An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 04 April 2012 08:21

Shin Mace Ta Taba Shugabanci A Nahiyar Afirka?

To yanzu kuma bari mu je ga tambayar mu ta biyu a cikin wannan shirin wacce ta fito daga mai sauraren mu Hajiya Lami Ibrahim daga Makka kasar Saudiyya wacce ta bugo waya ta ce: Ina son ku yi min karin bayani wai shin a nahiyar Afirka akwai macen da taba zama shugaban kasa kuwa, idan akwai ku gaya min sunanta da kuma kasar. Hajiya Lami daga Saudiyya mun gode da wannan tambaya taki da fatan kina cikin koshin lafiya tare da dukkanin masu sauraren mu da suke kasa mai tsarkin. To dangane da wannan tambayar taki a bisa binciken da muka gudanar mun gano cewa akwai mata guda uku da suka taba mulkan wasu kasashen nahiyar ta mu ta Afirka, daya a matsayin shugabar kasa, sai kuma wasu da suka shugabanci wasu kasashen a matsayin firayi minista, wanda dukkaninsu sun mulki wadannan kasashe kuma su ne suke da cikakken iko a lokacin, duk da cewa daya daga cikinsu ma har yazu yanzu din tana mulkin. Ala kulli hal dai ga abin da muka tanadar miki. Bari mu fara da matsayin shugaban kasa, mace ta farko wacce kuma ita ce guda daya tilo da ta rike wannan matsayi na shugabar kasa a nahiyar Afirkan ita ce shugabar kasar Liberiya ta yanzu wato Madam Ellen Johnson-Sirleaf wacce ta dare karagar mulkin kasar Liberiyan a watan Nuwamban 2005 kuma har yanzu ita ce shugabar kasar. Mace ta biyu kuma ita ce firayi ministan kasar Mozambique Luisa Dias Diago wacce ta dare wannan kujerar a 17 Fabrairu 2004 zuwa 16 Janairu 2010 ita ce kuma firaminista mace ta farko a kasar. Idan muka koma ga fagen shugabanci na firayi minista kuwa mace ta farko da taba rike irin wannan matsayi na firayi minista a nahiyar ta mu ta Afirka ita ce Elisabeth Domitien wacce ta rike matsayin firayi ministar kasar Afirka ta tsakiya daga shekarar 1975 zuwa 1976. Sai kuma Sylvie Kinigi wacce ta rike matsayin firayi ministar kasar Burundi daga shekarar 1993 zuwa 1994. Sai kuma Agathe Uwilingiyimana wacce ta rike mukamin firayi ministar kasar Rwanda daga shekarar 1993 har zuwa lokacin da aka kashe ta a shekara ta 1994 wanda hakan yana daga cikin mafarin kisa kiyashin da ya faru a kasar. Sai kuma Mame Madior Boye wacce ta kasance firayi ministan kasar Senegal daga shekara ta 2001 zuwa ta 2002. Sai kuma Luisa Dias Diogo wacce ta rike matsayin firayi ministan kasar Mozambique na tsawon shekaru shida wato daga ranar 17 ga watan Fabrairun 2004 har zuwa 16 ga watan Janairun 2010. Sai Maria das Neves wacce ta zama firayi minista a kasar Sao Tome and Principe daga 2002 zuwa 2004. Sai kuma Maria do Carmo Silveira ita ma firayi minista ce ta kasar Sao Tome and Principe a shekara ta 2005. Mace ta gaba ita ce Cisse Mariam Kaidama Sidibe wacce take rike da matsayin firayi minista a kasar Mali tun daga watan Aprilun wannan shekara ta 2011 har zuwa yanzu din nan tana ci gaba da rike wannan matsayin. Sai kuma Cecile Manorohanta wacce ta taba rike wannan matsayi na firayi minista na rikon kwarya na kasar Madagasca. To Hajiya Lami wannan shi ne abin da muka tanadar miki dangane da wannan tambaya ta ki da fatan kin gamsu. Sai mun sake ji daga gare ki, ki huta lafiya.

Add comment


Security code
Refresh