An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:16

Shiri Na 38

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan karin ni’ima da kyautatawa ga wanda yake godiya, kafin mu shiga shirin ga wannan *******************Musuc*********************** Masu saurare godiya ga hallitun Allah madaukakin sarki na daga cikin kyawawen dabi’u kuma duk wanda yake godewa wanda ya kautata masa kamar ya godewa ubangijinsa ne kuma yayi aiki da hadisin Ma’aikin Allah tsira da amnicin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ne wanda yake cewa (ku dabi’antu da dabi’un Allah) Hakika daga cikin siffofin Allah shi mai godiwa da kuma gafara ne kuma yayiwa alkawarin karin ni’ima ga masu gode masa, a cikin suratu Ibrahimu Aya ta 7 Allah madaukakin sarki na cewa :(lallai idan kuka  gode wa Ni’imata ba shakka zan kara muku).a cikin littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake yiwa daya daga cikin ‘ya’yansa  nasiha yana mai cewa (ya kai Dana ka godewa wanda ya ni’imtar da ku, ka taimakawa wanda ya gode maka domin ni’ima ba za ta taba gushe maka mutukar kana godiya, kuma ba zama a tare da kai ba matukar ka kafircewa wanda ya baka ni’imar ba,mai godiya da gidarsa za a kara masa ni’imar da ta wajabta a gode masa sannan sai ya karanto wannan aya mai albarka (lallai idan kuka  gode wa Ni’imata ba shakka zan kara muku, idan kuwa kuka butulce, hakika azabata mai tsanani ce). Suratu Ibrahimu Aya ta 7, a cikin littafin kafi na sikatu islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Masma’a bn Abdulmalik ya ce mun kasance a zaune wajen shugabanmu Imam Sadik (a.s) a Mina a gabanmu a kwai Inabi muna ci ,sai wani Alamajiri  ya zo yayi bara,Imam (a.s) ya yi umarni da a dauki wani reshe daga cikin inabin da muke ci  a bashi, sai wannan almajiri ya ce shi ba ya bukatar Inabi, idan dai a kwai Dirhami ma’ana kudi a bashi, wato abinda ya bukata kudi , shi bay a bukatar  abinci,sai Imam (a.s) ya ce Allah ya buda maka sai wannan almajiri ya ta fi bayan ya dan wani lokaci ,sai ya dawo ya ce a bashi wannan inabi da aka bashi yaki karba a baya, Imam (a.s) ya ce Allah ya wassa’a maka bai ba shi ba, bayan dan wani lokaci sai ga wani Almajirin na daban ya zo yayi bara sai Imam (a.s) ya dauki Inabi kwara uku ya bashi, sai wannan almajiri ya karba da hanu biyu sannan ya ce na godewa Allah madaukakin sarki da ya arzitani da wannan, sai Imam (a.s) ya tsaida shi sannan ya cika masa hanunsa da Inabi,sai almajirin ya ci gaba da cewa godiya ga Allah madaukaki da ya kara arzuta ni da wannan.sai Imam (a.s) ya sake tsayar da shi, sannan ya tambayi yaronsa shin a kwai wasu Dirhami wato kudi na wancan lokaci   a gurinka? Sai ya ce masa a kwai Dirhami 20 , Imam (a.s) ya amsa ya baiwa wannan almajiri, almajirin ya kara da cewa  godiya ta tabbata ga Allah wannan daga wajenka ,kai kadai ne mai ikon yin haka ba kada abokin tarayya, sai Imam (a.s) ya sake tsayar da shi sannan ya cire wata riga a jikginsa ya meka masa , sai wannan almajiri ya ce na godewa Allah madaukakin sarki da ya suturtar da ni da wannan, a wata rawayar kuwa ya ce wa Imam (a.s)Allah ya saka maka da alheri).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon dabi’antuwa da irin wadannan kyawawen dabi’un musulinci. ********************Musuc**************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan kaskantar da kai ga mai aikata alheri ko kuma rashin girmar kai ga wadanda suke bayarwa a gaban mabukata  ,a cikin suratu Mudasir Aya ta 6 Allah madaukakin sarki ya ce :(kada ka ba da abu don ka nemi mafi yawa daga gareshi) An ruwaito hadisi a cikin littafin Kafi daga shugabanmu Imam Bakir(a.s) yayin da yake fassara wannan Aya ya ce:(kada ka bukaci mafi yawa kan alherin da ka aikata saboda Allah), a cikin littafin Nahjul balaga an ruwaito hadisi daga Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce ku kiyayi neman lada mai yawa saboda aiyukan da ku ka yi mutane ko kuma ku kanbama aiyuka da kuka yi Mutane ko kuma kin cika alkawarukan da kuka yiwa Mutane domin hakan ya na bata aiyukan da ku ka yi masu kyau kuma yana tafiya da hasken gaskiya). Masu saurare Alkur’ani mai girma ya hana bankama aiyuka da Bawa da aikata don neman mai yawa kan abinda ka bayar ko kuma ka aikata,hadisai da dama sun umarce mu da aiyukan alheri gami da kyautatawa kuma mu kallesu a matsayin wani dan aiki kadan, hakika Allah madaukakin sarki cikin tausayinsa ya sanya hakan a matsayin wani shi’ari ko alama ga wadanda aka kyautatawa daidai golgwadon matsayinsu da aiyukansu a wajensa.a cikin littafin Kafi na sikatu Islam kulaini an ruwaito Hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(shin b aka ganin cewa kyautatawa ba ta gyaruwa sai da abubuwa guda uku: kaskantar da ita, boyeta da kuma gaggautata,domin idan ka kaskantar da ita za ta, ka girmamata a wajen wand aka kyautata ma, kuma idan ka boye ta to ba shakka ka cika ta,ma’ana ka aikatata yadda ake bukata ka zo da ita idan kuma ga gaggauta aikatata to ka amintu daga waswasin shaidani kuma yak an sanya mabukaci yayi farin ciki ga kyautatawar). Masu saurare kamar yadda aka saurara a wannan hadisi kaskantar da kai ga mai taimako a gaban mabukaci na daga cikin cikar kyautatawa, haka zalika ma bayar da taimakon cikin sirri,hadisai da dama sun yi bayyani a kan cewa bayan da sadaka cikin sirri ka kiyaye mutuncin mabukacin da karamarsa kuma hakan na kawar da kirmar kai gami da jiji da kai ga mai bayarwa.kamar yadda bayar da sadakar cikin gaggawa kan sanyar farin ciki a cikin zukatan mabukan da wadanda suka taibaya kuma Allah madaukakin sarki yak an daga hajjarsa da wannan,abin al’ajabi da kuma Lutufinsa, Allah madaukakin sarki ya kaddarawa masu kyautata bin wadannan hanyoyin guda uku wajen bayan da taimako ko kuma sadaka domin yin hakan shi ze kirmama ladansu kuma ya bayyana mutuncinsu da karamcinsu a idanun mutane.a cikin Littafin Nahjul Balaga an ruwaito hadisi daga Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa:(biyan bukatu ba su tabbatuwa sai da ababe guda uku,da gaskantar da ita domin a girmamata, da boyeta domin a bayyana ta,da gaggautata domin ayi fara’a da ita).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon koyi da wadannan kyawawen dabi’u. *****************************Musuc************************** Masu saurare, ganin lokaci na hararenmu a nan zamu dakata, sai kuma a maku na gaba da yardar Allah madaukakin sarki za a jimu dauke da wani shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri,wassalama aleikum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.  
More in this category: « Shiri Na 37 Shiri Na 39 »

Add comment


Security code
Refresh