An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 20 May 2012 05:41

Tarihin Birnin Damaskus Na Kasar Siriya

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata shirin da ke amsa tambayoyin da ku masu saurare ku ka aiko mana ta hanyoyin da kuka saba saduwa da mu, da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yau ma ga mu da wani sabon shirin inda muke fatan za mu amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana din. Ba tare da bata lokaci ba tambayarmu ta farko ta fito ne daga mai saurarenmu Malam Murtadha daga jihar Taraban Nigeria wanda ya bugo waya ya gabatar da tambayarsa kamar haka: "Don Allah ina son ku bani Tarihin birnin Damaskus na kasar Siriya da irin daulolin da aka kafa a cikinta tun bayan bayyanar addinin Musulunci". --------------------------------------- To Malam Murtadha daga Taraba mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu musamman a daidai wannan lokacin da muke amsa maka wannan tambaya taka. Shi dai birnin Damaskus shi ne babban birnin kasar Siriya sannan kuma gari mafi girma a bangaren girman kasa a Siriya kuma na biyu a yawan jama'a bayan garin Halab don kuwa a bisa kidayar da aka gudanar a shekara ta 2011 birnin Damaskus din yana da kimanin mutane miliyan 4, 711,000. An fara zama a birnin ne tun kimanin Alfiyya ta biyu kafin annabi Isa (a.s), sannan kuma birnin ya zamanto helkwatar dauloli da gwamnatoci daban-daban har zuwa lokacin daular Umayyawa wanda birnin Damaskus din shi ne babban birninsu. To sai dai kuma sakamakon kifar da daular Umayyawan da kafa daular Abbasiyawa, birnin Damaskus din ya fuskanci koma baya sakamakon mayar da helkwatar daular musulmi din ta lokacin zuwa birnin Bagadaza. Tsawon mulkin Abbasiyawan birnin Damaskus ya fuskanci koma baya da rashin kulawa, duk da cewa daga baya a lokacin mulkin Ayyubawa da suke da tushe na Kurdawa da kuma mulkin Mamlukawa, to amma birnin ya fuskanci gagarumar koma baya lokacin mulkin daular Usumaniya ta Turkawa. A halin yanzu dai garin Damaskus din shi ne babban birnin kasar Siriya sannan kuma babban birnin al'adu na kasashen larabawa. Malaman tarihi sun bayyana cewar tarihin kasar yana komawa ne ga misali karni na 15 kafin haihuwar Annabi Isa (a.s). Tsawon tarihi din dai larabawa suna kiran garin da sunan Dimashq al-Sham to amma saboda wahalar fadi ko kuma don tajartawa sai ana kiran garin da sunan Dimashq ko kuma Sham, duk da cewa wasu suna kiran kasar Siriyan gaba daya ne da sunan Sham din, to amma a mafi yawan lokuta idan aka kara da bilad al-sham shi ne ake nufin kasar Siriyan gaba daya. Mafi yawan mutanen birnin Damaskus din larabawa ne wanda aka ce sun kai kashi 90 da wani abu cikin dari, sai kuma sauran kabilu musamman Kurdawa. A bangaren addini ma kashi 90 da wani abu na mutanen Damaskus musulmi ne, sai kuma kiristoci da suke biye musu. Bisa la'akari da dadewar birnin don haka akwai wajajen tarihi da yawan gaske da a kowace shekara ake samun miliyoyin mutane da suke kai ziyara wajen don gane wa idanuwansu abubuwan da suke wajen, wasu kuma don neman albarka saboda alakar da wajajen suke da ita da addini da kuma wasu waliyan Allah. Daya daga cikin fitattun wajaje na Musulunci a garin na Damaskus shi ne Masallacin Umayyawa da ke garin, har ila yau kuma da haramin Sayyida Zainab 'yar Imam Ali da Fatima (a.s) ga kuma kabarin Sayyida Ruqayya 'yar Imam Husain (a.s), haka nan kuma akwai makabartar da aka ce a nan ne aka bisne kawukan shahidan Karbala da kuma wajen da Imam Zainul Abidin dan imam Husain (a.s) ya yi ibada tsawon zamansa a garin a matsayin fursunan yaki da dai sauran wajajen tarihi masu girma. Idan muka koma ga bangare na biyu na tambayar taka da kake son sanin daulolin da aka kafa bayan bayyanar Musulunci a garin na Damaskus, to a farkon shirin dai mun yi ishara da wasu daga cikinsu. Wato tun bayan lokacin da sojojin Musulunci a lokacin halifofin musulmi suka sami nasarar kama garin na Damaskus, musulmi sun kafa ikonsu a garin musamman lokacin da Mu'awiyya ya kafa mulkinsa a kan musulmi bayan shahadar Imam Ali (a.s) inda wajen ya zamanto helkwatar daular Umayyawa din. Daga nan kuma bayan zuwan Abbasiyawa an dan sami rikice-rikice a birnin lamarin da ya kawo wasu gwamnatoci na wasu lokuta masu cin gashin kansu har zuwa lokacin mulkin Fatimiyawa. Daga nan kuma har zuwa lokacin mulklin daular Turkawa ta Seljuq da Ayyubiyawa har zuwa lokacin mulkin Mamluk wanda suka kwace mulki bayan hare-haren da Mogol suka kawo Siriya da kwace garin. Su dai Mamluk din sun mai da wa Damaskus wani bangaren na daularsu da suke gudanar da ita daga Masar har zuwa shekara ta 1516 lokacin da daular ta fadi sannan kuma Daular Turkawa ta Usumaniya ta dare karagar mulki. To Malam Murtadha a takaice wadannan su ne manyan dauloli da suke yi mulki a birnin Damaskus din bayan bayyanar Musulunci, kuma da hakan ne muka kawo karshen abin da muka tanadar maka kan wadannan tambayoyi naka da fatan ka gamsu sai mun sake ji daga gare ka. Ka huta lafiya. Masu saurare kafin mu je ga tambayarmu ta biyu a cikin shirin ga wannan abin da ke bisa injin.

Add comment


Security code
Refresh