An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:15

Shiri Na 37

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne  a kan godiya ga ni’imar Allah madaukakin sarki, amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai ********************Musuc*************************** Masu saurare, godewa N’imar Allah madaukakin sarki na daga cikin kyawawen dabi’u na addinin musulinci ya yi umarni da shi kuma Allah madaukakin sarki ya yi alkawarin kari ga duk wanda ya gode masa a kan ni’imar da ya basa, a cikin suratu Ibarhim Aya ta 7 Allah madauakin sarki na cewa:(kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar cewa: Lallai idan kuka gode wa (Ni’imata )ba shakka zan kara muku, idan kuwa kuka butulce, to hakika azabata mai tsanani ce.) Daga cikin misdakin godewa Allah madaukakin sarki godiya ga wanda Allah ya sanya daga hanunsa ni’imar Allah ta isa zuwa ga bawansa, a cikin littafin Kafi na sikatu Islam kulaini an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sajjad (a.s) na cewa :(hakika Allah madaukakin sarki ya na son zuciya mai nadama, kuma ya na son bawa mai godiya,a ranar Kiyama Allah madaukakin sarki  zai cewa wani bawa daga cikin bayinsa shin ka godewa wane? Sai wannan Bawa ya ce A’a sai dai godiyata a gareka ne kawai ya Ubangiji, sai Allah ya ce ba ka gode mani ba, matukar dai ba ka gode masa ba, sai Imam (a.s) godiyar ku ga Allah ita ce godewa mutanan da suka yi maku alheri) Masu saurare daga cikin falalar godiya ga ma’abota alheri shine karfafa su wajen ci gaba da yin alherin da suke yi  kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yi ishara da hakan a cikin wani hadisin da aka ruwaito cikin littafin Kafi inda Imam (a.s) ke cewa:(Allah ya la’anci wanda yake yanke hanyar alheri, sai aka tambayeshi su wane masu yanke hanyar alheri?mutuman da aka yi masa alheri ya kafirce ma’ana yarena alherin da aka yi masa ya ki godewa kuma hakan ya sanya wanda ya yi alheri ya yi sanhi ya ka sa yiwa waninsa alherin). A cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda aka kautata masa ya yi kokori wajen sakawa wanda ya yi masa da ma fi kyau, idan kuma ya kasa ya gode masa,duk wanda ya ki yayi wannan to ya kafircewa ni’imar Allah).har ila yau a cikin littafin Kafi Ma’aikin Allah (S.W.S) ya ce (Allah madaukakin sarki bai budewa Bawa kofar godiya ba sai da ya tanadar  masa hanyar  kari). A cikin littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Allah madaukakin sarki yana cewa:(hakika na daukawa kaina alkawarin ba zan karbi godiyar bawa ba a kan ni’imar da na yi masa har sai ya godewa wanda ta hanyar sa ce wannan ni’ima ta isa gareshi daga cikin bayina) *********************Musuc***************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da riwayar shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik(a.s) wacce aka ruwaito a cikin littafin Tahzibul Ahklaq inda Imam (a.s) ke cewa:(hakika Allah madaukakin sarki ya yi wa wasu Mutane daga cikin Bayinsa Ni’ima sai suka ki su gode masa, sai wannan ni’ima ta kasance bala’I a garesu, kuma wasu Mutane daga cikin bayinsa ya jarabce su da wahalhalu kala-kala sai suka yi hakuri bisa wannan Musaba ,daga karshe hakurinsu bisa wannan musiba ta kasance  Ni’ima a garesu).masu saurare hakika godiyar ni’imar Allah madaukakin sarki ga dukkanin ma’anarta sanadiyar isa ne zuwa ga samun albarkatun ni’imar kamar yadda raina ni’ima ko kuma kin godiya ga ni’imar Allah ya kan zamanto sanadin ukubar duniya tun kafin aje Lahirar ma,a cikin littafin Amaly na shek tusy an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah (s.a.w) na cewa:(zunubai kala uku a kan gaggauta ukubar su a nan duniya tun kafin aje lahira, na farko sabawa iyaye, na biyu zalunci da kuma cutar da Mutane, sai kuma na ukun su butulcewa ihsani ko kuma kautatawa) Har ila yau a cikin littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga Imam Aliyu bn Husain Zainul abidin (a.s) yayin da yake wasaici ga dansa yana mai cewa:(ya kai dana ga godewa wanda ya kautata maku, ka kautatawa wanda ya gode maka,har abada  ni’ima ba za ta kushewa ba wanda yake godiya ga wanda ya kautata masa, kuma ni’ima ba za ta dore ba ga wanda ba ya godiya ko kuma ya kafircewa wanda ya kautata masa, mai godiya da godiyarsa Allah madaukakin sarki zai kara masa daukaka da kuma ni’imar da ta wajabci godiya sannan ya karanto wannan Aya mai albarka   :(kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar cewa: Lallai idan kuka gode wa (Ni’imata )ba shakka zan kara muku, idan kuwa kuka butulce, to hakika azabata mai tsanani ce.) suratu Ibrahim Aya ta 7. Da fatan Allah madaukakin sarki ya arzitamu da wannan dabi’a kyakkyawa mu zamanto masu godiyar Allah madaukakin sarki ga dukkanin ni’imar da ya hore mana ta hanyar godewa bayinsa da ya sanya ta hanyarsu ne Allah ya arzita da ni’imarsa . **************************Musuc*************************** Masu saurare a nan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Injeniyarmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya ni ke muku fatan alheri wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.
More in this category: « Shiri Na 36 Shiri Na 38 »

Add comment


Security code
Refresh