An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:18

Shiri 40

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan falalar nuna so ga miskinai tare da tallafa masu da kuma kyautata masu, amma kafin nan bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai. ***************************Musuc********************************** Masu saurare hakika cikin ayoyi da dama na Alkur’ani mai tsarki Allah madaukakin sarki ya yi wasici ga bayinsa na su kyautatawa  miskinai,a cikin suratu Nisa’a Aya ta 36 Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma ku bauta wa Allah kada ku hana wani da shi kuma kula ga kyautatawa ma’aifa, da dangi, da marayu, da miskinai, na makoci na nesa, da abokin tafiya, da matafiyi, da abinda hannayanku suka mallaka (watau Bayi)hakika Allah bay a son wanda ya kasance mai takama mai yawan alfahari)  masu saurare kamar yadda wannan Aya mai albarka ta yi umarni ,kyautatawa miskinai ko kuma tallakawa da ma sauren gungun da ta yi ishara kan su na daga cikin misdakin tsarkaka daga girman kai da kuma jiji da kai da ganin fifiko ga  wani saboda dukiya, Arziki ko kuma milki da saurensu, daga cikin wasiyar da shugaban Hallitu Muhamad dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi wa mashhurin sahbin nan mai suna Abu Zaril Gaffari ya ce masa(ka so miskinai ko talakawa kuma ka yawaita zama da su), sheik saduk ya ruwaito hadisi daga Salman Muhamadi yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce (masoyina ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi mini wasici a abubuwa guda 7 kuma ba zan bar sub a, cikin ko wani hali, daga cikin ababen guda 7 a kwai son miskinai ko tallakawa kuma in kasance cikin kusanci da su) har ila yau shek saduk a cikin littafinsa mai suna man La Yahduruhu Fakih ya ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce :(duk wanda ya kirmama tallaka mumuni zai hadu da Allah madaukaki sarki  yana kuma Yardadde a gareshi).a cikin Littafin Tuhuful Ukul an ruwaito Hadisi daga Ma’aikin Allah ya ce (madalla ga wanda ya kaskantar da kansa saboda Allah, kuma yaji kan miskinai ko tallakawa, madalla ga wanda ya samu kudinsa ta hanyar Halal ba ta hanyar sabo ba daga cikin mumunai kuma ya ciyar da tallakawa da su). Masu saurare a bangare guda kuma wasu hadisan sun yi galgadi da jan kunne mai tsanani wajen kin kulawa da tallakawa, misali a cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih na Sheik Saduk an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce :( ku saurara , duk wanda ya ki kulawa da tallaka musulmi ko kuma ya yi masa rikon sakainar kashi, hakika ya yi wasa da kuma ko inkula da hakin Allah, kuma Allah ba zai kula shi ranar Alkiyama idan ba tuba yayi ba).har ila yau a wata riwayar Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Allah ya la’anci wanda ya wulakanta tallaka saboda Talaucinsa, duk wanda ya wulakanta tallaka saboda talaucinsa, za a kira sa a sama da makiyin Allah da kuma makiyin Annabawa, kuma ba za a karbi Addu’arsa ba, ba za a biya kuma bukatunsa ba). *************************Musuc********************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne a kan falala na  tausayin marayu da kuma kiyaye cutar da su tare da yin mu’amala da su cikin wani nau’I na tausayi ,yin hakan na daga cikin  dabi’u masu kirma daga dabi’un Allah madaukakin sarki kamar yadda ya bayyanawa Annabinsa mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka a cikin Suratu Duha Allah madaukakin sarki ya ce :(Ina rantsuwa da Hantsi*da Dare a lokacin da ya lulluba (da duhu)*Ubangijinka bai maka bankwana ba kuma bai ki k aba*kuma lalle ta karshe ce( wato Lahira)mafi alheri a gare ka daga ta farko (wato Duniya).* kuma lalle ne, Ubangijinka , zai yi ta ba ka kauta sai ka yarda*Ashe bai same ka ba maraya ba, sa’an nan  ya yi maka makoma?)suratu Duha daga Aya ta 1 zuwa 6 hakika Allah madaukakin sarki ya yi wasici da kirmama Maraya da kuma marayu , a cikin suratu Duha Aya ta 9 Allah madaukakin sarki ya ce:(saboda haka kada ka yi wa maraya tilas) har ila yau a cikin suratu Nisa’a Allah madaukakin sarki ya yi wasaici da a kyautata masu ,kamar yadda yayi galgadi gami da jan kunne na a kiyayi muzguna masu tare da mumunar mu’amala a tare su, Allah madaukakin sarki ya ce:(idan kuma makusanta da marayu da miskinai suka halarci gurin rabon (rabon gado)to ku arzuta su daga gareshi, kuma ku fada musu sananniyar magana ta Alheri*kuma wadanda su ke da,sun bar zuriya masu rauni a bayansu (watau Yara kanana) za su rika jiye masu tsoron (a cuce su) to su ji tsoron Allah (a kan dukiyar marayun da take hanunsu) kuma su fadi magana madaidaiciya*Hakika wadanda suke cin dukiyar marayu da Zalunci, to wuta ce kawai suke ci a cikin cikkunansu,kuma za su shiga cikin wata wutar mai tsanani). suratu  Nisa’I Aya ta 8 zuwa ta 10, a cikin suratu An’ami Aya ta 152 Allah madaukakin sarki ya ce:( kada kuma ku kasanci dukiyar maraya face wadda take ita ce mafi kyau har sai ya kawo karfinsa , kuma ku cika mudu da sikeli da adalci,ba mu dora wa rai sai abinda yake iyawa,to idan kuma kuka ba da shaida, to ku fadi gaskiya ko da kuwa a kan dan’uwa ne,alkawarin Allah kuma ku cika (shi), da wannan (Allah) ya yi muku wasiya don ku wa’azanta). Masu saurare, hakika Allah ya yi alkawarin babban sakamako ga masu kyakkyawar mu’amala gami da tausayi tare da Marayu, a cikin littafin Makarimul Akhlaq an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da aimincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, daga cikin wasiyoyin da ya yi wa Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(ya Ali duk wanda ya wadatar da Maraya wajen ciyar da shi da dukiyarsa har ya wadatu, Aljanna ta wajabta a gareshi, Ya Ali duk wanda ya shafi kan Maraya saboda tausayinsa, Allah madaukakin sarki zai bashi haske kan  ko wani kwara daya na cikin gashinsa a ranar Alkiyama).a cikin littafin Kurbul Isnad an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah na cewa:(duk wanda ya dauki nauyi Maraya ya kuma dauki nauyin ciyar da shi zan kasance tare da shi a cikin aljanna kamar haka, sai ma’aikin Allah ya nuna yatsarsa manuniya da kuma ta tsakiya wacce suke tare)  har ila yau a cikin khudubar ma’aikin Allah na tunkarar watan Ramadana ya ce :(duk wanda ya kirmama maraya a cikin watan Ramadana Allah zai kirmama shi a ranar da zai hadu da Allah madaukakin sarki ), har ila yau a cikin Littafin  kafi, Amiri mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce (ku tarbiyatar da Maraya da abinda kuka tarbiyatar da ‘ya’yanku), da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon aiki da wadannan wasiyu masu Albarka *******************Musuc****************************** Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.  
More in this category: « Shiri Na 39 Shiri Na 41 »

Add comment


Security code
Refresh