An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:10

Shiri Na 32

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan kyakyawar abotaka da mu’amala tare da Mutane , amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. ******************Musuc********************************* masu saurare hakika ayoyi da daman a cikin Alkur’ani mai tsarki su yi  umarni da kyakyawar mu’amala da bangarori na Mutane daban-daban makusanta ne ko kuma  wadanda babu alakar jini a tsakaninmu da su, kamar yadda aka umarce mu da yin biyayya ga ma’aifa da kuma kyakkyawar mu’amala da iyalanmu. Hadisai da dama sun umarcemu da riko da kyawawen dabi’u wadanda suke gina kyakyawar alaka ta yau da kulun tare da Al’umma wacce ta ginu bisa soyayya da girmama juna a tsakanin Al’umma. A cikin littafin Nahjul Balaga, shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya bayyana sakamakon kyakyawar mu’amala tare da Al’umma:( Mu’amalarku da mutane ta kasance idan kun koma ga Allah, Al’ummar za ta yi kukan rashin ku, idan kuma kuna raye za a dinke koyi da ku). Har ila yau a cikin littatafan , Almahasin da Man La yahdurul fakih an ruwaito hadisi daga Imam Sadik(a.s) ya ce:(Ya Ku mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka, ku sani cewa ba ya daga cikinmu wanda ba ya mallakar kansansa a yayin da yayi fishi, da kuma wanda bai yi kyakkyawar abotaka ba da abokaninsa da kuma wanda yayi mumunar mu’amala da abokanin zamansa). Kyakkyawar mu’amala hanya ce ta shiga cikin karamar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka kuma hanya ce ta shiga cikin karamar Allah madaukakin sarki kamar yadda shugabanmu Iman Bakir (a.s) ya yi ishara da shi, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Bakir(a.s) na cewa:(babu ruwan Allah ga wanda ya kama wannan hanya,(wato hanyar zuwa aikin hajji) matukar ba yanada wadannan ababe guda uku ba, na farko tsantseni wanda zai hana shi sabon Allah,na biyu hakurin da zai sanya ya mallaki kansa yayin da rai ya bace, sai kuma na uku kyakkyawar abotaka da kyakkyawar kuma mu’amala da Mutane) Imam Bakir (a.s) na cewa duk wanda ba shi da wadannan sifoffi guda uku to  bai hallita ba ma ya kama hanya zuwa aikin hajji ba har sai ya gyara halayansa. ***********************Musuc*************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hakika ko wani mumuni ana bukatar ya dabi’antu da irin wadannan kyawawen dabi’u, ya zamanto mai hakuri, mai tsantseni da kuma kyakkyawar abotaka tare da ko wani mutune , abokin tafiya ne a ko kuma abokin mu’amala ne na yau da kulun, tare da iyalan ne ko kuma abokanai ne na aiki ko kuma makobtane ne nay au da kulun da sauransu,a cikin littatafen Kafi da Almahasin an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:(ka kasance mai kyakkayawar mu’amala tare da wanda ka ke tare da su, ka kiyaye firta kalaman da za su cutar da abokinka ko kuma wanda ka ke tare da su, ka kasance mai hadiye fishi yayin da rai ya bace , ka rake yawan wassani da zolaya wanda hakan na iya batawa abokinka rai, ka zamanto mai shunfuda afuwa da yafiya a ko wani lokaci……..) Daga cikin misdakin kyakkyawar abotaka ka kasance mai taimako da abin hanunka daidai gwalgwado, imam Bakir (a.s) ya ce (duk mutuman da ke  abotaka da shi, kuma idan har za ka iya ya kasance hanunka ne kulun a sama wato kai ne mai bayarwa ko kuma mai taimaka ma sa ,to ka bayar ko kuma ka taimakama sa).maluman hadisi sun yi ta’aliki dangane da wannan hadisi sun ce idan kuna abotaka da mutune to ka zamanto a wani lokaci ka shiga gabansa wajen yi masa karamci, kautatawa, da kuma kokarin shafe masa hawaye duk lokacin da hajar hakan ta taso a cikin ko wani yanayi  da makamantansu. Har ila yau daga cikin misdakin kyakkyawar abotaka,boye sirrin aboki da kuma aibinsa,yafemasa a bisa kurakuran da yai maka, kiyaye abinda zai cutar da shi, da kuma giramama shi, Imam Bakir (a.s) ya ce:(ku giramama abokaninku,ku boye sirrinsu kadda ku cutar da junanku kada ku kasance masu hassadar junanku,ina galgadinku da ku kiyayi rowa kuma ku zamanto bayin Allah muhklisai) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzitamu da kyakkyawar mu’amala tare da abokane da ma mutane baki daya da kuma samun kusanci a gareshi don albarkar Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka. ******************Musuc************************** Masu saurare, a nan za mu dasa aya ganin lakacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka tallafawa shiri, musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.    
More in this category: « Shiri Na 31 Shiri Na 33 »

Add comment


Security code
Refresh