An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 13:40

Yadda Ake Kama Tashar Press TV Ta Iran

Yadda Ake Kama Tashar Press TV Ta Iran
Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

 

Yanzu kuma bari mu je ga tambayarmu ta gaba kuma ta biyu a shirin wacce ta fito daga mai saurarenmu Tijjani Ahmad Tudun Wada, PO Box 5012 Kano wanda yace a halin yanzu bai san dalilin da ya sa ba ya kama tashar nan ta Press TV ba saboda a cewarsa yana jin dadin shirye-shiryen da tashar take gabatarwa da kuma hanyoyin da za a ci gaba da kama ta.

 

To Malam Tijjani Ahmad Tudun Wadan Kano mun gode kwarai da gaske da wadannan tambayoyi naka da fatan kana cikin koshin lafiya. Ga abin da muka tanadar maka.

 

Da farko dai ita wannan tasha ta Press TV wacce take watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin harshen Turanci tana daga cikin tashoshin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da suka yi tasirin gaske cikin al’ummomin duniya musamman a kasashen Turai da Amurka da kuma nahiyarmu ta Afirka sakamakon fadin gaskiya da take yi da kuma bayyanar da hakikanin abin da ke gudana a kasashen Turai da Amurka da ma kasashen musulmi saboda irin yadda kafafen watsa labaran gwamnatocin wadannan kasashen suke boye gaskiya da kuma hakikanin abubuwan da ke faruwa a kasashensu.

 

Haka nan kuma a bangare guda tashar ta taka gagarumar rawa wajen tona asirin yahudawan sahyoniya da irin zaluncin da suke yi wa al’ummar Palastinu, al’ummar musulmi da ma sauran al’ummomin duniya.

 

Irin wannan tasirin da tashar ta yi ko shakka babu bai yi dadi ga wadannan kasashe da masu mulkinsu ba don haka suka fito da hanyoyi daban-daban wajen ganin sun rufe bakin wannan tasha da hana ta isa ga mutane.

 

Don haka ne gwamnatocin wadannan kasashen na Turai da Amurka da kuma HKI suka sanar da yakin su a fili kan wannan tashar da ma sauran tashoshin Iran. Daya daga cikin hanyoyin da suka bi shi ne hanyar sanya takunkumi a kan wadannan kafafen watsa labarai da hana watsa su ta tauraron dan’adam din wadannan kasashen, bugu da kari kan fito da dokokin hukumta kamfanonin da suke mu’amala da su.

 

Wannan watakila shi ne dalilin da ya sanya ba ka jin tashar Press TV din saboda toshe tashar da suke ci gaba da yi.

 

Idan kuma muka koma ga batun hanyoyin da kake son sani na kama tashar, to a nan muna iya cewa tun dai lokacin da turawan da abokansu suka kaddamar da wannan yaki na toshe tashar PRESS TV din su ma masu tashar suka tsaya wajen ganin sun samo hanyoyin da za su samar don masu saurarensu su sami damar kama su.

 

Daga cikin hanyoyin da suka bullo da su har da ci gaba da watsa shirye-shiryen na su ta hanyar internet musamman ga mutanen da suke kasashen Turai da Amurkan wadanda suke da hanyoyin internet masu karfin da za su iya gani da sauraren tashar cikin sauki.

 

Wanda idan aka shiga shafinsu na internet wato www.presstv.ir za a iya ganin wannan hanyar, kamar yadda kuma sun fito da wasu hanyoyi na saurarensu ta hanyar mobile ko kuma handset shi ma wanda za a iya gani a shafin nasu.

Add comment


Security code
Refresh