An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 13:43

Tarihin Rayuwar Dan Ta'adda Ariel Sharon

Tarihin Rayuwar Dan Ta'adda Ariel Sharon
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa muku tambayoyin da kuka aiko mana ta hanyoyin da kuka saba saduwa da mu wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan kuna cikin koshin lafiya.

 

 

To yau ma ga mu da wani sabon shirin inda za mu masa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko din.

 

Ba tare da bata lokaci ba bari mu je ga tambayarmu ta farko a shirin wacce ta fito daga mai saurarenmu Abubakar Yahaya Geidam, jihar Yobe Nijeriya wanda ya aiko mana tambayarsa ta adireshinmu na email da ke cewa: Ku ba ni tarihin tsohon firayi ministan (haramtacciyar kasar) Isra’ila wato Ariel Sharon da kuma irin ayyukan ta’addancin da ya yi a kan al’ummar Palastinu.

 

-------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa da fatan kuma mai tambaya Abubakar Yahaya Geidam yana cikin koshin lafiya sannan kuma yana tare da mu a daidai lokacin da muke kokarin amsa maka wannan tambaya taka.

 

Ana daukan Ariel Sharon a matsayin dan siyasa da jagoran yahudawan sahyoniya da ya fi zalunta da kuma aiwatar da ayyukan ta’addanci a kan al’ummar Palastinu da kuma larabawa gaba daya.

 

An haifi Ariel Sharon ne a garin Kfar Malal a shekarar 1928. Tun yana dan shekaru 14 a duniya ya shiga kungiyar Haganah ta dakaru masu dauke da makami da suka aikata mafi munin ta’addanci a kan al’ummar Palastinu musamman a lokacin da ake kokarin kafa haramtacciyar kasar Isra’ila da korar Palastinawa daga gidajensu. A lokacin da ya kai shekaru 20 ya zama daya daga cikin kwamandojin sojojin HKI wadanda suka aikata mafi munin ta’addanci a kan palastinawa fararen hula.

 

A shekarar 1953, Ariel Sharon ya samar da Bataliya ta 101, wacce wasu sojoji ne na sirri cikin sojojin HKI da ta aikata wani bangare na kisan gillan mafi muni da aka yi wa fararen hula Palastinawa. A matsayin misali a watan Oktoban 1953 wannan bataliyar ta kashe fararen hula Palastinawa 66 a lokacin da suka kai hari kauyen Qibya Yammacin Kogin Jordan na bangaren Jordan. Rahotanni sun ce a yayin wannan harin, sojojin Ariel Sharon din sun yi amfani da muggan makamai da bindigogi masu sarrafa kansu wajen kora mutanen wannan gari na Qibya zuwa cikin gidajensu daga baya kuma rusa gidajen a kansu da bisne wasunsu da ransu.

 

Daga watan Fabrairun 1955 zuwa Oktoban 1956, Ariel Sharon ya jagoranci wani birget na sojojin Isra’ilan inda suka kai hare-hare zuwa Zirin Gaza da cikin kasar Masar da kuma Yammacin Kogin Jordan inda suka kashe mutane 83 a daya daga cikin hare-haren da suka kai garin Qalqilya.

 

A shekarar 1964, an nada Ariel Sharon a matsayin kwamandan sansanin arewa na sojojin HKI; sannan a shekarar 1966 aka ba shi kulawa da bangaren horarwa na sojojin HKI, kana daga baya kuma a shekarar 1969 aka nada shi a matsayin kwamandan sansani kudu na sojojin HKI.

 

A shekarar 1972 bayan shekara da shekaru na aikata ta’addanci a kan Palasatinawa, Ariel Sharon ya yi ritaya daga aikin soji, don shiga ayyuka na siyasa (duk kuwa da cewa an sake dawo da shi cikin aikin sojin a yakin Yom Kippur). Sai dai duk da ya ce ya bar soji amma an ce ya ci gaba da jagorantar ‘yan ta’addan yahudawa da suke kai hare-hare kan Palastinawa da sauran larabawa a kokarin da suke yi na gina ‘Babbar Isra’ila’ inda suka kaddamar da wasu hare-haren da suka kashe da raunana dubban Palastinawa a yammacin kogin Jordan ne ko Zirin Gaza ko kuma Tuddan Golan.

 

A watan Disambar 1973 an zabi Sharon ya zamanto dan majalisar Knesset na HKI. Sai dai duk da cewa yana cikin Knisset din a shekarar 1974 Sharon ya jagoranci wasu yahudawa ‘yan share guri zauna wajen kafa sansanonin bincke a garin Nablus na Yammacin Kogin Jordan don kai hare-hare da cutar da Palastinawa.

 

A shekarar 1975, firayi ministan HKI Rabin ya nada Sharon a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro. A shekarar 1977, bayan da jam’iyyar Likud ta dare karagar mulki an nada Sharon a matsayin ministan ayyukan gona, inda a nan ma ya kara fadada filayen noma na yahudawa a Yammacin Kogin Jordan da Gaza. A tsawon wannan lokaci wato 1977-81 sama da yahudawa ‘yan share guri zauna 25,000 ne suka koma yankunan Palastinawa da aka mamaye inda a nan ma suka kafa wata kungiya ta ‘yan daba irin bataliya ta 101 da Sharon ya kafa inda suka aikata aika-aika daban daban kan palastinawa.

 

A shekarar 1979 bayan da babban kotun koli ta HKI ta kafa dokar sayen filaye a yankunan da aka mamaye inda a nan take Sharon da na kurkusa da shi suka kafa cibiyoyi na gidaje da sayen filaye inda suka ta matsin lamba kan batun mamaye dukkanin sauran yankunan Palastinawa.

 

Har ila yau Sharon ya sake fitowa fili da kuma tabbatar da ayyukan ta’addancinsa a shekarar 1982 lokacin da ya jagoranci kai hari da mamaye kasar Labanon da nufin kawo karshen kungiyar PLO ta ‘yanto Palastinu wacce ta kafa sansaninta a kusa ga garin Beirut na kasar ta Labanon inda a hare-haren da suka kai din suka kashe da kuma raunana dubun dubatan Palastinawa.

 

A watan Satumban wannan shekarar ne kuma Sharon, ya jagoranci kai hare-hare kan sansanin ‘yan gudun hijira na Sabra da Shatila inda sojojin HKI bisa goyon bayan Kiristocin Falangist na Labanon suka kashe mata da maza da tsoffi masu yawan gaske; duk kuwa da cewa kwamitin tsaron MDD ya fitar da kudurin yin Allah wadai da wannan hari, amma dai Sharon da HKI sun yi kunnen uwar shegu da wannan kudurin inda suka ci gaba da danyen aikin da suke yi da kuam ci gaba da fadada matsugunan yahudawa.

 

Har ila yau kuma Sharon ya rike matsayin ministan kasuwanci da masana’antu har zuwa shekarar 1990 lokacin da aka nada shi a matsayin ministan gidaje da gine-gine lamarin da ya share masa fagen ci gaba da burin da yake da shi na fadada matsugunan yahudawa a yankunan Palastinawa. A tsawon wannan lokacin da ya rike ma’aikatu daban-daban na HKI, ya sami damar fadada matsugunan yahudawa da gidajensu da adadin yahudawan ‘yan share guri zaunan da suka zauna a wajajen sun kai dubu 110,000.

 

Hatta a bangaren batun tattaunawar zaman lafiya da HKI da ake ta magana a kai wanda kungiyoyi da masana daban-daban na Palastinawan suke da alamun tambayoyi kanta saboda ana ganin hakan a matsayin wani kokari ne kawai da Amurkawa suke yi wajen biya wa HKI bukatarta cikin ruwan sanyi, to amma sai da Sharon ya yi wa wannan shiri kafar ungulu musamman shirin zaman lafiya na Oslo inda aka ce a bayan fage Sharon ya ta tunzura yahudawa ‘yan share guri zauna kan kada su amince su bar matsugunansu. Kai hatta wanda ya kashe firayi minister Rabin din wani mai tsattsauran ra’ayi ne da ya fito daga gungun ‘yan ta’addan da Sharon ya kirikiro a sansanin yahudawa ‘yan share guri zauna na Kiryat Arba.

Add comment


Security code
Refresh