An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 04 April 2012 08:20

Karin Bayani Kan Ma'anar Kasashen Larabawa

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata da ke amsa tambayoyin da kuka aiko mana wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako. To yau ma ga mu da wani sabon shirin da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkonsa har zuwa karshensa. Ba tare da bata lokaci ba bari mu je ga tambayoyin da muke da su. Tambayar da ke a hannunmu a halin yanzu ta fito ne daga hannun mai saurare Idi Abubakar, Jalingo, jihar Adamawan Nigeria wanda yake cewa ina so ku amsa min wadannan tambayoyi nawa: su ne kuwa: 1- Ina son ku yi min karin bayani kan abin da ake nufi da kasashen larabawa.2- Kasashe nawa ne ake kirga su a matsayin kasashen larabawan da kuma sunayensu3- Sannan kuma wace kasa ce ta fi yawan jama'a sannan kuma wace ce ta fi karanci a tsakanin wadannan kasashen? -------------------------------------- To Malam Idi Abubakar mun gode kwarai da gaske da wadannan tambayoyi naka, sai ka gyara zama don jin abin da muka tanadar maka. Dangane da tambayarka ta farko da kake son sanin me ake nufi da kasashen larabawa, to a nan dai akwai fassarori daban-daban da aka ba wa wannan kalma kowane yana la'akari da wani bangare da ya ba shi muhimmanci, hakan kuwa ya samo asali ne saboda rashin wata takamammiyar fassara da dukkanin bangarori suka yarda da ita. Ta farko dai ita ce cewa kasashen larabawa ko kuma abin da ake kira da al-Alam al-Arabi da larabci ko kuma Arab world da turanci shi ne kasashen da suke magana da harshen larabci da suka kumshi yankunan arewacin Afirka, yammacin Asiya da sauransu. Wata fassarar kuma tana ganin kasashen larabawan a matsayin kasashen da suke cikin kungiyar hadin kasashen larabawan (Arab League) wadanda su ne kasashe 22 wadanda a nan gaba za mu ji sunayensu. Hakan kuwa ya samo asali ne bisa irin fassarar da ita kanta kungiyar ta ba wa kalmar balarabe inda ta fassarar kalmar balarabe da cewa shi ne: "Duk wani mutumin da harshensa (yarensa) shi ne larabci, wanda ya ke rayuwa a daya daga cikin kasashen da suke magana da harshen larabci sannan kuma ya damu da matsaloli da kuma bukatun masu magana da harshen larabci", duk kuwa da cewa wasu suna ganin wannan fassarar tana da matsala don kuwa ta ba da muhimmanci ne kawai ga bangare na wajen da kasashen suke, don haka ne suke ganin akwai bukatar karin wasu kalmomi da wasu abubuwa cikinta. Don haka ne masu wannan ra'ayi suke ganin fassarar da ta fi dacewa ita ce cewa: Kasashen larabawa tana nufin wasu mutane da kasashe wadanda ta wani bangare harshen larabci, al'adu da kuma waje ya hadu su, ko kuma kasashe da yankunan da mafiya yawan mutanen wajen suna magana ne da harshen larabci. Masu wannan fassarar suna ganin idan aka fadi hakan ya hado da dukkanin bangarorin da aka tabo a sauran fassarar da aka bayar din. To wannan dangane batun fassarar kasashen larabawa kenan. Idan kuma muka koma ga tambaya ta biyun da ka gabatar malam Idi Abubakar da ke son sanin kasashen da ake kirga su a matsayin kasashen larabawan, to bisa la'akari da irin rarrabuwar da aka samu wajen fassarar ma'anar kalmar kasashen larabawan, to amma wajen amsa wannan tambayar taka za mu fi daukan fassarar da ta ke ganin kasashen larabawan a matsayin wadanda suke cikin wannan kungiya ta larabawa wadanda su ne kasashe 22 wadannan su ne: Aljeriya, Bahrain, Komoros, Djibouti, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Iraki, Jordan, Kuwaiti, Labanon, Libiya, Masar Mauritaniya, Maroko, Oman, Palastinu, Qatar, Saudi Arabiya, Somaliya, Sudan, Siriya, Tunusiya da kuma kasar Yemen Wadannan su ne kasashe 22 na suke cikin kungiyar hadin kan kasashen larabawan kamar yadda ka bukata. Idan kuma muka koma ga tambayarka ta uku da kake son sanin wace kasa ce cikin kasashen larabawan ta fi yawan mutane sannan kuma wace ce tafi karancin mutanen. To a nan dai kasar Masar ita ce kasar da ta fi yawan jama'a a kasashen larabawan wadanda a halin yanzu dai suna da mutane sama da mutane miliyan 81 saboda a bisa kididdigar da aka fitar a wannan shekara ta 2011 an bayyana cewar adadin mutanen kasar sun kai mutane miliyan 81, da dubu 15 da 887, sai kuma kasashen Aljeriya da Iraki da suke biye mata wadanda suke da miliyan 35 da wani abu da kuma miliyan 34 da wani abu. Idan kuma muka koma ga bangaren da kake son kasar da ta fi karancin mutane a cikin kasashen larabawan. To a nan dai kasar da tafi karancin mutanen ita ce kasar Komoros wacce take da mutane kasa da miliyan guda. A bisa kididdigar da aka gudanar a shekarar bara (2010) an bayyana cewar mutanen kasar sun kai mutane dubu 798, kafinta kuma sai kasashen Djibouti mai mutane dubu 864 sai kuma Bahrain mai mutane miliyan 1, da dubu 234 da 596. Malam Idi Abubakar daga Jalingon jihar Adamawan Nigeria wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wadannan tambayoyi naka, da fatan ka gamsu. Sai mun sake ji daga gare ka, ka huta lafiya.

Add comment


Security code
Refresh