An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Kyawawan Dabiu

Kyawawan Dabiu (42)

Monday, 29 June 2015 07:05

Shiri Na 28

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka da suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani dangane da mahimancin hadiye fishi tare da irin kyawawen sakamokon dake tattare da shi, domin mahimancin wannan maudu'in shirin na Yau ma zai ci gaba daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.   Musuc**************************************************   Masu saurare shirin na yau zai farada kaolin Allama Sayyid Ali Khan Almadani Alshirazi a cikin littafinsa mai suna Riyadu Salikin Fi Sharhi Sahifatu Sayidu Sajidin) yayin  da yake sharhi kan isharar da Imam Sajjad (a.s) yayi na nemam wannan kyakkyawar dabi'a daga Allah madaukakin sarki , Sayyid Ali Khan yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce ma'anar hadiye fishi shine idan Mutune yayi fishi, to ya danne fishinsa a ransa ba tare da  ya firta wata magana ba wacce ke nuna ya ya fishi. ko kuma ya aikata wani abu wanda ke nuna fishinsa a zahiri ko ya bayyana fishin a fuskarsa ko makamancin haka, wannan shi ake kira da hadiye fishi kuma wannan kyakkyawar dabi'a na daga cikin dabi'u kyawawa wanda Allah madaukakin sarki yayi ishara da su a cikin Alkur'aninsa mai tsarki kamar haka:( wadanda suke ciyarwa cikin halin yalwa da guntsi ,da masu hadiye fushi, da masu yafewa Mutane, Allah kuwa yana Son masu kyautatawa.) suratu Ali Imran Aya 134 sayyid ya ci gaba da cewa bayan wannan aya hadisai da dama sun ishara a kan wannan kyakkyawar dabi'ar. hakika masu saurare wanda Allah madaukaki ya bashi ikon yafiya gami da hadiye fishinsa yayin da aka yi masa wani laifi, zai gudanar da rayuwarsa cikin konciyar hankali wacce ta nisanta da bacin rai gami fishi da kuma daukan fansa, a cikin littafin Mishkatu Anwar na shek Tabrasi an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(wanda ya fi kowa hankali daga cikin Mutane,shine wanda ya fi kowa isa siyasa wajen tafiya da al'umma kuma wanda ya fi daurin kai daga Mutane wanda ya fi su hadiye fishinsa yayin da rai ya bace). har ila yau hadiye fishi yayin da Rai ya bace ya kan sanya Mutune ya kai ga samun daya daga cikin rukunan kamalar Imani, a cikin Littafin Almahasin na shek Barki an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ababe guda uku duk wanda ya kasance yanada su Imaninsa ya kammala, na farko wanda idan ya amince da wani abu  to ba zai yarda ya sanya yardar nan tashi cikin bata ba, na biyu  wanda idan yayi fishi to ba zai yarda fishin nan nashi ya fitar da shi daga tafarkin gaskiya ba, na uku kuma wanda idan yayi rashi baya daukan na waninsa).   Musuc**************************************************   Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Hadisin shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) inda a cikinsa yake siffanta hakikanin mumuni.a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa:(mumuni shine wanda yake aiki da damar da Allah madaukaki sarki ya bashi, mai hadiye fishi yayin da rai da bace, kuma mai kyawawen dabi'u). A cikin littafin Khisal na shek Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) na cewa:( ababe guda uku duk wanda ya kasance yanada su Imaninsa ya kammala wanda yayi hakuri bisa zalunci kuma ya hadiye fishinsa yayin da rai ya bace kuma ya meda komai ba komai ya yafe ya kuma yi gafara, zai kasance daga cikin wadanda za su shiga Aljanna ba tare da hisabi ba,kuma su hadu da ceton Allah yayin da suke cikin matsatsi da yalwa). Hakika shek Saduk yardar Allah tabbata a gareshi ya ruwaito wasiyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ga shugaban wasiyai da mumunai Aliyu bn abi talib (a.s) a cikin Littafinsa mai suna Man La Yahduruhul Fakih, Ma'aikin Allah na cewa:(Ya Ali zan yi maka wata wasiya sai ka kiyayeta kuma idan har ka kiyaye ba shaka ba zaka gushe daga Alheri ba, Ya Ali duk wanda ya hadiye fishinsa yayin da yake da ikon ramawa kuma ya yafe, hakika Allah madaukakin sarki zai saka masa da aminci ranar Alkiyama kuma zai dandana masa dadin Imaninsa) har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) na cewa:(duk wanda ya hadiye fishinsa a yayin da yake da ikon ramawa kuma ya yafe Allah madaukakin sarki zai kiyaye zuciyarsa daga duk wani sabo kuma a bashi cikekken aminci da kuma imani ranar alkiyama). Daga karshe masu saurare bari mu karanto wannan  hadisi na shugabanmu   Imam Ja'afaru Sadik (a.s) wanda sikatul Islam kulaini ya ruwaito a cikin Littafinsa mai suna Alkafi inda a cikin sa Imam (a.s) ke cewa:(duk wanda ya hadiye fishinsa yayin da aka bata masa rai kuma yaga  dama ya yafe domin yanada iko ramawa , Allah madaukakin sarki zai sanya masa yardarsa a zuciyarsa kuma ya bashi babban sakamako ranar Alkiyama).   Musuc**************************************************   Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah, a madadin wadanda suka hada shirin har ya kammala musaman ma Injeniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.    
Monday, 29 June 2015 07:04

Shiri Na 27

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na yau ci gaban shirin da ya gabata ne, inda a ba'amanta ba a makun day a gabata mun kawo muku Ayoyin Alkur'ani da kuma na Ma'aikin Allah gami da na iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da mahimancin hadiye fishi, shirin nay au ma zai dora ne daga inda muka tsaya a baya  sai a biyo mu domin jin abinda shirin nay au ya kumsa amma kafin  nan, bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.   Musuc**************************************************   A Cikin Littafin Sharhin Nahjul Balaga na Sayyid Sharif Rida (RTA) an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa(babu wata Gorzantaka da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa kamar hadiye fishi yayin da rai ya bace) Sayyid Sharif Rida ya yi ta'aliki a kalkashin wannan hadisi inda yake cewa a wannan hadisi an ambaci Gorzanta mai tasiri gaske, wacce idan Bawa yayi ta zai samu sakamako mai kyau duk da cewa mutune sai ya daure kafin ya iya irin wannan juriya A Cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s)inda yake cewa Dansa ya Dana babu wani abu wanda ya fi farantawa Ma'aifinka Rai kamar hakuri da kuma hadiye fishi yayin da Rai ya bace). har ila yau a cikin wannan littafin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa: (babu wata Gorzanta da bawa zai yi kuma ya samu babban sakamako daga wajen Allah madaukakin sarki kamar Hadiye fishi lokacin da rai ya bace a yayin  zuciya ke kokonto ta dauki fansa ko kuma tayi hakuri, a wannan lokaci sai bawa ya yi Gorzantaka ya fifita yin hakuri tare da hadiye fishinsa kuma ya mayar da komai ba komai ba ba shakka wannan zai samu sakamakon mai kyau a wajen mahalicinsa). hakika hadisai da dama sun yi bayyani dangane da mahimancin  hakuri da kuma hadiye fishi yayin da Rai ya bace sannan kuma ya bayyana irin kyakkyawan sakamako dake tattare da wannan aiki mai albarka kuma hakuri tare da hadiye fishi na sanya mai shi samun izza da buwaya gami da daukaka a tsakanin Mutane a Duniya da kuma samun izza a Lahira, a cikin littafin Tuhful Ukul na Ibn Shu'ubatul Bahrani yardar Allah ta tabbata a gareshi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) na cewa:( abu uku wanda ya kasance ya nada su zai kasance shugaba, na farko mai hadiye fishinsa a yayin da Rai da bace, na biyu yin afuwa da yafiya ga mumunan abu sai kuma na uku sada zumunci ga 'yan uwa da abokanai tare da taimakawa wadanda suka yanke zumuncinsu a gareshi).   Musuc**************************************************   Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a cikin littafin Kafi Sikatu Islam kulaini ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa:(babu wani Bawa da zai hadiye fishinsa yayin da ransa ya bace sai Allah madaukakin sarki ya kara masa Izza a Duniya da Lahira kuma Hakika Allah madaukakin sarki na cewa:(wadanda suke ciyarwa cikin halin yalwa da guntsi ,da masu hadiye fushi, da masu yafewa Mutane, Allah kuwa yana Son masu kyautatawa.)suratu Ali Imran Aya ta 134 bayan kuma ya karanto wannan Aya Sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa kuma sai Allah madukakin sarki ya saka masa da Aljanna a madadin hadiye fishinsa da yayi). a cikin littafin Mishkatul Anwar na Sheik Tabrasi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yana cewa: (duk Mutuman da aka zalunta kuma aka kaddara zai rama zaluncin da aka yi masa sannan bai rama ba, Allah madaukakin sarki zai canzamasa da Izza a madadin hakurin da yayi na kin ramawa). aksin wannan riwaya kuma duk wanda ba ya iya hadiye fishinsa a yayin da Ransa ya bace zai fada cikin kaskanci da kuma tsangoma na Makiya. a cikin littafin Kanzul Fawa'id an ruwaito wani bangare na wasiyar Lukmanul Hakim (a.s) da yayiwa Dansa, a cikin wannan Wasiya Lukamanul hakim (a.s) na cewa Ya Dana duk wanda yake son yardar Allah to dole ya sabawa Son Ransa, duk wanda bai sabawa son ransa ba, ba zai hadu da yardar Ubangijinsa ba, kuma duk wanda ya kasa hadiye fishinsa to zai fuskancin muzguna da kuma dariyar makiya). daga karshe masu saurare bari mu kawo muku wani kauli da Sheik Muhamad Salih Almazandarani a kan hadiye fishi yayin da Rai ya bace,a cikin littafinsa na Sharh Usulul Kafi shek na cewa Hakika Hadiye fishi yayin da Rai ya bace wata falala ce mai karfi da Allah madaukakin sarki ya baiwa bayinsa mumunai kuma na daga cikin girman daukaka na Adamtaka).   Musuc**************************************************   Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah, a madadin wadanda suka hada shirin musaman ma Injeniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.  
Monday, 29 June 2015 07:03

Shiri Na 26

Written by
Masu saurare Assalamu Aleikum barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen Dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi , daga cikin Siffofin Allah madaukakin sarki a kwai cewa Allah madaukakin sarki baya wani aiki ba tare da manufa ba kamar yadda yake cewa a cikin Alkur'aninsa mai girma ban halaci Mutune da Aljan ba sai don su baitamin , idan muka duba cikin rayuwar Annabawansa tare da waliyansa makusanta za muga cewa suma sun suffanto da irin wadannan siffofi kyawawa ma'ana za kaga duk aiyukan da suka yana da manufa babu wasa a cikinsa.amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.   Musuc*************************************************************   Masu saurare aiki tare da manufa shine hakikanin hikima, kamar yadda aka ruwaito cikin Tafsirul majma'ul bayan dga Aliyu bn Asbat yana cewa wata rana na shiga Garin Madina kan hanyata ta zuwa kasar Masar sai na shiga wajen baban Ja'afar Muhamad bn Ali Arrida (a.s) a wancan lokacin Imam(a.s) nada kimanin shekaru hamsin  a Duniya sai na kasance ina tunanin kan yadda zan siffanta shi ga Mutananmu  idan na isa Masar wato ganin cewa yana da yawan shekaru,sai Imam (a.s) ya kalleni sannan yace maniYa Ali Hakika Allah madaukakin Sarki ya sanya Imamanci ko khalifanici  kamar yadda ya sanya a annabci sai Imam (a.s) ya karanto wannan ayoyi guda biyu ta farko itace ولما بلغ أشده واستوى آتيناه حكما وعلما" wato lokacin kuma da yakai karfinsa ya kuma kammala ,sai muka bashi hukunci da ilimi.sannan kuma  ya kara karanto wannan Aya  kamar haka واتيناه الحكم صبيا"، kuma muka bashi annabci tun yana karami . wato idan aka  hada wadannan Ayoyi guda biyu  wato Imam (a.s) yana nifin cewa kamar yadda Allah madaukakin sarki ke bayar da hukunci ga Dan shekaru 40 haka zalika yake bayarwa ga yaro dan karami ko kuma jariri. Masu saurare wadannan kyawawen siffofi na Allah madaukakin sarki tare da Annabawansa sun tabbatu a tafarkin Imamai na iyalan Gidan Ma'aikin Allah tsarkaka tun farkon rayuwarsu, misali Imam Hasan Askari (a.s) ya shahara wajen kyawawen Dabi'u irin na Kakansa Ma'aikin Allah Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka wajen kyautarsa,nutsuwarsa,karamcnisa, kamin  kansa da saurensu ,haka zalika tun yana Dan karami yayi fice ga  sarakai da Maliman lokacinsa, a cikin litattafan Duraru Asnaf,Nurul Absar da Sawa'ikul muhrika an rawaito wani hadisi yana cewa  wata rana Bahlul ya ga Imam Hasan Askari (a.s)yana kuka ,lokacin  kuma yana yaro dan kankane , a yayin da sauren yaran suke wasa  a kusa das hi. sai Bahlul yayi tsammanin cewa Imam Hasan Askari (a.s) yana kuka ne sanadiyar ko yaran nan sun amshe masa abin wasansa sai yace wa Imam Hasan (a.s) shin kana so in siyamaka abin wasa? Sai Imam Yace masa ba a halicemu ba don wasa sai Bahlul yace to don mi aka haliccemu ? sai Imam (a.s) yace masa don neman ilimi da Ibada sai Bahlul yace daga ina ka samu wannan? Sai Imam (a.s) yace daga Fadar Allah madaukakin sarki  "أفحسبتم أنما خلقناكم عبثا، وأنكم إلينا لا ترجعون" ga fassarar Ayar (Allah ya ce da su ) ko kuna tsammani ne cewa mun halicce ku ne da wasa kuma ku ba za a dawo da ku gare Mu ba.   Musuc***********************************************   Masu saurare daga cikin amfanin gudanar da  aiyuka tare manufa da kuma nisantar wassani shine Mutune ya tsarkake halayansa daga almubanziranci ko kuma banzatarwa domin  irin yauni da Dan Adam yake jin cewa yana da shi  .wannan shine irin wasiyar da Imaman na iyalan gidan Ma'aikin Allah ke yi.misali idan muka dubi riwayar da sheik kulaini ya rawaito cikin littafinsa mai suna Alkafi daga Yasir hadimin Imam Rida (a.s) yana cewa wata rana wasu bayi guda biyu daga cikin bayin Imam Rida (a.s) sun kasance suna cin Touffa sai suka gutsiri kadan daga ciki, sannan  suka yi jifa da sauren  sai Imam Rida (a.s) yace masu Subhanallah idan kun wadatu da shi  to a kwai masu bukatarsa , idan  ku ba kwa ci, to  ku ciyar da mabukata.   Masu saurare daga cikin Dabi'un Allah madaukakin sarki bada mafuka ga wanda ya nemi mafukar a gareishi ko da ya kasance mai aikata sabo ne , hakika wadannan kyawawen dabi'u sun tabbatu ga iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka , idan muka dubi irin taimako da Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin (a.s) yayi ga bani umaiwa yayin da suka nemi mafuka a gareishi bayan sun aikata mumunan aiki ga Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsakaka a waki'ar karbalah, imam ya baiwa iyalan Marwan mafuka kamar yadda ya bukata yayin da Al'ummar Garin Madina suka yi bori a gareisu, a wata waki'a da ake kiranta واقعة الطف الدامية ko kuma waki'atul hur,maliman tarihi sun rubuta cewa bayan mumunan aikin da yazid dan mu'awiya ya aikata a Karbala'a na kashe iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka musaman ma shugaban samarin Aljanna Imam Husain (a.s), Mutanan  Garin Madina sun yi wani bori  ga shugabanin Bani Umaiya dake wannan Gari mai tsarki inda suka kai hari da nufin kashe Gwamnan bani Umaiya da manyan 'yan siyasarsu wadanda suke shugabanci a Garin Madina sai suka gudu,amma  kafin su gudun sun  nemi gurin da za su bar Matansu da 'ya'yansu  sai Imam Zainul Abidin (a.s) ya karbesu ya ciyar da su ya shayar da su kamar iyalansa ya basu kariya har saida ya tabbatar suna cikin aminci.shahararen malamin Tarihi nan sheik Tabri ya rawaito hadisi a cikin shahararren littafinsa na tarihi wato Tarihul Tabri  inda a cikin Hadisin aka ce Hakika Aliyu bn Husaini(a.s) ya baiwa iyalan Marwan bn Hakan mafuka yayin da  za su gudu daga Garin Madina zuwa Sham saboda borin Mutanan Madina a gareisu.Tabri ya rawaito hadisi daga Muhamad bn Sa'ad shima daga Muhamad bnUmar yana cewa yayin da Mutanan Madina suka fidda Usman bn Muhamad (wato shine Gwamnan Bani Umaiya a wancen lokaci )daga Garin Madina sai Marwan bn Hakam ya bukaci Ibn Umar ya baiwa iyaliansa mafuka sai Ibn  Umar yaki amincewa sai yaje wajen Imam Aliyu bn Husain (a.s) ya bukaci ya baiwa Iyalansa mafuka sai Imam (a.s) ya amince da bukatar tasa ya ciyar da su ya shayar da su kamar yadda yake ciyar da iyalansa ya basu mafuka har saida ya tabbatar da cewa suna cikin aminci.   Musu**************************************   Masu anan shirin namu zai dasa aya sai kuma a Mako na gaba idan  Allah ya kaimu za a jimu dauke da wani sabon shiri a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da hada shirin aka saurara ni  madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.    
Monday, 29 June 2015 07:02

Shiri Na 25

Written by
Masu saurare Assalama Aleikum barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin kyawawen Dabi'un Musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,daga cikin siffofin Allah madaukin sarki akwai  jinkiri ga bayinsa don basu dama gyara kusruren da suka aikata, hakika Allah madaukakin sarki yayi Alkawalin cewa sai ya tabbatar da Addininsa a doran kasar baki daya ,sannan kuma yayi wa bayinsa Salihai alkawalin gadar masu Gasarsa ,saidai wajen tabbatar da hakan, Allah madaukakin sarki ba ya gaggawa , saboda ya baiwa gungu gungu masu ganin cewa suna iya cikekken milki ba tare da kuskure ba  gudanar da na su milkin,daga karshe ya sanya Hukumarsa ta adalci ta mallaki Duniya gaba daya wanda kuma babu wata hukuma da ta iya gudanar da miliki  cikin Adalci  da masalahar Al'umma kuma ta mallaki duniya  gabaki daya in bat a Allah madaukakin sarki ba.masu saurare irin wadannan kyawawen Dabi'u na yin jingiri wajen meda martani sun tabbatu ga iyalan gidan Manzan Rahama tsarkaka musamman ma wajen Mu'amalarsu da sauren Al'umma.amma kafin mu shiga shirin ba ri mu saurari a binda a kayi mana tanadi a kan faifai.   ************************MUsuc************************** Masu saurare shirin na mu na yau zai dubi ne kan  tafarkin shugabanmu Imam Bakir(a.s) a cikin riwayar da Abi bakar Hadrami ya rawaito inda yake cewa : yayin da aka kai Imam Bakir(a.s) birnin Sham wajen Hisham bn Abdulmalik Imam Bakir (a.s)ya kasance a kofar Majalisin Hisham bn Abdulmalik kafin a bada umarnin shugowarsa ,sai  Hisham bn Abdulmalik yacewa fadawansa tare da na hannun damarsa daga cikin kabilar Bani Umaiya. A lokacin da kuka na muzanta Muhamad bn Ali to kuma ku muzanta shi daya bayan daya.sannan ya bada izini a shigo da Imam(a.s).   A yayin da Abu Ja'afar (a.s) ya shigo sai ya daga hanunsa yayi sallama ga Mutanan gurin baki daya yace Masu Assalama Aleikum.sannan ya samu guri ya zauna , ganin haka sai bacin rai ya kara turnike Hisham bn Abdulmalik  saboda Imam bai je wajensa ba yayi masa Gaisuwa ta musaman a matsayin khalifa sannan kuma ya zauna ba tare da ya nemi  izininsa ba,sai ya juya wajen Imam (a.s) ya fara sukan lamirinsa tare da muzguna masa yana cewa ya Muhamd bn Ali har yanzu ka san cewa a kwai me rike da sandar Musulmi yana nifin kansa wato ya nufin shine Imami ko khalifa na wancen lokaci , ya fadi magangannu  masu yawa na muzgunawa Imam(a.s). Bayan yayi shuru sai Mutanan dake zaune a fadarsa suka fara kalaman batanci tare da sukan lamirin Imam (a.s) daya bayan daya ,har na  karshen ya gama ba tare da ya katse masu maganarsu ba  kuma bai ce masu komai ba , bayan sun gama sukansu da cin zarafi  sai Imam (a.s) ya tashi sannan yace masu yaku Mutane ina za kujeson ko kuma ina ake son zuwa da ku, daga garemu ne Allah ya shiryar da na farkonku, kuma daga garemu ne za'a kamala shiryar da na karshenku, idan kuna tsammanin kuna da milki mai gaggawa to mu kuma  muna da milki mai jinkiri kuma babu wani milki bayan namu milkin domin muke da kyakyawar makoma , Allah madaukakin sarki yana cewa kyakyawar makoma ta masu tsoran Allah ne.   musuc   masu saurare haka ta wannan hanya Imam(a.s) ya bayyanawa  hukumar umawiya cewa babu wata Daula inba ta iyalan gidan manzan Allah ba kuma itace daular karshe wadda zata wanzar da adalci a dororn kasar baki daya wato anan Imam Bakir (a.s) yana nifin daular jikansa Imam Mahdi(a.s), bayan wannan bayanai na Imam Bakir(a.s) sai aka bada umarni a kaishi Gidan kaso.a ci gaban wannan riwaya ta Abi Bakar Hadrami an bayyana cewa sai aka yi umarni a fice da shi Gidan Kaso, a lokacin da aka kaishi sai ya ci gaba da da'awarsa kafin wani lokaci dukkanin 'yan gidan kason sun zama mabiya tafarkin mazhabar Ahlulbait (a.s), da ganin haka sai shugaban Gidan kason ya ruga zuwa wajen Hashim yace masa:ya shugaban mummunai ba shakka  ina fargabar cewa an kusa a  rabaka da  Al'ummar Garin  Sham sannan ya bashi labarin abinda ke faruwa a Gidan Kaso.wato irin abinda Imam Bakir (a.s) ya aikata a gidan Kason ,wanda ya rawaito riwayar sai yace sai aka bada umarni a mayar da shi Garin Madina shi da sahabansa sannan kuma aka umarci dukkanin 'yan kasuwa kadda su sayar masu da komai a hanyarsu ta komawa Madina sai suka kasamce ba su ci komai har zuwa kwanaki 3,bayan sun isa Garin Madayyana  sai aka rufe kofar Garin ,a wannan lokaci  sahaban Imam (a.s) sai  suka meka kukansu wajen Imam(a.s) saboda tsananin yunwa da ishurwa sai Imam(a.s) ya hau babban dutsi  na wannan Gari, domin yayiwa 'yan Garin Madayyana jawabi sai ya daga muryarsa don kowa da kowa ya ji yace yak u Mutanan wannan Gari . nine Bakiyatullah wanda Allah yake nifi a cikin Alkur'ani mai Girma بقية الله خير لكم إن كنتم مؤمنين وما أنا عليكم بحفيظ". Wato abin da zai wanzu a gare ku na alheri a wurin Allah shi ya fi muku in kun kasance muminai.ni kuma ba mai gadin ku ba ne''. Wanda ya rawaito wannan hadisi ya ci gaba da cewa  a cikin Al'ummar Garin  Madayyana a kwai wani Lattijo mai yawan shekaru sai ya tashi ya tattara Al'ummar Garin sannan yace masu ya ku Al'ummar wannan Gari, wallahi wannan  kira irin da'awar Annabi Shu'aibu(a.s) ce, don haka idan baku bude kasuwanninku ba ga wannan Bawan Allah to Azaba na iya sabka a gareiku imam daga  samanku ko kuma daga kasan digadiganku, don haka ko da ya kasance  za ku karyatani a abubuwan da suka gabata , to a wannan karo ku Gasgantani sannan kuma ku yi biyayya  a gareini domin nib a wani bane illa mai Galgadi ne a gareiku.daga jin wannan Magana sai suka gaggauta bude kasuwaninsu ga Imam Abi Ja'afar (a.s) tare da sahabansa.sai wannan labarin na lattijo ya isa wajen Hisham bn Abdulmalik, dan jin haka sai ran Hisham ya kara baci sannan ya tura cikin gaggawa aka kawo masa wannan Lattijo , wanda ya rawaito wannan hadisi yace babu  wani wanda ya san yadda  Hisham bn Abdulmalik yayi da wannan Lattijo.   Musuc   Masu saurare  ganin cewa lokaci na hararrenmu a nan za mu dasa aya, sai kuma a Mako na gaba idan  Allah ya kaimu za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da hada shirin aka saurara ni  madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.    
Monday, 29 June 2015 07:01

Shiri Na 24

Written by
Masu saurare Assalamu Aleikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen Dabi'un musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi.shirin namu na yau zai yi dubu ne kan wasu riwayoyi guda biyu bisa tafarkin iyalan Gidan Manzon Allah tsarkaka,Ta farko na ishara ne kan irin falala da Allah madaukakin sarki ya basu na taimakon bayinsa tare da Izinisa, ta biyu kuwa na ishara ne kan Hakuri  amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanada a kan inji. ********************Musuc*************************   Masu saurare riwayarmu ta farko za ta yi Magana ne kan bada karfin gwiwa da kuzari ga Mummuni da Mutanan da kuma aka zalinta a cikin riwayar da Sheik Tusi ya rawaito cikin Littafinsa mai suna Al'amali daga Kafur Khadimin Imam Hadi(a.s) yana cewa Yunus Annakashi wato ana nifin Yunus mai yin zane ya kasance yana  zuwa wajen Imam Hadi (a.s) a boye  yana yi masa Hidima wata rana ya zo wajen Imam yana karkarwa sai yace ya shugabana na wasiya a gareku ku kula da iyalaina sai Imam(a.s) yace: mike faruwa ? sai Yunus yace nayi niya zan bar Garin. Sai Imam ya tambayesa cikin milmishi inda yace masa a wani dalili zaka bar Gari? Sai yace Musa bn Baga ya bani dutsinsa na  zobe ba wata tsada da shima  don inyi masa zane ,wajen yin zanan sai na karya shi ya rabu gida biyu kuma Alkawalin da mu kayi da shi gobe ne kuma kasan shi Musa bn Baga sakayyarshi shine imma bulala Dubu   ko kuma Kisa domin  Musa bn Baga shine babban Komandan Yaki  da Khalifan Abbasiyawa Ma’amun sai Imam Hadi(a.s)yace masa ka koma Gidanka zuwa Gobe babu abinda zai faru sai Alkhairi.a washe Gari zai Yunus ya dawo wajen Imam Hadi(a.s) yana karkarwa yana cewa Musa bn Baga ya turu in bashi dutsinsa na zobe sai Imam Hadi(a.s) yace masa ka koma Gidanka babu abinda zai faru in ba Alkhairi ba,Musa mai zane yace  idan na koma mi zan ce masa ya shugabana ? sai Imam(a.s) yayi milmishi  kaje wajensa ka saurari abinda zai ce maka babu abinda zai faru sai Alkhairi.a yayin da Yunus ya tafi bayan wani Dan Lokaci sai gashi ya dawo yana Dariya, Yace Ya shugabana ga abinda yace mani dama wannan Dutsi ina so ne in bayar da shi  kyauta ga daya daga cikin Makobta na amma yanzu sai su biyun sun fara jayayya  tsakaninsu ko za ka iya raba Dutsun gida biyu sai mu kara maka wani abu ?sai Imam (a.s) ya daga hannu ya ce Ya Ubangiji Godiya ta tabbata a gareka da kasanyamu daga masu maka Godiya ta Hakika. Kai kuma mi kace masa ?sai Yunus mai Zane yace : ce masa na yi ya bani lokaci inyi tunani kan cewa ko zan iya  rabashi gida biyu.sai Imam (a.s) yace kayi daidai. *******************Musuc******************************* Masu saurare hakuri na daga cikin kyawawen Dabi’un Allah madaukakin sarki domin shi kadai ne ke iya intar da mummuni daga saukin fishi ko kuma kyashi da makamantansu sannan ya na iya hauda mai shi zuwa kololuwar  Martaba na dan Adamtaka, masu saurare riwayarmu ta gaba na magana kan Hakuri musaman ma kan yadda iyalan Gidan Ma’aikin Allah tsarkaka suka tabbatu da irin wadannan kyawawen Dabi’u ,a riwayar da Sheik Mufid ya rawaito cikin Littafinsa mai suna Kitabul Irshad . ga abinda riwayar ke cewa wata rana wani Mutune daga cikin Mutanan Gidan Imam Aliyu bn Husain amincin Allah ya tabbata a garesu ya tsaya a Gaban Imam, yayin da Imam(a.s) ke zaune a tsakanin Almajiransa yana basu Ilimi sai wannan Mutune yayi ta gayawa Imam(a.s) Maganganu marassa dadi kai har ma yayi ta zakinsa amma Imam bai ce masa komai ba, ya kari masifarsa ya tafi, bayan ya tafi sai Imam (a.s) yacewa Almajiransa hakika kunji abubuwan da wannan Mutune yace mani to nima ina so ku biyoni kuji irin maida martanin da zanyi masa.sai Imam (a.s) ya sanya takalminsa ya fara Tafiya yana karanta wannan Aya.والكاظمين   الغيظ والعافين عن الناس والله يحب المحسنين  ma'anar wannan Aya shine da masu hadiye fishi da masu yafe wa Mutane Allah  kuwa yana Son masu kyautatawa .wanda ya rawaito wannan Hadisi yace dama mu kaji Imam (a.s) na karanta wannan Aya muka san cewa ba zai masa komai ba.a yayin da muka bi Imam har muka isa Gidan wannan Mutune sai Imam (a.s) yayi sallama sannan yace ace masa Aliyu bn Husain ne .sai wannan Mutune ya fito cikin fishi, da ka gansa kasan cewa yazo ne da neman tashin Hankali domin a tunanisa Imam (a.s) yazo ne ya maida masa Murtani kan irin cin mutuncin da yayi masa .sai Imam Aliyu bn Husaini (a.s) yace masa ya kai Dan Uwana Hakika dazu ka tardani Majlisina ka fadi abubuwa daban daban a kaina. Idan ya kasance abubuwa da ka fada Gaskiya ne to ina neman Gafara ga Allah madukakin sarki a kan hakan, idan kuma abubuwan da ka fada a kaida kuskure ne to ina rokon Allah madaukakin sarki ya Gafarta maka.sai wannan Mutune ya sunbaci Imam (a.s)sannan yace  abubuwan da na fada a kan kazafi ne nai maka, don Allah ka yafe mini domin nine da farko ya kamata inzo wajenka in nemi Gafara a wajenka sai Imam (a.s) ya rungume shi sannan yace Allah ya gafarmaka. *******************Music***************************** Masu anan zamu dasa Aya saboda Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu da wani sabon shiri a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni madugun shirin nike muku fatan Alkhairi wassalamu Aleikum wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.    
Monday, 29 June 2015 06:58

Shiri Na 23

Written by
Masu saurare Assalama Aleikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin kyawawen Dabi'un Musulinci wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi .shirin na mu na Yau ci gaba ne a shirin da ya gabata kan tafarkin shugaban Mummunai Imam Ali (a.s) saidai a yau bayan irin wasiku da wasiyoyi da Imam (a.s) ke aikewa wakilansa a Gariruwa daban daban muna dauke da wasu hadisai kan tafarkin jikokinsa tsarkaka  guda biyu wato Imam Ja'afar bn Muhamad Alkazim da kuma Dansa Imam Ali bn Musa Arrida (a.s) wanda dukkaninsu ke Magana kan irin tausayi da Allah madaukakin sarki ke yiwa bayinsa amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan inji. Daga cikin irin wasiyoyi da Shugaban Mumunai Imam Ali (a.s) ke yiwa wakilansa a yayin da ya nada su a gariruwa daban daban na Musulinci ga wasiyar da yaiywa Abdullah bn Abas yayin da ya nada shi a matsayin wali na Garin Basara sai Imam Yace masa Ka zamanto mai walwala da shinfidar fuska  a tsakanin Al'ummarka mai rahama da adalci wajen hukunci ga Al'umma sannan ka kiyayi yin fishi domin shi fishi wani makami ne daga makaman shaidani. Har ila yau daga cikin irin wasiku da shugabanmu Imam Ali (a.s) ke aikewa wakilansa yana cewa bayan yayiwa Annabi salati : haki ne a kan ko wani magabaci na kadda ya cansa finsa a kan mutanan da yake gabata kan irin Falala da Allah madaukakin sarki ya bashi sannan ya zamanto mai adalci wajen raba dukiyar da Allah madaukakin sarki yayi umarni a raba tsakanin bayinsa kadda ya zamanto mai fifiko ga 'yan uwansa , abukaninsa ko kuma zuriyarsa sannan ya zamanto mai adalci kan yadda zaiyi amfani da dukiyar Baitul mal.ku  saurara hakinku ne a kaina da kadda na boye maku ko wani irin sirri na milki in ba batutuwan da suka shafi yaki ba,sannan kuma in shawarce ku a dukan lamura ba tare da bata lokaci idan har ba hukuncin  Allah madaukain sarki ba ne ba,sannan dukkaninku a waje na guda ne, babu wani babbanci ganin irin wannan Mu'amala da Alllah subhanahu wa ta'ala ya umarceni inyi da ku babar ninima ce a gareku kuma wajibi ne ku Godemasa a kan hakan sannan kuma wajibi ne a gareku ku yi mani biyayya. Har ila yau masu saurare irin wadannan kyawawen Dabi'u na Allah madaukakin sarki sun tabbatu a wajen shugabanmu shugaban Mummunai Imam Ali(a.s) wajen Mu'amalarsa da Mutunan wadanda ba Musulmi ba a yayin da suka kai Karen shugabansu kan yanayin da yake Mu'amala da su.sai Imam Ali(a.s) ya rubuta wasika zuwa ga walinsa na wannan gari inda a cikin wannan Wassika yake cewa da dama daga cikin Mutananka suna kokawa da kai kan yadda kade Mu'amala da  su cikin fishi da bacin rai tare da muzguna masu da kuma kaskantar da su , sai naga bai kamata ba kayi irin wannan Mu'amala da su saboda Addininsu,sannan bai kamata ka muzguna masu saboda irin Alkawalin da muka kulla da su.ka za manto mai sassauci da tausayi wanda hakan zai kore irin kankin da suka shiga sannan kayi Mu'amala mai kyau tare da su a cikin tausayi.har ila yau ka zamanto mai wasa da dariya tare da su don kusanto ga Addinin Allah.wannan shine abinda muke bukata daga gareka idan Allah ya yarda. Masu saurare irin wadannan kyawawen Dabi'un Allah madaukakin sarki na tausayi ga bayinsa sun tabbatu ga jikokin Manzon Allah da Imam Ali (a.s)  wato Imam Kazim da Imam Rida (a.s)wadanda baban manufar hakan shine nisanta daga cutar da wani ko kuma wasu bayin Allah. A cikin Littafin Kurbul Isnad an rawaito riwaya daga Humairi tare da sanadinsa wanda ke komawa zuwa Mufadal bn Kais inda yake cewa naji baban Hasan na farko wato yana nifin Imam Kazim (a.s) yayi ranzuwa kan cewa ba zai yi magana ba da Muhamad bn Abdullahi Al'Alkat har abada saboda shi Muhamad din na Anfani da Mu'amalarshi tare da Imam Kazim yana kirkira karya sannan ya danganta ta da Imam Kazim (a.s) a daliln haka, ya batar da  Al'umma da dama saboda Mutane suna kama zancensa ganin yanda yake kai kawo wajen Imam Kazim (a.s) tare da yadda Imam (a.s) ke kaimasa Ziyara wanda hakan a hakikanin Gaskiya na cutar da kansa da kuma Al'umma mabiya tafarkin Mazhabar iyalan gidan Monzon Rahama tsarkaka,sai Mufadal Bn Kais wanda ya rawaito wannan riwaya yace a raina sai nace shin yanzu wannan shine umarni  da Imam ke mana na yin biyayya tare da zumunti?yanzu kuma gashi  yayi ranzuwa kan cewa ba zaiyi magana da Dan kawunsa ba har abada? sai Imam Kazim (a.s) ya kallesa sannan yace masa  wannan hanya itace zata toshe cutar da Mutane da kuma cutar da kansa saboda idan Mutane suka fahinci cewa bana yi masa magana to kaka ba za su kama zancensa ba sannan shima zai kama bakinsa daga anbatona sai hakan ya zamanto Alkhairi a gareishi da ma Al'umma gaba daya. A cikin littafin mai suna Uyunu Ahkbaru Rida (a.s) an rawaito Hadisi daga Umair bn Buraid yana cewa na kasance wajen baban Hasan Imam Aliyu bn Musa (a.s) sai aka anbaci sunan Muhamd bn Ja'afar shima saboda irin mummunar Mu'amalarsa da imam (a.s) kan yadda yake kirkira karya yana danganta ta da Imam sai Imam (a.s) yace nayiwa kaina alkwali ba zan hada runfa guda ba da shi sai Umair bn Buraid yace a cikin tsuciyarsa wannan shine umarni da Imam ke mana na biyayya da kulla Zumanci ?amma yana fadan irin wannan kalma a kan kawunsa sai Imam Rida (a.s) ya Kalleshi sannan yace masa wannan shine abinda yafi da cewa domin duk lokacin da yazo wajena sannan ya firta maganar da banfada ba Mutane zasu gasgantashi, amma idan bai zo waje na ba kuma nima ban je wajensa duk abinda ya fada a kaina Mutane ba zu amince ba. Masu saurare ganin cewa lokacin da ake debawa shirin ya kawo karshe a nan za mu dasa aya sai kuma a maku mai zuwa za a jimu da wani sabon shirin a madadin Aminu Ibrahim kiyawa d aya hada shirin aka saurara ni jagoran shirin ni ke muku fatan alkhairi wassalamu aleikum wa rahamtul    
Wednesday, 04 February 2015 07:55

Shiri Na 22

Written by
Masu saurare Assalama aleikum,barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyukan da kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin hanyar kyakyawar rayuwa a zaman duniya da na lahira, shirin na yau zai yi dubu ne a kan wasu wasiyoyi na Ma'aikin Allah da kuma iyalan tsarkaka wadanda suke bayyanni a kan afuwa, sai a biyo mu domin jin abinda shirin na yau ya kumsa   Musuc***********************************************   A cikin Littafin Makarimul Akhlaq na babban malamin hadisin nan sheik Abul kasim kufy, an rawaito hadisi  inda a cikinsa aka ce wata rana wani bawan Allah ya je Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka tare da neman ya yi masa Nasiha sai Manzon Allah (SWS) ya ce nah ore ka da tsoron Allah da kuma yafiya da afuwa ga Mutane).   A cikin littafin (كشف المحجة لثمرة المهجة) na sayyid ibn Tawus wanda ya rubuta shi domin yayiwa Dansa Sayyid Muhamad Nasiha, an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yana cewa shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce dansa imam Hasan (a.s) kadda ziyarar da ka ke yiwa dan uwanka ta kasance ta fi wanda ya yanke zumunci a gareka(ma'ana ka sada zumunci ga wanda ya yanke zumuncinsa a gareka kamar yadda kake ziyartar dan uwanka na jini mai ziyartarka a ko wani lokaci) sannan ya ci gaba da ce masa kadda ka kasance daga cikin wadanda munanan aiyukan suka rinjayi kyawawa, kuma wadanda rowarsu ta irnjayi alherinsu ko kuma kyautarsu,kuma ga wadanda kuskuransu ya rinjayi aikukansu na falala kuma na mustahabi, kadda ka zamanto masu giramama zalincin da aka yi masu domin yin haka zai sanya zuciya ta dinka damuwa da kuma kokarin daukar fansa, wannan zai yi babbar illa aiyuka kyawawa da kuma yafiya da afuwa).   A cikin littafin Da'a'imul Islam na babban malamin nan alkali Na'aman Almagribi an rawaito hadisi daga shugaban muminai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yayin day a rubuta wasika zuwa ga wasu daga cikin sahabansa yana mai yi masu Nasiha (ku kasance masu kyautatawa ga wadanda suka muzguna maku,kuma masu riko ga masu kyautata maku, masu afuwa ga wadanda suka zalunce ku, masu galgadi ga masu taimakonku, ku baiwa wadanda suka haramta maku, kuma ku zamanto masu tawadu'I ga wadanda suka baku, kuyi godiya mai yawa ga Allah madaukakin sarki a kan matsayin da Allah ya yi maku, kuma ku gode masa a kan duk wata jarrabawa da ta sameku).   Musuc**************************************************   Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi ishara ne kan wani hadisi da aka ruwaito daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) wanda yake bayyani fifikon afuya da yafiwa a kan ramuwa,a cikin littafin kafi na sikatu islam kulaini an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) na cewa yin Nadama a bisa yin afuwa ya fi  kyau kuma ya fi sauki a bisa yin nasama kan ramuwa). Yayin da maluman hadisi suke ta'aliki a kan wannan hadisi sun ce ba shakka wannan hadisi yana karfafa ruhi wajen aikata alheri ga mutane kuma yana rage sha'awar daukan fansa ga wadanda aka zalunta da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yin yafiya da afuwa.   A cikin littafin Ma'anil Akhbar na sheik Saduk (r.t.a) an ruwaito hadisi daga  Jara'ihul madani ya ce Abu Abdullah Imam Sadik (a.s) ya ce da ni shin kana so in labarin  kyawawen dabi'u? sai Yace Na'am: yafiya da kuma tawadu'I ga Mutane, da kuma rashin kirman kai, Mutune ya kasance mai ganin kansa daya dake da uwansa ko min dukiyarsa da matsayi, kuma ya kasance mai anbaton Allah da yawa). a cikin littafin tuhuful Ukul na ibn Shu'uba Alharani an rawaito wata wasiya da shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yiwa Abdullah bn Jundab, a cikin wasiyar Imam Sadik (a.s) na cewa Ya Jundab  ka ziyarci duk wanda ya yanke ziyartarka,  ka baiwa duk wanda ya hanaka, ka kyautatawa wanda ya muzanta maka, ka yi aminci ga wanda ya zageka, mai adalci ga wanda ya yakeka, mai afuwa ga wanda ya zalunce ka kamar yadda kake so a yi maka afuwa, ka  dauki darasi a kan afuwar da Allah madaukakin sarki yake yi ga bayinsa, shin ba ka ganin cewa Allah madaukakin sarki yak an fitar da Ranarsa ga bayin Allah na kwarai da kuma fajirai, haka zalika yak an saukar da ruwansa ga salihai da kuma masu sabo). Muna rokon Allah madaukakin sarki da ya bamu damar yin aiki da wadannan wasiyoyi na ma'aikin Allah da kuma iyalan gidansa tsarkaka tare da yin koyi das u wajen tabbatar da umarnin ubangiji domin shi Allah mai ji ne kuma mai karbar du'a'I ne.   Musuc**************************************************   Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.            
Wednesday, 04 February 2015 07:54

Shiri Na 21

Written by
Masu saurare Assalama aleikum,barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyukan da kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin hanyar kyakyawar rayuwa a zaman duniya da na lahira, shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin yin Afuwa ga Mutane domin shima na daga cikin zarkakakun dabi'u kyawawa, sai a biyo mu domin jin abinda shirin na Yau ya kumsa.   Musuc**************************************************   A cikin littafin Mustadrakul wasa'il an rawaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayin da yake fassara wannan aya ta cikin suratu Shura'a (to duk wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata,to ladansa yana wurin Allah) suratu shura'a aya ta 40. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:idan ya kasance ranar Alkiyama sai asa mai kira ya yi kira:duk wanda ya kasance yanada wani sakamako a wajen ubangiji ya ta shi, a wannan lokaci sai ma'abuta yafiya ga Mutane su tashi, sannan su shiga Aljanna ba tare da wani hisabi ba. Allama jalil Kutbuddin Rawandi cikin littafinsa mai suna Lubbu libab, an rawaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(gungu uku suna sauka cikin Aljanna duk lokacin da suka ga dama Manzon Allah ya fara zano su har gurin da ya ce:  da kuma Mutuman day a yafe a kan zalintar da aka yi masa). A cikin littafin Adadul Kawiya an rawaito hadisi daga Annabi Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(hakika dama ko kuma lasisin da aka baiwa mai shi zabi, shine cewa Allah madaukakin sarki ya ce ba zai yi wa bawa ukuba ba kan rama zalincin da aka yi masa ba. Allah madaukakin sarki na cewa:(Sakamakon mummunan abu kuma shine mayar da kamarsa. To wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata,to ladansa yana wurin Allah, hakika shi ba Ya son masu Zalunci) suratu shura Aya ta 40. Sai Ma'aikin Allah ya ci gaba da cewa hakika wannan lasisi da Allah madaukakin sarki ya baiwa wanda aka zalunta idan yaga dama ya yafe idan kuma ya so ya rama.   Musuc*************************************************   Masu saurare barkanmu da sake saduwa, daga cikin sirrin da Allah madaukakin sarki ya yi yin yafiya da afuwa shine ta yadda bawan da aka zalunta zai yafe duk da cewa Allah madaukakin sarki ya bashi lasisin damawa. Domin haka ne ma mai yafiya ya kasance daga cikin ma'abota falala. A cikin littafin kafi an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s).yace (idan ya kasance ranar Alkiyama Allah madaukakin sarki zai tara mutanan farko da na karshe a guri guda sannan a umarci mai kira ya yi kira: ya ce ina ma'abota falala da karamci? Sai wani gungu daga cikin Mutane su tashi sai Mala'ikai su tambayesu minene falalark? Sai wannan gungu su ce mun kasance muna sada zumunci wato muna ziyartar duk wani wanda ya yanke zumuncinsa a garemu, ku muna baiwa duk wanda ya hanamu, ma'ana suna baiwa wanda ya hanasu a nan duniya, kuma  muna yin afuwa ga duk wanda ya zalunce mu, sai Mala'ikai suce masu hakika kunyi gaskiya ku shiga Aljanna).   Hakika masu saurare yin afuwa wanta hanya ce ta gyara zukatan masu sabo tare da meka sakon mai kyau na alheri a zukatan Mutane.kuma yin Afuwa garkuwa ce daga duk wani sharri.hakika a cikin littafin Mustadrakul wasa'il an rawaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda aka ce wata Rana wani Mutune ya kai karan masu yi masa hidima wajen Ma'aikin Allah Sai Ma'aikin Allah ya ce ka yi masu domin yin hakan shi zai saya ka gyara zukatansu, sai wannan Mutuman ya ce ya Ma'aikin Allah masu yi mini hidmar sun kasance har musabaka suke yi wajen aikata munanan abubuwa, sai Ma'aikin Allah ya ce masa ka yi masu Afuwa. Sai wannan Bawan Allah ya yi aikin da umarnin ma'aikin Allah ya yi masu Afuwa)   An rawaito wani hadisi daga shugaban muminai Aliyu bn abi talib (a.s) na cewa (ka lallashi dan uwanka ta hanyar kautata mishi kuma ka kare sharrinsa ta hanyar yi masa kauta).   A karshe masu saurare bari mu karanto wannan aya ta cikin suratu Imran inda  Allah madaukakin sarki ke cewa:(saboda rahamar Allah ne kawai ka tausasa masu, da ka kasance mai fishi,mai kaushin hali to da sun watse daga gurinka, sai kayi masu Afuwa, ka kuma nema masu gafara, kuma ka shawarce su a dukan al'amura.idan kuma ka tasar wa (tunkarar wani abu) to sai ka dogara da Allah, hakika Allah yana son masu tawakkali).  Suratu Imran Aya ta 159.   Musuc************************************************** Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.        
Wednesday, 04 February 2015 07:53

Shiri Na 20

Written by
Masu saurare Assalama aleikum,barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyukan da kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin hanyar kyakyawar rayuwa a zaman duniya da na lahira, a shirye-shiryen da suka gabata mun yi muku bayyani dangane da mahimancin yafiya gami afuya a tsakanin Al'umma, shirin namu na yau zai dora ne daga inda muka tsaya a shirye-shiryen da suka gabata; a shirin na yau za mu karanto muku wasu daga cikin hadisai iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka wadanda suke bayyani ga wannan maudi'i, amma kafin mu shiga shirin ga wannan.   Musuc**************************************************   Hakika shek Saduk (r.a) a littafinsa mai suna Ma'ani Akhbar ya rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) na cewa: (hakika Allah madaukakin sarki ya ware kyawawen dabi'u ga Ma'aikinsa Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka sai ku jarabci zukatanku idan sun kasance suna dauke da  su to zai ku godewa Allah madaukakin sarki kuma ku kara meka kodayinku a gareshi domin ya kara maku, idan kuma ku kaji cewa ba ku dauke da kyawayen dabi'u sai ku roki shi madaukakin sarki da ya arzita da shi.) Kuma kamar yadda aka rawaito cikin littatafan hadisai da dama ya kasance daga cikin kyawawan dabi'un Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, yin Afuwa. Sheik Ayyatullah Nury (r.a) ya rawaito wani hadici a cikin littafinsa mai suna Mustadrakul wasa'il an ce:ya zo a cikin littatafan hadisai cewa ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka bai taba dauka wa kansa fansa ba sai dai shi a kulun ya kasance yana yin afuwa ga duk wani laifin da aka yi masa. A cikin littafin Khisal na sheik saduk (r.a) an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya na cewa dabi'armu mu Ahlilbait yin afuwa da yafiya ga duk wanda ya zalunce mu). Masu saurare a cikin littafin Amaly shek Tusy (k.s) ya rawaito hadisi daga Ahmad bn Isa Al'alawy ya ce :ja'afar bn Muhamad (a.s) ya ce min idan wani mabukaci ya zo min da bukatarsa to zan gaggauta biya masa ita domin tsoron jinkirin da zanyi ya sanya ya wadatu da taimakon da ya bukata daga garemu, saurara kyawawen dabi'u sun tattaru ne bisa harufa uku sannan sai ya karanto wannan aya ta 199 cikin suratu A'araf inda Allah madaukakin sarki ke cewa: (ka yi riko da Afuwa,kuma ka yi umarni da alheri,ka kuma rabu da jahilai).a tafsirin wannan aya malima sun bayyana cewa ka ziyarci duk wanda ya yanke zumunci a gareka,ka yi afuwa ga wanda ya zalunce ka kuma baiwa duk wanda ya hana maka.   Musuc**************************************************   Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara ne da wata riwaya da aka rawaito cikin littafin Biharu Anwar inda aka ce wata baiwar Imam Aliyu bn Husain Zainul abidin (a.s) ta kasance tana zuba masa ruwa yana alwalla sai ta saki butar ta fada masa har ya samu rauni sai ya daga kansa ya kalleta sai ta karanto wannan Aya ta ce da masu hadiye fishi, sai Imam(a.s) ya ce na hadiye fishina, sai wannan baiwa ta ce da masu yafiya ga Mutane, sai Imam (a.s) ya ce Allah ya yafe miki, sai kuma wannan baiwa ta kara da cewa kuma Allah yana son masu kyautatawa. Sai Imam Zainul abidin (a.s) ya ce mata ta tafi ya 'yantar da ita saboda Allah. A cikin littafin Misbahu Shari'a an rawaito hadisi daga Imam Sadik(a.s) na cewa hakika yin afuwa da yafiya ga Mutuman dake karfin daukan fansa ko kuma ikon ramawa na daga cikin sunar murasalai kuma wannan sirri ne daga cikin sirrin masu tsoron Allah ne, tafsirin Afuwa shine kadda ka rike mutuman da ya yi maka laifi a zahiri kuma ka manta da abinda ya yi maka a badini bayan haka ya femasa, hasali ka ci gaba da kyautata masa, ka kara a kan kyautatawar da ka ke yi masa ya fi na da.  Masu saurare har abada ba za mu taba samun wata shiriya ba kamar wacce shugaban hallitu Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya zo da ita wanda kuma shine Allah madaukakin sarki ya ce ya gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa da kuma wanda ya rage ya kuma cika ni'imarsa a gareshi, ya kuma kawata shi da karamcinsa sannan ya lullube shi da haskensa na gafara da Afuwa domin wadannan siffofi guda biyu, siffofi ne daga cikin siffofin Ubangiji da ya horewa murasalansa tare da wasiyansa kuma ya sanya shi sirri daga sirrinsa domin haka ne Allah madaukakin sarki a cikin suratu Nur Aya ta 22 yake cewa: (lallai kuma su yafe, su yi rangwami, shin ku ba kwa son Allah ya gafarta muku?Allah kuwa Mai Gafara ne Mai Rahama). Daga karshe bari mu karanto wani hadisi daga shugabanmu Imam Sajjad Zainu Abidin (a.s) wanda aka rawaito cikin littafin kafi na sikatu islam kulain(r.a) a cikin wannan hadisi Imam (a.s) na cewa (babu wata bajinta da na fi so a rayuwanta kamar hadiye fishi musaman ma a lokacin da wanda yayi min laifi ya ke tunatun zan yi masa hukunci mai tsanani.)   Musuc************************************************** Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.          
Wednesday, 04 February 2015 07:52

Shiri Na 19

Written by
Masu saurare Assalama aleikum,barkanku da warhaka da kuma sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin hanyar samar da kyakyawar rayuwa a zaman duniya da na lahira, a shirye-shiryen da suka gabata mun yi muku bayyani dangane da mahimancin yafiya gami afuya a tsakanin Al'umma, shirin namu na yau zai dora ne daga inda muka tsaya a makun da ya gabata, amma kafin mu shiga shirin ga wannan.   Musuc**************************************************   Masu saurare, ayoyi da dama a cikin kur'ani mai tsarki sun bayyana cewa yafiya gami da Afuwa na kore munanan abu a tsakanin Al'umma domin haka ne Allah madaukakin sarki ya umarci masoyinsa Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka da yin yafiya gami da Afuwa, a cikin suratu Muminin Aya ta 96 Allah madaukakin sarki ya ce:(ka ingije mumunan abu da wanda ya fi kyau.Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffanta ka da shi).hakika maliman tafsiri sun fassara Kalmar wanda ya fi kyau, da afuwa tare yin yafiya ga wanda yayi munanan aiyuka tare da sakawa da kyakyawan aiki da sharadin cewa yin haka ba zai yi illa ba ga addinin musulinci. A cikin littafin Kafi an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya tura a kira masa Bashar bn Ata'I Tamimi bisa wani laifi da ya aikata, yayin da ma'aikin shugaban mumunai ya isa ga kabilar bani Asad, sai Na'im bn Dujaja Al'asadi ya tashi, ya wanke wannan bawan Allah kan zarkin da ake yi masa domin kabilarsa ta bashi goyon baya na kin amsa kirar shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) kuma ma idan har Amiri mumunin ya dage akan sai ya hukunta shi to yana iya fuskantar tawaye daga wannan kabila.sai aka dawo aka gaya masa abinda ke faruwa, sai Amiri mumunin (a.s) ya sake tura wa da a zo masa da Na'im, bayan anzo da shi sai Amiri mumunin (a.s) ya bada umarni da a yi masa bulala a kan abinda ya aikata.kafin hakan sai Na'im ya tashi yana mai cewa  Na rantse da ubngiji, wannan matsayi na tare da kai, kaskanci ne ya shugaban mumunai kuma rabuwarka da shi kafirci ne. yayin da shugaban mumunai (a.s) ya ji haka sai ya ce Ya Na'im hakika mun yafe maka domin Allah madaukakin sarki na cewa :(ka ingije mumunan abu da wanda ya fi kyau.Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffanta ka da shi). Amma kaulin ka na cewa rike wannan matsayi na tare da ni, kaskanci ne, mumunan laifi ne ka aikata, amma maganar ka ta cewa rabuwa da shi kuma kafirci ne. hakika maganarka gaskiya ce kuma ka aikata kyakyawan abu don haka wannan da wannan, ma'ana sakawa mumuna da mai kyau. Sai Shugaban mumunai (a.s) ya bada umarni da a sake shi kuma sai aka sake shi.   Musuc**************************************************   Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai fara ne da aya ta 22 cikin suratu Ra'ad inda a cikin wannan aya aka bayyana siffofin waliyan Allah madaukakin sarki:(Da wadanda suka yi hakuri don neman yardar Ubangijinsu, suka kuma tsaida salla, kuma suka ciyar daga abinda muka arzuta su da shi a boye da sarari, suke kuma ingije mumunan aiki da kyakkyawa, wadannan suna da makoma a gida (kyakkyawa). Malimai tafsiri sun fassara ma'anar ma'anar ingije mumuna da kyakkyawa da cewa ma'ana suna saka munana da kyakkyawa tare da yin yafiya gami da Afuwa. A bangare guda kuma Allah madaukakin sarki ya bayyana wa Manzon sa yadda zai yi mu'amala da wadanda ba suyi imani ba, a cikin suratu Zuhruf Aya 89 Allah madaukakin sarki na cewa: (to ka kawar da kanka daga garesu,kuma ka ce:Na kubuta (daga hakkinku ). Don haka ba da dadewa ba za ku sani). A bangare guda kuma Allah madaukakin sarki ya umarci bayinsa baki daya da yin yafiya gami da afuwa kamar yadda yazo a cikin suratu Jasiya Aya ta 14 (ka ce da wadanda suka bada gaskiya su yi afuwa ga wadanda ba sa kaunar kwanakin Allah (ma'ana ba s  kaunar su je yaki saboda Allah )don ya saka wa Mutane irin abin da suka kasance suna tsuwurwuta.) Har ila yau a cikin suratu Tagabun Aya ta 14 Allah madaukakin sarki ya ce: (Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya, hakika daga matanku da 'ya'yanku a kwai makiyanku saboda haka ku tsorace su.idan kuma kuka yi afuwa kuka yafe kuma kuka yi gafara, to hakika Allah mai yawan gafara ne Mai jin Kai). A cikin suratu Muzamil Aya ta 10 Allah madaukakin sarki ya umarci Masoyinsa da yin afuwa ga masu yi masa izgili tare da kaurace masu a bisa aiyukansu na jahilci.Allah subhanahu wata'ala ya ce: (kuma ka yi hakuri a kan abinda suke fada, ka kuma kaurace masu kyakkyawar kauracewa). Da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon mallakar zuciyarmu wajen yin hankuri tare da yin afuwa  ga duk wanda ya yi mana abinda ba daidai ba, kuma mu saka masa da kyakkyawa domin shi ubangiji tabaraka wa ta'ala mai ji ne kuma mai karbar Addu'ar bayinsa ne.   Musuc************************************************** Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.     
Page 2 of 3