An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:11

Shiri Na 33

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirin da ya gabata munyi bayyani kan mahimancin kyakyawar abotaka da mu’amala tare da Mutane, a shirin na yau kwa za mu yi bayyani ne kan falalar amincewa ko kuma karbar Nasihar dan uwa musulmi ko mumuni, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan. ***********************Musuc**************************** Masu saurare hakika kur’ani mai tsarki ya umarce mu da yin Nasiha da kuma karbarta daga wajen mutanan da suka dace, ayoyi da dama sun shiryer da mu bisa wannan kyakkyawar dabi’a, za mu takaitu da Aya guda wacce take bayyana mumunan sakamako ga wadanda suka kauracewa karbar Nasiha, a cikin suratu Bakara Aya ta 206 Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan kuwa aka ce da shi ka ji tsoron Allah sai girman kai ya hau kansa saboda sabon (da aka hana shi yi)to jahannama ta ishe shi makwanta,kai lallai makwantar kuwa ta munana). Hakika masu saurare babban abinda yake janyo kin karbar Nasiha shine girman kai, bautar zuciya da kuma son rai, duk wanda ya kasance ya dabi’anto da sauraren nasiha ba shakka zai rubanto da wata falala ta daban, falalar kuwa ita ce tsarkakar zuciya daga girman kai da kuma rage aikata sabo ,da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon sauraren nasiha daga wajen mutanan da suka dace.hadisai da dama sun kwadaitar da mu wajen saurare da kuma karbar Nasiha kuma sun bayyana cewa wannan kyakkyawar dabi’a na daga cikin ni’imar da Allah madaukakin sarki ya horewa bayinsa salihai, hakika  a cikin littafin Assara’ir na Allama bn Idris Alhilly an ruwaito hadisi daga Ayub bn Nuh ya ce  hakika Imam Ali Alhadi (a.s) ya rubuta wasika zuwa daya daga cikin mabiyansa yana mai cewa:(ka tunatar da wani, duk wanda Allah madaukakin sarki ya nufe sa da Alheri sai ya bashi damar saurare da kuma karbar Nasihar ‘yan uwansa mumunai ko musulmai).a cikin litattafan Kafi , Almahasin da kuma Attahzib  an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce (ka bi mutuman dake sanya ka kuka a yayin da yake yi maka Nasiha, kadda kabi mutuman dake sanya ka dariya a yayin da yake yaurarka, kuma baki dayanku za ku koma zuwa ga Allah madaukakin sarki sannan ya sanar da ku abinda kuka kasance kuna aikatawa). ******************Musuc********************************* Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Nasihar shugabanmu Imam Aliyu bn Husain Zainul Abidin (a.s), a cikin littafin Amaly na sheik Tusy (K,S) an ruwaito hadisi daga shugabanmu Zainu Abidin (a.s) yayin da ya ke yiwa dan Dansa Nasiha yana mai cewa:(Ya Kai Dana ka kiyayi abotaka da wawa,domin Shi Wawa, idan ya aikata wani abu zai bata shi, ba ya wani aiki na kashin kansa wanda zai wadatar da shi, kuma ilimin waninsa ba ya amfanar da shi,sannan ba ya biyayya ga mai yi masa Nasiha). Masu saurare shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana cewa karbar Nasiha na daga cikin dabi'un da mumuni ba ya wadatuwa da shi matukar ya na bukatar kyakkyawar rayuwa, a cikin littafin Almahasin na sheik Ahmad Barki an ruwaito hadisi dag Imam Sadik(a.s) na cewa:(hakika mumuni ba ya wadatuwa daga wadannan ababe guda uku, na farko,taufiki ko kuma dace daga Allah  madaukakin sarki, na biyu ya kasance mai yiwa kansa Nasiha, na uku kuma amincewa ko kuma karbar Nasiha daga wanda yayi masa Nasiha). Har ila yau shugaban Imam Sadik(a.s) ya bayyana karamar Nasihar ga dan uwa, a cikin littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa: ( wanda na fi so daga cikin 'yan uwa ne shine wanda ya yi mini kyauta da bayyana mini aibi na ko kuma ababen da nuke yi marassa kyau ) a wani hadisin kuwa ya na cewa wanda ya tuna tar da ni bisa wata barna da ya ga zan aikata ko kuma na aikata domin in gyra). A wani bangare kuwa Alkur'ani mai tsarki na umartar mu da muka sance masu yi umarni da alheri  kuma masu hani da abun ki, a cikin Suratu Ali Imran Aya ta 104, Allah madaukakin sarki ya ce:(Lallai ne wata Al'umma ta kasance daga cikinku (wadanda)za su rika kira zuwa ga alheri, kuma su rika umarni da aikata abin kirki, su rika kuma hani ga mumunan aiki.wadancan kuwa sune masu samun babban rabo) A wani bangare kuwa Alkur'anin ya umarce da kadda mu manta kawunanmu wajen aikata alheri kadda mu zamanto masu yin Nasiha sannan mu kuma muna aikata sabanin hakan, a cikin Suratu bakara Aya ta 44 Allah madaukakin sarki ya ce:(Yanzu kwa rika umartar Mutane da kyakkyawan aiyuka kuna kuma mantawa da kanku, alhali kuwa ku kuna karanta littafin (Attaura)? Yanzu ba za ku hankalta ba?). **********************Musuc************************* Masu saurare, a nan za mu dasa aya ganin lakacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka tallafawa shiri, musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.       
More in this category: « Shiri Na 32 Shiri Na 34 »

Add comment


Security code
Refresh