An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:17

Shiri Na 39

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan kyakkyawar mu’amala da wanda aka ke bi bashi yayin da yake cikin tsanani na babu  ta yadda ba zai iya biyan bashin ba, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda a kayi tanadi a kan faifai. ********************************Musuc***************************** Masu saurare, hakika Allah madaukakin sarki ya wajabtawa bayinsa mumunai da su jinkirtawa wadanda suke bi bashi yayin da ba su da halin biya, a cikin suratu Bakara Aya ta 280 Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan (wanda ake bin bashin) ya kasance cikin mawuyacin hali to sai a saurara masa har zuwa lokaci da ya wadata ko kuma ya samu, idan kuka bar masu a matsayin sadaka alheri ne a gareku idan kun kasance kun sani) a cikin littafin Majma’ul bayyani an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa aka tambayi Imam Sadik (a.s) kan wanda ake bi bashi da ya kamata a jinkirta masa har ya wadata, sai Imam (a.s) ya ce :(shine  abinda yake samu baya isarsa ya ciyar da kansa kuma ya ciyar da iyalansa).wannan a bangaren yi masu jinkiri har zuwa lokacin da Allah madaukakin sarki ya hore masu, wanda ya fi kuma shine kiran da Allah madaukakin sarki yayi mana na cewa a yefe masu bashin kwata kwata kamar  yadda ya  zo a karshen wannan Aya:( idan kuka bar masu a matsayin sadaka alheri ne a gareku idan kun kasance kun sani). Masu saurare hakika  hadisai da dama sun kwadaitar da mu falalar sassauti ga wanda ake binsa bashi yayin da ba shi da halin biya tare kuma da taimaka masa, a cikin littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Imam Sadik(a.s) ya ce: (wata rana Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalansa tsarkaka ya hau minbarinsa bayan ya godewa mahalicinsa ya kuma yi wa Annabawa (A.S) salati sai yace: Ya Ku Mutane wanda yake nan ya isar da wannan sako ga wanda baya nan (ma’ana wanda bai halarci wannan guri ba) ku saurara duk wanda ya jinkirawa wanda yake bi bashi yayin da yake cikin tsanani na biya  , Allah madaukakin sarki zai bashi lada ko wata rana har lokacin da Allah ya horewa  wanda yake bi bashin ya kuma biyashi)sannan Imam Sadik (a.s) ya karanto Ayar da ta gabata mai albbarka wacce ta cikin suratu Bakara sannan yayi ta’aliki yana mai cewa  idan kusan cewa wanda ake bi bashi yana cikin tsanani ba ya iya biya, ku biya masa daga cikin   dukiyarku hakan shine alheri a gareku). A cikin Tafsiri Ayashi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda yake son Allah ya sanya shi a cikin inuwar Al’arshinsa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa, to yayi sasauci ga wanda yake cikin tsanani idan yana binsa bashi   ya kuma  yafe masa daga cikin dukiyar da yake binsa), a cikin Tafsiru Burhan an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) ya ce :(duk wanda yake son Allah ya karesa daga wutar Jahanama   to yayi sasauci ga wanda yake cikin tsanani idan yana binsa bashi kuma ya yafi masa daga cikin dukiyar da yake binsa). Imam Sadik (a.s) na cewa:(hakika Allah madaukakin sarki yana son wadanda suke yin  sassauci ga wadanda suke bi bashi a yayin da suka shiga cikin tsakani).ma’ana ba sa matsa masu a kan cewa lallai lallai sun sun biya su , sukan kyale su har  sai lokacin da Allah ya wadata su sannan sub a su). A cikin littafin sawabul A’amal na shek Saduk (k.s) an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) ya ce :(ranar Alkiyama Allah zai tayar da wasu Mutane kalkashin Al’arshin ubangiji, fuskokinsu suna   haske, suturansu daga haske, kuraren zamansu zuna haske, sai hallitu su tambaya shin wadancan Annabawa ne? sai wani mai kira daga kalkashin Al’ashi ya ce a’a wadancan ba annabawa ba ne,sai hallitun su ci gaba da tambaya Shahidai ne, sai ace masu a’a ba shahidai ba ne sai wadancan da kuke gani Mutanan da suka kasance a duniya suna saukakawa mumunaine  kuma suna yi sassauci ga wadanda suke bi bashi a yayin da suke cikin tsanani ba sa tambayarsu har sai lokacin da Allah ya wadatar da su suka biya su  da kansu). ***************************Musuc********************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan mahimanci kula da kuma himma wajen biyan bashi.a cikin littafin safinatul Bihar an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa :(kokarin da kulawa wajen biyan bashi na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci) .an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce (ku rage daukan bashi dake kawunanku domin rage daukan bashi yana kara yawan kwanuka, saboda shi cin bashi yana yana sanya karaya a zukatan masu cin bashin kuma karayar zuciya na sanya damuwa gami da karamcin kwanuka).hakika masu saurare kin biyan bashi a yayin da mutune ke da halin biya na daga cikin misdakin cin amana da sata ko da kuma ba shin na wadanda ba mumunai ba ne kai ko da na firkar Marji’a ne wacce bani umaiyya suka kirkirota , an ruwaito hadisi daga Abi Samama ya ce na shiga wajen babban Ja’afar Imam Bakir (a.s) sai nace masa  na sanya fansar raina a gareka ina son zuwa Makka domin in sauke farari , sai dai a kwai bashi a kaina na mabiyin birkar Marji’a mi za ku ce dangane da hakan, sai Imam (a.s) ya ce ma saka koma ka biya bashinka, ka yi jiran saduwa da Allah madaukakin sarki babu bashi a kanka, hakika mumuni bay a cin amana). Imam Sadik (a.s) ya ce : (barayi kala uku ne daga cikinsu wanda ya dauki bashi kuma bashi da niyar biya).a wata riwayar kuma Imam (a.s) na cewa:(duk wanda ya rufe dan uwansa mumuni saboda yana binsa bashi kuma ya san ba shi da halin biya, wallahi ba zai dandana abincin Aljanna ba, kuma ba zai sha daga cikin kogin Rahikul Makhtum ba).har ila yau a cikin littafin Safinatul Bihar shahararen malamin tafsiri da hadisi shek Kummi (yardar Allah ta tabbata a gareshi)ya ce an  ruwaito hadisi daga Mu’awiya bn wahab ya ce: na cewa Imam Sadik (a.s) mun samu labarin cewa wani mutune daga cikin Ansar ya mutu da bashi a kansa sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ki ya yi masa Salla, sannan ya ce kadda ku yiwa dan uwanku salla har sai an biya bashin dake kansa, Imam Sadik (a.s) ya ce hakika wannan labari gaskiya ne domin Ma’aikin Allah ya yi haka ne don Mutane su yi yarjejjeniya ta gaskiya da wadanda suke bin dan uwansu bashi, kuma wadanda ake bi bashi su gaggauta biyan bashin dake kansu sannan kuma su fasa sako sako wajen biyan bashin). A karshe  bari mu karanto wani hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) inda yake cewa:(ko wani zunubi a kan karkare ne ga wanda ya rasa ransa ta hanyar Allah amma banda bashi, domin shi bashi sai an biyashi ko kuma wanda yake bi bashin ya yafe) *****************************Musuc******************************** Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.  
More in this category: « Shiri Na 38 Shiri 40 »

Add comment


Security code
Refresh