An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 20 May 2012 05:40

Bayani Kan Lokacin Da Aka Kafa Kungiyar 'Yan Ba Ruwanmu

Masu saurare barkanmu da sake saduwa. Tambayarmu ta gaba ta fito ne daga mai saurarenmu Bala Manu, P.O.Box 2346 Gombe, jihar Gomben Nigeria wanda ya ce yana son sanin yaushe ne aka kafa kungiyar nan ta Non-Aligned Movement da ake kira kungiyar 'yan ba ruwanmu da kuma manufar kafa kungiyar. To Malam Bala Manu mun gode kwarai da gaske da wadannan tambayoyi naka, yanzu sai ka gyara zama don sauraren abin da muka tanadar maka. Da farko dai ita wannan kungiyar ta Non Aligned Movement (NAM) ko kuma wadda ake kira da kungiyar 'yan ba ruwanmu wata kungiya ce ta wasu gungun kasashe wadanda suke ganin kansu a matsayin wadanda ba su karkata zuwa ga wasu daga cikin manyan kasashen duniya masu fadi a ji ba ko kuma suna adawa da daya daga cikinsu. Su dai suna ganin kansu ne a matsayin 'yantattu wadanda suke gudanar da ayyukansu ba tare da nuna kiyayya ko kuma jingina da daya daga cikin masu karfi na duniya. An kafa kungiyar ne a shekarar 1961 a garin Belgrade karkashin kokari da kwazon wasu shugabanni na wancan lokacin irin su tsohon shugaban kasar Yugoslavia Josip Broz Tito, firayi ministan farko na kasar Indiya Jawaharlal Nehru, tsohon shugaban kasar Masar Gamal Abdul Nasir, shugaban kasar Ghana na farko Kwame Nkurumah da kuma shugaban kasar Indonesiya na farko Sukarno. Dukkaninsu sun kasance masu kira zuwa ga samar da kasashe masu tasowa wadanda za su sami matsaya ta tsaka-tsaki dangane da rikicin da ke gudana tsakanin kasashen yammaci da na gabashi a lokacin yakin ruwan sanyi. Dangane da manufar kafa wannan kungiya a nan muna iya cewa ana iya ganin hakan cikin wani jawabi da tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro ya yi inda ya ke cewa dalilan kafa kungiyar ita ce tabbatar da "'yancin kan kasashe, mutumci da kuma tsaron wadannan kasashe na 'yan ba ruwanmu, a kokarin da suke yi na fada da mulkin mallaka, nuna wariya da kuma dukkanin wani kokarin wuce gona da iri na manyan kasashen duniya. Kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu suna a matsayin kashi biyu cikin uku na dukkanin kasashe membobin MDD sannan kuma su ne kashi 55 cikin dari na yawan al'ummomin duniya. Ya zuwa yanzu dai kungiyar tana kasashe 120 a cikinta da kuma 'yan kallo 17. Malam Bala Manu wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wadannan tambayoyi naka, da fatan ka gamsu, sai mun sake ji daga gare ka. --------------------------------- END

Add comment


Security code
Refresh