An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 20 May 2012 05:38

Tarihin Captain Amadu Sanogo Shugaban Juyin Mulkin Mali

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata shirin da ke amsa tambayoyin da kuka aiko mana wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi kowane mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya. Yau ma ga mu da wani sabon shirin inda za mu amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana. Ba tare da bata lokaci ba, bari mu je ga tambayarmu ta farko da ta fito daga mai saurarenmu Mamman Sani Amadu daga garin Maradi na jamhuriyar Nijar wanda ya ce yana son karin bayani kan mutumin nan da ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a kasar Mali Captain Amadu Sanogo da kuma dalilan da ya sanya shi yin wannan juyin mulkin. -------------------------------------- To mai saurarenmu Mamman Sani Amadu mun gode kwarai da gaske da fatan kana cikin koshin lafiya kuma kana tare da mu musamman a daidai lokacin da muke amsa maka wanann tambaya taka. Ga abin da muka tanadar maka. Da farko dai yana da kyau a san cewa bisa la'akari da cewa shi Captain Amadu Haya Sanogo ba wani sanannen mutum ba ne sosai don kuwa ya fito fagen siyasa har aka san shi sosai a duniya ne bayan juyin mulkin da ya yi a kasar da ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin shugaban kasar Amadou Toumani Toure a ranar 22 ga watan Maris na wanann shekarar ta 2012, kana kuma ya nada kansa a matsayin shugaban gwamnatin sojin kasar, don haka iyakacin binciken da muka gudanar ba mu sami wani cikakken bayani kansa ba in ba dan abu kalilan ba. Don haka muna iya farawa da cewa an haifi Kaptain Amadou Sanogon ne a shekarar 1972 wasu kuma suka ce a shekarar 1973 a wani gari mai suna Segou da ke kasar Malin. Captain Sanogo ya fara karatunsa ne a garin na su daga nan kuma sai ya wuce zuwa wata makarantar soji inda ya yi karatu a can. Wasu bayanan suna nuni da cewa ya dan fuskanci matsala a yayin wanann karatu amma dai duk da haka ya sami nasarar ci gaba da katatun nasa na soji. A tsawon wannan karatun nasa ya tafi kwasa-kwasai daban-daban na soji don samun karin horo. Daga cikin kasashen da ya tafi don gudanar da irin wadannan kwasa-kwasai har da Amurka, hakan ne ma ya ba shi damar koyon harshen turanci duk kuwa da cewa a kasarsa ana magana ne da harshen faransanci. Captain Sanogo ya shafe shekaru 22 a cikin aikin sojin, sai dai kuma kafin yayi juyin mulki ya rike wasu 'yan kananan mukamai ne a kasar ta Mali don haka ne ma lokacin da aka sanar da shi a matsayin shugaban mulkin soji na kasar da dama da suka sanshi musamman wadanda suka koyar da shi a baya ba su taba zaton zai taba samun irin wannan mukami mai girma a kasar Mali din ba. Daga cikin abubuwan da ya fara yi bayan darewarsa karagar mulkin kasar shi ne dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, dakatar da ayyukan wasu kungiyoyi da kuma sanya dokar ta bace da rufe kan iyakokin kasar. Captain Sanogo ya mulki kasar Mali din ne na tsawon kwanaki 21 don kuwa ya sauka daga karagar mulkin ne a ranar 12 ga watan Aprilu 2012 sakamakon yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsa da kungiyar ECOWAS ta tattalin arzikin yammacin Afirka na dawo da mulki hannun fararen hula sannan su kuma ba za a hukumta su ba. Captain Sanogo dai yana da mace guda da kuma 'ya'ya uku mata. Idan kuma muka koma ga bangaren tambayar taka da kake son sanin dalilan juyin mulkin da suka yi din to a zahiri dai sannan kuma bisa ga abin da suka sanar shi ne irin mu'amalar da gwamnatin Amadou Toumani Toure ta ke yi da buzaye 'yan tawaye na arewacin kasar da kuma yadda ta gaza wajen kawo karshensu, baya ga batun rashawa da cin hanci. To sai dai kuma su ma sojojin sun gagara tabuka wani abin a zo a gani kan hakan don kuwa bayan kwanaki goma da darewa karagar mulkinsu ne 'yan tawaye buzayen suka sami nasarar kwace manyan garuruwa na arewacin da suka hada da garuruwan Kidal, Gao da kuma Timbuktu wanda yake nufin kusan dukkanin arewacin ya fada hannunsu. Malam Mamman Sani Amadu wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wadannan tambayoyi naka da fatan ka gamsu. Sai mun sake ji daga gare ka. Ka huta lafiya.

Add comment


Security code
Refresh