An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 April 2014 13:38

Tarihin Kauyen Qunu, Mahaifar Nelson Mandela

Tarihin Kauyen Qunu, Mahaifar Nelson Mandela
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa muku tambayoyin da kuka aiko mana ta hanyoyin da kuka saba saduwa da mu wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan kuna cikin koshin lafiya kuma za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

To yau ma ga mu da wani sabon shirin. Ba tare da bata lokaci ba ga tambayarmu ta farko wacce ta fito daga masu saurarenmu Sani Mai Lange-Lange Yawuri na jihar Kebbin Nigeria wadanda suka ce suna son mu ba su tarihin kauyen nan na Qunu, inda aka haifi tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela sannan kuma aka bisne shi a can.

 

----------------------------------.

 

To masu saurarenmu Malam Sani Mai Lange-Lange da kuma Malam Ango malamain makaranta a Yawurin jihar Kebbin Nigeria mun gode kwarai da gaske da wannan wasika da kuma tambaya taku da fatan kuna cikin koshin lafiya kuma kuna tare da mu musamman a daidai lokacin da muke kokarin amsa muku wannan tambaya ta ku. Sai ku gyara zama don jin abin da muka tanadar muku.

 

Garin Qunu dai wani dan karamin kauye da ke lardin Gabashin Cape na kasar Afirka ta kudu; wanda lardi ne mai tsohon tarihi da kuma muhimmanci musamman saboda wani adadi mai yawa na shugabanni da jagororin al’ummar Afirka ta kudun sun fito ne daga wannan lardin irin su Nelson Mandela, Oliver Tambo, Walter Sisulu, Govan Mbeki, Raymond Mhlaba, Robert Mangaliso Sobukwe, Chris Hani, Thabo Mbeki, Steve Biko and Charles Coghlan da dai sauransu wanda kowane guda daga cikinsu ya taka gagarumar rawa a fagen fada da wariyar launin fata da kuma ci gaba da ciyar da kasar gaba bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fatan. Garin na Qunu dai yana kimanin kilomita 32 daga kudu masu yammacin garin Mthatha shi ma dai mai tarihi.

 

Shi dai wannan gari dan wani karamin gari ne wanda ba shi da wani cikakken rubutaccen tarihi hakan kuwa saboda ba wani gari ne mai girma ba don haka iyakacin binciken da muka gudanar dan abin da muka samu bai wuce wajen da kauyen yake ba da adadin mutanen kauyen wanda shi ma yake komawa ga kirgen jama’a da aka gudanar ne a shekara ta 2001 wanda a lokacin mutanen da suke garin ba su kai mutane 300 ba wanda mafiya yawansu mata ne, wato kashi 57.28% na mutanen kauyen mata ne sai kuma maza wanda ba su wuce kashi 42.72% ba. Don haka a takaice dai mutanen kauyen ba wani yawa suke da shi ba.

 

Dukkanin mutanen kauyen kuwa bakaken fata ne. A bangaren yare kuwa mafi yawa daga cikin mutanen kauyen suna magana ne da harshen isiXhosa sai kuma wasu ‘yan kadan na mutanen kauyen da suke magana da harshen isiNdebele.

 

Kamar yadda muka ce haihuwar wasu fitattun mutanen Afirka ta Kudu a wannan garin shi ne ya fito da shi fili har aka sanshi. Daga cikin wadanda aka haifa a wajen shi ne tsohon shugaban Afirka ta kudun marigayi Nelson Mandela sannan kuma a wajen ne ya girma sannan kuma a can aka bisne shi bayan mutuwarsa kamar yadda ya bukata.

 

Sannan kuma a wannan wajen ne mahaifin Nelson Mandelan ya koma da zama bayan da aka tsige shi daga sarautar Mvezo na kauyen yankin.

 

A takaice dai wannan shi ne abin da muka tanadar maka Malam Sani Mai Lange-Lange Yawuri da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. Ka huta lafiya.

 

Masu saurare kafin mu je ga tambayarmu ta gaba, sai a shakata da abin da ke bisa inji.

Add comment


Security code
Refresh