sojojin Rasha daga kasar Afghanistan Mulla Umar ya sake komawa makaranta don karo ilimi. A wancan lokacin ne ma ya yi aure.

 

Bayan fatattakan sojojin Sobiyetin daga kasar, maimakon lamurra su yi kyau a kasar Afghanistan din sai kuma batun neman mulki ya shigo cikin zukatan wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin mujahidai da suka yi fafutuka, su kuwa makiya suka sami kafar shigowa. A daidai wannan lokacin ne kasar Amurka, wacce da man ta jima tana taimakawa mujahidan wajen ganin sun fatattakin tsohuwar tarayyar Sobiyetin wacce ta zamanto musu karfen kafa a wajen, ta shigo da dukkan karfinta, hakan kuwa da nufin samun iko sosai a kasar da kuma hana su kansu mujahidan da sauran al'ummar Afghanistan tsara wa kansu rayuwa. A wannan lokacin ne Amurka ta dinga hada baki da wasu kungiyoyin da tursasa wasu, a bangarre guda kuma ta hada baki da kungiyar leken asiri ta kasar Pakistan don cimma wannan manufa da take da ita a kasar Afghanistan din.

 

To daga nan ne batun kafa kungiyar Taliban ya taso. Don haka ana iya cewa an kafa kungiyar Taliban din ne a shekarun 1993-94 ko kuma kungiyar ta fara gudanar da ayyukanta bisa goyon baya da kuma taimakon kasar Amurka da kasar Pakistan don biyan bukatun kasar Amurka inda suka ci gaba da fada da sauran kungiyoyin da suka yi gwagwarmayar kawar da sojojin mamayan tsohuwar tarayyar Sobiyetin. A shekarar 1996 ne ‘yan kungiyar Taliban din suka kama babban birnin kasar Afghanistan, Kabul, a takaice dai suka kama kasar da kafa ikonsu a mafiya yawa daga cikin yankunan kasar, inda Mulla Muhammad Umar ya zamanto jagoransu kuma mai shiryar da su. Tun daga wancan lokacin har zuwa lokacin da gwamnatin Bush ta Amurka ta mamaye kasar Afghanistan Mulla Muhammad Umar ya ci gaba daga zama shugaban wannan gwamnati, sannan kuma har ya zuwa yanzu ya ci gaba da zama shugaban kungiyar Taliban din duk kuwa da cewa ya ci gaba da buya a cikin kasar tun bayan mamayan. Bisa la'akari da irin yanayi da kuma akidar da ‘yan kungiyar Taliban din suka rika, samun cikakken bayani kan da dama daga cikin jami'ansu lamari ne mai wahala, musamman ma shi Mulla Umar din wanda ya kasance a boye sannan kuma ba a ma ba da dama a tattauna da shi ko kuma daukan hotonsa. Ala kulli hal dai babu wani rahoto da ke nuna cewa ya mutu ko an kashe shi, kai bil’hasali ma cikin ‘yan watannin nan akwai wasu bayanai da suke fitowa da akejingina su gare shi dangane da batun shirin tattaunawar sulhu da kungiyar ta Taliban take yi da gwamnatin Afghanistan da Pakistan. Haka nan kuma batun inda ya ke kan babu wani bayanin da ya fito da ke nuni da takamammen inda yake kamar yadda muka bayyana a baya, sai dai kuma wasu suna cewa yana nan a yankuna masu duwatsu na kasar Afghanistan kusa da kan iyakan kasar Pakistan.

 

Malam Sani daga Ivory Coast wannan shi ne abin da muka tanadar maka da fatan ka gamsu. Mun gode sai mun sake ji daga gare ka. ka huta lafiya.

 

--------------------------------------/

 

END

Add comment


Security code
Refresh