An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:13

Shiri Na 36

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan kyautatawa wanda ya kyautata, ma’ana sakawa wanda ya kyautata maka da mafi kyakkyawan sakamako,amma kafin mu shiga shirin ga wannan. ************************Musuc************************** Masu saurare shirin na yau zai fara da Aya ta 60 cikin suratu Rahaman inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Ba Wani abu ne sakamakon kyakkyawa ba sai kyakkyawa), an ruwaito hadisi daga Hafiz Aljalil Husain bn Sa’ed cikin littafin Azuhud, ya ce an tambayi Imam Sadik (a.s) kan fadar Allah madaukakin sarki  (Ba Wani abu ne sakamakon kyakkyawa ba sai kyakkyawa) sai Imam (a.s) ya ce wannan Aya a kan iya zartar da ita kan mumuni da kafiri,mutuman kirki da fajiri, duk wanda ya yi abin kirki ko kuma kyakkyawan abu to shima a saka masa da kyakkyawa, sakamaka da kyakkyawa ba shi ba  ne a yi masa makamanci abin ya aikata  a’a, sai a diba abinda ya fi a sakama masa da shi).masu saurare wannan hadisi shaida ne bisa kyakkyawan sakamako ga wanda ya kyautata, mumuni ne ko kafiri, mutuman kirki ne ko fajiri ne ,kuma sakamakon ya kasance ya fi wanda yayi da farko, to amma ta yaya mutuman da ba shi, zai iya sakawa wanda ya kyautata masa?amsar wannan tambaya ita ce riwayar da aka ruwaito a cikin Littafin Zuhud daga shugaban halittu Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda ya ce:(duk wanda ya tambayeku saboda Allah ku bashi,kuma duk wanda ya kyautata maku  to ku saka masa da kyakkyawa, idan kuma ba ku da abinda za ku saka masa to ku roka masa Allah madaukakin sarki har sai kun ji cewa kun saka masa da mafi kyakkyawan alherin da ya yi maku).amsar wannan tambaya kamar yadda wannan hadisi ya yi ishaka shine yawaita addu’ar alheri ga wanda ya kyautata maka shine sakamakon mafi alheri ga wanda ya kyautata maka matukar dai ba ka da abinda zaka iya saka masa da shi ,a wata riwayar kuwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa daga cikin hanyoyin sakawa wanda ya kyautata maka shine gode masa da kuma ambatonsa da alheri, kamar yadda aka ruwaito cikin littafin Azuhud daga Husaini bn Sa’ed ya ce ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (ya isar maka yi wa dan uwanka addu’a da kuma ambatonsa da  alheri idan ya yi maka alherin, kamar ka ce Allah ya saka masa da alheri, idan kuma an ambace a guri baya nan sai ka ce Allah ya sakama da alheri, idan ka aikata haka, ya isar maka a matsayin kyakkyawan sakamako bisa alherin da ya yi maka).a cikin Littafin Amaly na shek tusy an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa:(hakin wanda ya kyautatawa mumuni ya saka masa da mafi alheri,to idan ya kasa da haka, wajibi ya kyautata masa ta hanyar ambato irin ni’ima da kuma soyayyar da ya gwada masa, idan ya kuma kasa da hakan to lallai shi ba irin mutanan da ya  kamata a kyautata masa ba ne).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon godiya ga wanda ya kyautata mana musaman ma ga shugaban ni’ima da kyauta, shugaban halittu baki daya. ****************************Musuc******************* Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai yi bayyani ne kan yin mu’amalar da ta dace ga hallitun Allah madaukakin sarki.a cikin littafin Musadikatul Ikhwan na shek Saduk(k,s) an  ruwaito hadisi daga imam sadik (a.s) na cewa:(ka dubi abinda ka samu daga cikin dukiyar ka sai ka bayar da shi ga ‘yan uwanka domin Allah madaukakin sarki na cewa(hakika kyakkyawa ya na kore mumuna)sannan ya ci gaba da cewa ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce abu uku ba za ya jure wa wannan al’umma ba, na farko mu’amala ta hanya da ya da ce cikin  dukiyar su, yi wa kansu adalci wajen mu’amala da mutane, sai kuma ambaton Allah madaukakin sarki cikin ko wani hali, ba ambaton Allah ba kawai a harshe,duk lokacin da wani abu na sabon Allah ya tunkaresu su kauce masa su ce mu muna tsoron Allah ubangijin talikai).masu saurare mu’amala da mutnae ta hanyar da ya dace na daga cikin kyawawen aiyukan da suke kawar da munana kuma na daga cikin hanyar tsarkaka daga aiyuka munana, kamar yadda yake daga cikin alamomin gasganta Imani, a cikin littafin khisal an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa(duk wanda yayi mu’amalar da ta dace da wanda baya da shi, ma’ana duk wanda ya taimakawa fakiri daga cikin dukiyarsa kuma ya daidata mutane da kansa wannan shine hakikanin mumuni).har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) na cewa:(amiru mumunin (a.s) ya kasance ya na cewa mu iyalan gidan Ma’aikin Allah (s.a.w) an umarce mu da mu ciyar da abinci, mu tabbatar da wakilci a cikin mutane, mu kuma yi sallah yayin da mutane ya kwana).har ila yau a cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga imam sadik (a.s)na cewa:(hakki ne ga musulmi su yi kokari wajen taimakawa masu rauni daga cikinsu, su yi kyakkyawar mu’amala da kuma taimako, su taimakawa mabukata kuma su tausaya masu, sai su kasance bisa umarnin Allah madaukakin sarki na cewa, masu tausayi a tsakaninsu) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon taimako da kuma kyakkyawar mu’amala tare da bayin Allah baki daya. *******************************Musuc*********************** Masu saurare,a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injeniyamu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar ni ke muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatu llahi wa barkatuhu.    
More in this category: « Shiri Na 35 Shiri Na 37 »

Add comment


Security code
Refresh