An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Aminu

Aminu

bayan harin da kungiyar Ashabab ta kai kan dakarun kungiyar AU, a kudancin Somaliya, kasar Kenya ta karfafa matakan tsaro a kan iyakan kasar da kudancin Somaliya. kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya nakalto wani babban jami'in tsaron kenya a jiya Assabar na cewa, Dakarun tsaron kasar sun karfafa matakan tsaro a kan iyakar kasar da Somaliya tare da kuma da kai hare-hare ta sama da ta kasa a kan sansanin mayakan Ashabab dake kudancin Somaliya.
kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa Na kasar China ya habarta cewa a jiya Assabar mayakan Boko haram sun kai hari kan Dakarun tsaron Nijer a yankin Kablewa dake karamar hukumar Bosso na jihar Diiffa mai iyaka da Najeria, inda suka kashe Sojoji 6 tare da jikkata wasu biyar na daban.
shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO, kuma shugaban kasar Senegal Maki Sal ya yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai kasar Burkina Faso sannan ya meka ta'aziyarsa ga gwamnatin Burkinada da kuma iyalan mutanan da harin ya ritsa da su.
Ministan harakokin wajen Iran ya bayyana manufar kasar saudiya na  kawo cikas ga yarjejjeniyar da kasar ta cimma tare da manyan kasashen duniya tare kuma da kara rura wutar rikici a yankin gaba daya. Muhamad Jawad Zarif ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta iran ya bayyana cewa abin takaici wasu kasashen duniya sun yi ta kokarin sanya shamaki a yarjejjeniyar da Iran ta cimma tare da manyan kasashen duniya,bayan an cimma yarjejjeniyar wucin gadi a watan Nuwanban shekara ta 2013, magabatan birnin Riyad sun yi amfani da dukkanin karfinsu domin ganin wannan yarjejjeniya ba ta tabbata ba.ganin hakar su ba ta cimma ruwa ba, sai suke kokarin tayar da fitina tare kuma da rura wuta rikici a yankin baki daya.
Gwamnatin kasar Sudan ta yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Darfur. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa dakarun tsaron kasar Sudan sun yi amfani da karfi da ya fice kima wajen tarwatsa masu zanga- zanga da suka taro a gaban ginin Gwamnati jiya lahadi a yankin Darfur ta yamma.
Monday, 11 January 2016 07:03

Masar:An Zabi Sabon Kakakin Majalisar Kasar

Sabuwar majalisar dokokin Masar ta zabi sabon kakakinta a jiya Lahadi Kafar watsa labaran Alyaumu sabi'I ta kasar Masar ta habarta cewa bayan buda majalisar dokokin da take rufe shekaru uku da suka gabata, a jiya Lahadi sabin 'yan majalisar sun zabi Ali Abdul-ali a matsayin sabon kakakin majalisar.
Kungiyar Ansarul…ta kasar yemen ta gindaya sharadin tattaunawa  da kasar Saudiya. A wata sanarta da ya fitar jiya, Muhamad Abdul-salam kakakin kungiyar Ansarul.. ya ce ba za su shiga tattaunawa ba da magabatan Riyad matukar ba a dakatar da harin wuce gona da irin da ake kaiwa kasar sa ba. Kakakin ya ce tattaunawar da aka yi cikin wata Decembar shekarar da ta gabata a birnin suizilland ta kumshi batutuwa guda biyu ne kawai, sakin firsinonin biyar da kuma kawo karshen killacewar da aka yiwa garin Ta'az. Har ila yau kakakin ya ce harin wuce gona da irin da saudiya ke kaiwa a kasar na gudana ne kalkashin jagorancin jakadan kasar Amurka dake birnin Sana'a
Monday, 11 January 2016 06:56

Amurka Da Faransa Za Su Kai Hari Libya

Kasashen Amurka da Faransa sun bayyana shirinsu na kai hari kan 'yan ta'addar IS a kasar Libiya. Kafar watsa labarar Adiyar ta kasar Lobnon ta habarta cewa kasashen Amurka da Faransa sun sanar da kasar Aljeriya cewa tare da taimakon wasu kasashen yamma za su fara kai hari kan kungiyar IS a kasar Libiya. Magabatan washinton da Paris sun bukaci magabatan Aljeria da su bada hadi kai domin ganin ba a samu yawan asarar rayuka na fararen hula ba.
Fiye da dalibai dubu 30 ne ‘yan kasar Turkiya, aka koro daga kasar Rasha. Kafafen watsa labaran Turkiya sun habarta cewa bisa wata wasika da kasar Rasha ta aikewa ma’aikatar ilimim kasar kimanin daliban kasar dubu 30 ne da suke daukan darasi a jami’o’I daban daban na kasar Rasha aka kore su.
‘Yan adawa a kasar Burundi sun kai farmaki kan wasu ofisoshin jami’an tsaro a Bujunbura babban birnin kasar Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto mai baiwa shugaban kasar Burundi shawara a bangaren yada labarai na cewa a yau juma’a wasu daga cikin ‘yan adawa sun kai farmaki kan wasu ofisoshin jami’an tsaro domin kubutar da firsinonin da ake tsare da su, saidai jami’an tsaron kasar sun mayar musu da martani mai tsanani, lamarin da ya sanya hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Page 1 of 208