An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 13:56

Tarihin Shugaban Kungiyar Taliban Ta Pakistan Hakimullah Mehsud

Tarihin Shugaban Kungiyar Taliban Ta Pakistan Hakimullah Mehsud
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa muku amsoshin da kuka aiko mana wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan kuna cikin koshin lafiya, kuma za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

Ba tare da bata lokaci ba bari mu je ga tambayarmu ta farko a cikin shirin wacce ta fito daga mai saurarenmu Alh. Ali Kiragi Gashuwa, jihar Yoben Nigeria wanda ya tubuta mona wasikarsa ta adireshinmu na email yace: Don Allah ku bai tarihin marigayi madugun kungiyar Taliban a yankin arewacin Waziristan (na kasar Pakistan) Mr. Hakimullah Mehsud da Amurka ta kashe shi a ranar 1 ga watan Nuwamban 2013.

 

----------------------------------------/

 

Masu saurarenmu musamman mai tambaya Alh. Ali Kiragi mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu musamman a daidai wannan lokaci da muke kokarin amsa maka wannan tambaya taka. Sai ka gyara zama don jin abin da muka tanadar maka.

 

Shi dai Hakimullah Mehsud, wanda da farko ake kiransa da Jamshid Mehsud ko Zulfiqar Mehsud an haife shi ne a shekarar 1979 a yankin Kotkai na kusa da garin Jandola da ke yankin Waziristan na kasar Pakistan kimanin shekaru 33 zuwa 34 kenan da suka gabata.

 

Hakimullah Mehsud ya yi karatunsa ne a makarantar addini na gargwajiya da lardin Hangu inda a nan ne ma tsohon shugaban Taliban na Pakistan din Baitullah Mehsud wanda shi ma Amurka ta kashe shi ya yi karatun nasa.

 

Bayan wasu shekaru na karatun, Hakimullah Mehsud ya shiga cikin kungiyar jihadi wanda Baitullah Mehsud ya kafa inda ya zamanto daya daga cikin masu gadin Baitullah din sannan kuma daya daga cikin masu ba shi shawara. Baitullah Mehsud ya yi fice ne a cikin kungiyar ta Taliban ta Pakistan da aka fi sani da Tehrik-i-Taliban Pakistan saboda kwarewar da yake da ita wajen sarrafa bindigar yaki musamman bindigar nan ta AK-47.

 

A shekara ta 2004 kungiyar ta Taliban ta Pakistan ta nada  shi a matsayin kakakinta. Har ila yau kuma a tsakanin shekarun 2007-2008 ya jagoranci wasu hare-hare da aka kai wa sojojin Amurka lamarin da ya tilasta aka rufe hanyar nan ta Khyber Pass da sojojin Amurkan suke amfani da ita wajen wucewa da kayayyakinsu. Hakan ne ma  ya sanya a shekara ta 2008 aka ba shi matsayin kwamandan yankunan Orakzai, Khyber da Kurram.

 

Hakimullah Mehsud ya ci gaba da rike wannan matsayin har zuwa ranar 22 ga watan Augustan 2009 lokacin da majalisar shura ta kungiyar ta Taliban mai wakilai 42 ta zabe shi a matsayin sabon shugaban kungiyar ta Taliban ta kasar Pakistan a lokacin yana dan shekaru 28 a duniya bayan kashe shugaban kungiyar Baitullah Mehsud da Amurka ta yi sakamakon wani hari da aka kai masa, duk kuwa da cewa a lokacin ‘yan Taliban din ta bakin kakakinsu Hakimullah Mehsud din ya musanta mutuwar tasa da bayyana cewar yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya ne. Daga baya dai kungiyar ta Taliban ta tabbatar da mutuwar Baitullah Mehsud din sakamakon harin da Amurka ta kai masa da makamai masu linzami a gidan daya daga cikin sirikansa a lokacin da ya kai masa ziyara.

 

Tsawon wannan lokacin dai Hakimullah Mehsud ya jagoranci kai hare-hare kan jami’an tsaro da fararen hula na kasar Pakistan lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wani adadi mai yawa na kashe mutane mafiya yawansu fararen hula da ba su ci ba su sha ba bugu da kari kan sace mutane da kungiyar take ci gaba da yi. Hakan ne ya sanya gwamnatin kasar Pakistan sanya ladar dala dubu 600 ga duk wanda ya taimaka wajen ba ta bayanan da za  su ba ta damar kama shi ko kashe shi. Kamar yadda ita ma gwamnatin Amurka ta sanya shi cikin gungun sunayen manyan ‘yan ta’adda na duniya da kuma sanya dala miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka mata kama shi.

 

Daga karshe dai a ranar 1 ga watan Nuwamban shekarar nan ta 2013 ne, bayan samun wasu bayanan sirri, gwamnatin Amurka ta sami damar kashe Hakimullah Mehsud ta hanyar kai masa hari da wani jirgi mara matuki a gidansa da ke kauyen Dande Darpa Khel da ke arewacin Waziristan na kasar ta Pakistan.

 

Gwmanatocin Pakistan da Afghanistan sun bayyana rashin jin dadinsu kan wannan kisa da Amurka ta yi wa shugaban na Taliban suna masu cewa hakan zai yi kafar ungulu ga shirin zaman lafiya da suke kokarin kullawa da kungiyar ta Talaiban.

 

Alhaji Ali Kiragi wannan shi ne abin da muka tanadar maka a takaice dangane da tarihin rayuwar tsohon shugaban kungiyar ta Taliban Hakimullah Mehsud. Da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. ka huta lafiya.

 

-Masu saurare kafin mu je ga tambayarmu ta gaba ga abin da ke bisa inji.

Add comment


Security code
Refresh