An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 13:50

Bayani Kan Kungiyar Taliban Ta Kasar Pakistan

Bayani Kan Kungiyar Taliban Ta Kasar Pakistan
Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

 

Tambayarmu ta gaba ta fito ne daga wajen mai saurarenmu Abubakar Musa daga Zariya jihar Kadunan Nijeriya wanda ya ce yana son karin bayani kan kungiyar nan ta Taliban ta kasar Pakistan.

 

To Malam Abubakar Musa mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya ga abin da muka tanadar maka dangane da wannan tambaya taka.

 

Ita dai wannan kungiya ta Tehreek-e-Taliban Pakistan ko kuma wacce aka fi sani da Pakistan Taliban (Taliban ta kasar Pakistan) wata kungiya ce mai dauke da makami mai tsaurin ra’ayin addini wacce mafiya yawan membobinta dalibai ne na makarantun addini wadanda kuma suka sanar da yaki kan gwamnatin kasar Pakistan bayan kafa ta a shekara ta 2007.

 

Tushen kungiyar yana komawa ne ga lokacin da Amurka da gwamnatin Pakistan suke tattaro matasa da sunan Mujahidai da nufin yakar tsohuwar Tarayyar Sobiyeti a kasar Afghanistan a shekarun 1980. Mafi yawa daga cikin wadannan mujahidin sun koma sun shiga kungiyar Taliban ta Afghanistan, amma da dama daga cikinsu ‘yan kasar Pakistan sun koma gida wato yankunan kabilun kasar. Bayan da Amurka ta kaddamar da yaki a kan Afghanistan da mamaye kasar, wadannan mayakan sun sake tasowa da nufin goyon baya da kuma taimakawa ‘yan Taliban na Afghanistan wadanda daman tushensu guda ne. Wasu daga cikinsu sun tafi Afghanistan din don yaki a can wasu kuma sun tsaya a gida suna yakar gwamnatin kasar saboda goyon bayan da take ba wa Amurka da kuma kungiyar NATO wajen ci gaba da mamaye Afghanistan da kuma hare-haren da suke kai wa kan ‘yan kungiyar Taliban da ci gaba da kashe jagorori da membobinta.

 

Da farko dai, wadannan mayakan kowanne guda daga cikinsu yana gudanar da aikinsa ne bisa ‘yanci ba tare da dogaro da wani bangare ba, karkashin wani kwamanda guda na yankin da suke. To amma daga baya a shekara ta 2007, kungiyoyi 13 daga cikinsu sun hadu da kafa kungiya da wannan suna na Tehreek-e-Taliban Pakistan karkashin jagorancin Baitullah Mehsud wanda ya zamanto shi ne babban kwamandan mayakan a lokacin bayan mutuwar Nek Muhammad wanda sojojin Amurk suka kashe shi.

 

Ita dai wannan kungiya tana gudanar da ayyukanta a dukkanin yankunan kabilun kasar ta Pakistan su 7 kuma an ce suna da mayakan da ba su gaza 30,000 ba wadanda suka watsu yankuna daban-daban na Pakistan da ma Afghanistan sannan kuma suke ci gaba da kai hare-hare kan gine-gine na gwamnati musamman na jami’an tsaro da kuma cibiyoyi wdanda ba na gwamnati ba musamman na wadanda suke da sabani da su a bangaren akida da tunani. Irin wadannan ayyukan ne ya sanya wasu kasashen yamamci irin su Amurka da Birtaniya da Kanada da kuma kwamitin tsaron MDD sanya su cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya, sannan ita ma gwamnatin Pakistan ta haramta kungiyar.

 

Ita dai wannan kungiya ta Taliban ta Pakistan ta kulla alaka da kawance da kungiyoyi na ‘yan ta’ada masu tsaurin ra’ayi da suke gudanar da ayyukansu na ta’addanci a Pakistan din da suka hada da kungiyar nan ta Lashkar-e-Jhangvi da Sipah-e-Sahaba, kungiyoyi biyu masu tsananin adawa da Shi’anci wadanda kuma suke da hannu cikin hare-haren ta’addancin da ake kai wa tarurruka da wajajen ibadu na ‘yan Shi’a. Har ila yau kuma da kungiyoyi irin su Lashakar-e- Tayyaba da Jaish-e-Muhamma da Lashkar-e-Islam da sauransu kungiyoyin ta’addanci da suke gudanar da ayyukansu a Pakistan.

 

Ita dai wannan kungiya ta Taliban ta Pakistan ta yi kaurin suna wajen kai hare-haren ta’addanci da ya yi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutanen Pakistan mafiya yawansu fararen hula da ba su ci ba su sha ba.

 

Shugaban kungiyar na farko shi ne Baitullah Mehsud wanda Amurka ta kashe shi a wani hari da ta kai masa da jirgin sama mara matuki a ranar 23 ga watan Augustan 2009 inda daya daga cikin dalibansa Hakimullah Mehsud ya dare karagar mulkin kungiyar shi ma dai Amurkawan ne suka kashe shi a watab Nuwambar bara (2013), shugaban kungiyar na yanzu shi ne Khan Sajna Said.

 

Malam Abubakar Musa wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wannan tambaya taka da fatan ka gamsu. Sai mun sake ji daga gare ka. Ka huta lafiya.

 

--------------------------------/

 

END

Add comment


Security code
Refresh