An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:12

Shiri Na 35

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan soyyaya da juna a tsakanin Mutane  , amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. ***************************Musuc************************* Masu saurare, daga cikin kyawawen dabi’un musulinci da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa,shine sun nunuwa junana soyayya da kauna wanda hakan shi ke nuna falala, karamci, rahama da kuma son gafara a garesu, hakika hadisai da dama sun yi bayin Allah  wasaicin da nunawa juna soyayya a tsakaninsu, kamar yadda aka ruwaito a cikin Littafin Kafi daga shugabanmu Babban Ja’afar Imam Bakir (a.s) ya ce:(hakika wani balaraban kauye daga kabilar Bani Tamim ya je wajen ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce masa Ya Ma’aikin Allah yi mini galgadi, daga cikin irin galgadin da ya yi masa ya ce mas aka so Mutane sai su ma Mutanan zai su so ka). Masu saurare wanzuwar soyayya a tsakanin Mutane wata ibada ce da mumuni yake dabi’antuwa da ita domin samun kusanci zuwa ga Allah madaukakin sarki,kamar yadda ta ke hanya ce ta samun soyayya a tsakanin halittu, kuma wannan shi ke kare su da cutuwa domin haka ne wani hadisi ke bayyani sa a matsayin rabin hankali,Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(wanzuwar soyayya da kuma goda soyayya ga mutane rabin hankali ne).a cikin Littafin kafi na sikkatu islam kulaini an ruwaito  hadisi daga Imam Kazim (a.s) ya ce (bayanna soyayya ga Mutane rabin hankali ne, tausayi kwa rabin rayuwa ce).har ila yau a cikin wata riyawa kwa Imam Hasan Mujtaba (a.s):(kusanci shine kusancin soyayya ko da kwa dan uwantaka na tsakaninku ya nada nisa, nisanci shine wanda ya nisanta daga soyayya ko da a kwa dan uwantaka dake tsakaninku ta kusa ce sosai).kamar yadda Ma’aikin Allah (S.A.W) ya shiryar da mu yadda Mutane ya kamata su bayyana Soyayya tsakaninsu a aikace, a cikin riwayar da Imam Sadik (a.s) ya ruwaito a cikin Littafin Kafi ya ce Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ababe uku ne ke kwada soyayyar musulmi a kan dan uwansa musulmi, na farko, ya tarbe shi da milmishi, ya giramashi wajen wanzar  masa da guri a yayin da suka zauna tare, sai kuma na uku ya kira shi da sunan da fi so).har ila yau a cikin wata riwayar Imam Sadik (a.s)ya ce:(idan kana son dan uwanka to ka sanar da shi, domin Annabi Ibrahim (a.s)ya ce:(Ya tuna lokacin da Ibrahimu ya ce:Ya Ubangijina ka nuna mini yadda kake raya matattu, (sai Allah) Ya ce :shin ko ba ka ba da gaskiya ba ne? sai Ya ce A’a bah aka ba ne,don dai raina ya kwanta kawai..)sai Imam (a.s) ya ce idan kana son Mutune to bayyana masa soyayyarka domin hakan shi zai tabbatar da soyayyar dake tsakaninku).masu saurare,Kyautatawa,alheri,kyakkyawar mu’amala , kaucewa cutarwa, giramamawa,Afuwa ga kurakure da makamantansu na daga cikin misdakin bayyana Mutune irin son da ake yi masa kamar yadda wadannan riwayoyi da ma makamantansu suka bayyana mana. ***********************Musuc********************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai yi bayyani ne dangane da kyawawen wasani gami da zolaya a tsakanin Al’umma,a cikin littafin Yunus Shaibani an ruwaito hadisi daga Imam Ja’afaru Sadik(a.s) na cewa:(shin ba ku zolayar junanku ne, hakika zolaya na daga cikin kyawawen dabi’u, domin za ka sanya farinciki a zuciyar dan uwanka, kuma hakika Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yak an zolayi mutune idan ya na so ya sanya shi  dariya). Imam Bakir (a.s) ya ce:(hakika Allah madaukakin sarki ya na son mai baiwa al’ummar dariya ba tare da aibata wani ba). A cikin littafin Kafi sikatu Islam kulaini ya ruwaito hadisi daga Mu’amar bn Khalad ya ce (na tambayi Babban Hasan (a.s) dangane da mutumane da yake yin abuban ban dariya cikin al’umma tare da zolaya wanda hakan yak an sanya su dariya sai Imam (a.s) ya ce babu laifi matukar babu alfasha ko kuma aibanta wani ba domin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan balaraban kauye ya kawo masa kauta, sai ya ce masa to ya bashi biyan kautar da ya kawo masa sai ya yi dariya, idan an sha kwanaki sai ma’aikin Allah ya tuna da abinda wannan balaraben kauyen ya ce sai ya ce ina ma balaraben kauyen nan ya zo mana).masu saurare, zolaya ko kuma wasan da babu cin tsarfi, fallasa ku kuma aibata juna shine wasan da musulinci ya amince da shi.an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:(babu wani mumuni da ba ya wasa da dan uwansa). Har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Kazim (a.s)na cewa :(Annabawan Allah madaukakin sarki da wasiyansu sun kasance suna wassani tare da baiwa juna dariya da sahabansu).bayan haka masu saurare wani irin wassani ko zolaye ne addinin musulinci ya hana ? sai a tarbemu a maku na naga domin jin irin hadisin za mu karanto mu ku dangane da wannan maudu’i.   **********************Musuc************************* Masu saurare, a nan za mu dasa aya ganin lakacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka tallafawa shiri, musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu
More in this category: « Shiri Na 34 Shiri Na 36 »

Add comment


Security code
Refresh