An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 20 May 2012 05:42

Membobin Kungiyar Commonwealth

Masu saurare barkanmu da sake saduwa. Yanzu kuma bari mu je ga tambayarmu ta biyu a cikin shirin wacce ta fito daga mai saurarenmu Malam Musa Uzairu daga garin Tamale na kasar Ghana wanda ya bugo waya ya gabatar da tambayarsa kamar haka: cewa yana son mu gaya masa kasashe nawa ne membobin kungiyar nan ta Commonwealth, nawa ne daga cikinsu suka fito daga Afirka sannan kuma shin dukkanin kasashen da Ingila ta yi musu mulki suna cikin kungiyar. To Malam Musa Uzairu daga kasar Ghana mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya. Ga abin da muka tanadar maka. Ita dai wannan kungiya ta Commonwealth (wato kamar yadda ake kiranta da hausa da cewa kungiyar kasashe renon Ingila) an kafa ta ne a shekarar 1931 kuma mafi yawa daga cikin membobin kasashe ne da suka kasance karkashin mulkin mallakar Ingila duk da cewa akwai wadansu kasashe membobin kungiyar da ba su kasance karkashin ikon Ingilan ba. Kamar yadda kake son sani ita wannan kungiyar tana da kashashe 54 ne matsayin membobinta, wanda 18 daga cikinsu sun fito ne daga nahiyar mu ta Afirka kamar yadda kake son sani wadannan kasashe kuwa sun hada: Nigeria, Ghana, Gambiya, Kamaru, Kenya, Lesotho, Malawi, Mauritius, Mozambique, Botswana, Namibiya, Rwanda, Saliyo, Afirka ta kudu, Uganda, Tanzaniya da Zambiya. Don haka wadannan su ne membobin wannan kungiya ta commonwealth da suka fito daga nahiyar mu ta Afirka. Idan kuma muka koma ga bangare na uku na tambayar taka da kake son sanin shin dukkanin kasashen da Ingila ta yi musu mulkin mallaka suna cikin wannan kungiya ko kuma a'a, to a nan dai amsar ita ce a'a, wato ba dukkanin kasashen da Ingila ta yi musu mulkin mallaka ne suke cikin kungiyar ba don kuwa akwai kasashe irin su Amurka da Yemen da Burma wadanda duk da cewa Ingila ta yi musu mulkin mallaka amma ba su taba zama cikin wannan kungiyar ba, kamar yadda kuma akawai wadansu kasashe wadanda Ingila din ma ba ta taba musu mulki ba amma sun shigo cikin kungiyar kasashe irin su Mozambique wacce kasar Portugal ce ta yi mata mulkin mallaka, da Rwanda wacce Belgium ce ta mulke tad a kuma kasar Kamaru wacce kasashen Ingila da Faransa suka yi mata mulkin mallaka. To amma duk da haka ana kiran wannan kungiyar da sunan kungiyar kasashe renon Ingila saboda kuwa kashi casa'in da wani abu na membobin kungiyar sun kasance ne karkashin iko da mulkin mallakan Ingilan inda ban da wadannan kasashe ukun da muka ambaci sunayensu. To Malam Musa Uzairu wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wadanann tambayoyi naka da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka ka huta lafiya............................ (END)

Add comment


Security code
Refresh