An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 13:47

Yakukuwan Da Aka Yi A Zamanin Manzon Allah (s)

Yakukuwan Da Aka Yi A Zamanin Manzon Allah (s)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa muku tambayoyin da kuka aiko mana ta hanyoyin da kuka saba saduwa da mu wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan kuna cikin koshin lafiya.

 

 

To yau ma ga mu da wani sabon shirin inda za mu masa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko din.

 

Ba tare da bata lokaci ba bari mu je ga tambayarmu ta farko a cikin shirin inda mai tambayar Malam Iliyasu Mato daga kasar Kamaru wanda ya bugo mana waya ya ce yana son ya san yakukuwa nawa aka yi a lokacin Manzon Allah (s.a.w.a).

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Mai tambaya Malam Iliyasu Mato daga Kamaru mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu musamman a daidai lokacin da muke kokarin amsa maka wannan tambaya taka.

 

Ga abin da muka tanadar maka.

 

Da farko dai yana da kyau a san cewa malaman tarihi sun raba yakukuwan da aka yi a lokacin Ma’aiki (s.a.w.a) zuwa biyu akwai wanda suke kira da larabci ‘al-Gazwu’ da kuma wanda suke kira da ‘Sariya’ wanda dukkaninsu a hausa ana iya kiransu yaki don kuwa an tura sojoji da nufin kwamawa wasu an kwama din wasu kuma ba a kwama ba.

 

A wajen malaman tarihin Gazwu yana nufin duk wani yakin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya halalta da kansa shin an kwama din a zahiri ko kuma ba a kwama ba amma dai an tafi da nufin kwamawa din. To wannan shi ne ake kira al-Gazwu din. Shi kuma yakin da ake kira Sariya shi ne yakin da Manzo (s.a.w.a) ya tura wasu daga cikin sahabbansa su yi shi amma shi bai je da kansa ba. Don haka muna iya cewa dukkanin wadannan yakukuwa ne da aka yi su lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) sai dai banbamcin shi ne na farko Manzo din ya halarci yakin shi da kansa, na biyun kuma ya ba da umurnin yinsa ne.

 

To dangane da yakin da Manzo din ya halalta da kansa, an sami sabani tsakanin malaman tarihi kan adadinsu inda wasu irin su sanannen malamin tarihin nan Al-Mas’udi suka bayyana cewar adadinsu 26 ne, wasu malaman kuma suka ce 27 ne. Don haka dai adadinsu yana tsakanin 26 da 27 ne. Sabanin da aka samu tsakanin malaman yan komawa ne gay akin Khaibar inda malaman da suke cewa yakukuwa 26 ne suka ganin yakin Khaibar din da na Wahi’ul Qura da aka yi bayan dawowar Manzon Allah daga Khaibar a matsayin yaki guda. Amma su kuma wadanda suke ganin yakukuwan biyu a matsayin masu cin gashin kansu, don haka suke cewa yakukuwan guda 27 ne. Duk da cewa akwai kuma wasu malaman tarihin irin su Ibn Ishaq duk da cewa suna ganin yakin Khaibar da na Wadi’ul Qurah din a matsayin yaki guda amma kuma sun bayyana cewar Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi yakukuwa 27 ne saboda sun shigo da Umratul Qadha a matsayin yaki.

 

Yakin farko da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi shi ne yakin Abwah wanda kuma ake kiransa da yakin waddan wanda aka yi shi a watan Safar shekara ta biyu bayan hijira sannan yaki na karshe kuma da ya yi shi ne yakin Tabuka da aka yi shi a watan Rajab shekera ta tara bayan hijira. Kamar yadda muka ce wasu daga cikin wadannan yakukuwan irin su Badar, Uhud, Khandaq, Quraiza, Mustalaq, Khaibar, Fath, Hunain da Ta’if an kwama da makiya amma sauran yakukuwan kuma ba a kwama din ba an dai je yakin ne irin su yakin Tabuka da sauransu.

 

Idan muka koma ga Sariya din kuma wanda muka ce yaki ne wanda musulmi suka yi lokacin Ma’aiki (s.a.w.a) amma ba tare da ya halarci yakin da kansa ba sannan kuma adadin mutanen da aka tura din ba su wuce 400 ba. A mafi yawan lokuta manufar irin wannan yakin ita ce fada da ashararai, kiran kabilu zuwa ga Musulunci, yin rigakafi ga wani makirci na makiya da makamantansu, a wasu lokutan ma da nufin isar da sako da koyarwar Musulunci zuwa ga wasu al’ummu.

 

Mafi yawa daga cikin wadannan yakukuwa da aka yi lokacin Manzo din sun fara su ne daga shekara ta shida bayan hijira. Malaman tarihi sun ce adadin irin wadannan yakukuwa ya kai talatin da shida, wasu kuma sun ce guda 48 ne wasu kuma sun ce sun kai 66. Sai dai mafiya yawan malaman sun tafi a kan adadin farko din ne wato 36.

 

Malam Iliyasu wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wannan tambaya taka. Da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. ka huta lafiya.

 

Masu saurare kafin mu je ga tambaya ta gaba bari mu dan shakata kadan.

Add comment


Security code
Refresh