An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:09

Shiri Na 31

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin zai yi bayyani a kan yin  adalci yayin mu’amala da Al’ummar musulmi  har ma da wadanda ba musulmi ba , amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. ************************Musuc***************************** A cikin suratu Ma’ida Aya ta 8 Allah madaukin sarki na cewa:(Ya Ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku zamanto masu tsayawa sosai da hakkokin Allah, masu bada shaidar gaskiya kada  kin wasu Mutane ya hana ku yin adalci. Ku yi adalci, shi ya fi kusa da tsoron Allah. Kuma ku ji tsoron Allah. Hakika Allah masanin abin da kuke aikatawa ne). Har ila yau a cikin wannan surat wani bangare na Aya ta 2 Allah madaukakin sarki na cewa:(kada kuma kiyayar wasu Mutane, don sun hana ku isa massallaci mai alfarma, ta sa ku yi ta’adda) a wannan bangare na Aya an ambato Kalmar (لاَ يَجْرِمَنَّكُمْ)ma’anarsa shine kada ya sanya ku cikin wani aikin da ba na gaskiya, Kalmar (شَنَآنُ)kuwa ma’anarta ita ce kiyayya da adawa mai tsanani.ma’ana kadda tsakanin kiyayya ya sanya ku ku aikata wani aiki da ya sabawa gabskiya. Masu saurare wadannan ayoyi masu albarka suna umarce mu da yin kyakkyawar mu’amala gami da adalci wajen mu’amalarmu da jama’a musulmi  har ma da wadanda kiyayya ta shiga tsakaninku ko kuma  makiya Allah madaukakin sarki , Allah ya umarce mu da mu kiyayi yi masu adawa ta ba gaira babu dalili. Irin wadannan kyawawen dabi’u na daga cikin misdakin da hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka ke yin kira a kansu, ma’ana kyakyawar mu’amala da bayin Allah har ma da wadanda  ba musulmi ba. A cikin littafin Ma’anil Akhbar na shek Saduk (R.A) an ruwaito hadisi daga shugabanmu Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib(a.s)ya ce (ka sanya ababe biyu a cikin zuciyarka, bukatuwa zuwa ga Mutane da kuma wadatuwa daga garesu,bukatarka a garesu ta kasance cikin tattausar magana , fara’a,sakin fuska da kyakyawar mu’amala,wadatarka a garesu ta kasance daga abin hanunsu , idan kayi haka ba shakka za ka kiyaye  mutuncinka  da izzarka a tsakanin Al’umma). A cikin littafin Kafi na sikatu islam kulaini an ruwaito hadisi daga Mu’awiya bn wahab ya tambayi shugabanmu Imam Sadik (a.s) yaya ya kamata mu yi mu’amala tsakaninmu da mutananmu da kuma wadanda muke mu’amala da su ta yau da kulun wadanda ba mazahabarmu guda ba, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa:(ku dubi shugabaninku wadanda kuke koyi da su sai ku aikata abinda suke aikata, na rantse da Allah hakika sun kasance masu ziyartar marassa lafiyarsu,kuma suna halartar Jana’izarsu, kuma suna bayar da shaida mai kyau a garesu, suna kuma riko da kuma tabbatar da Amanar da suka basu) wannan shine abinda shugabaninku ke yi domin haka kuma kuyi koyi da shi. ****************Musuc***************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani ne dangane da wasiyar  shugabanmu Imam Sadik (a.s) wacce yayi wa mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka da  aka ruwaito a cikin Littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini(r.a), a cikin wannan wasiya Imam(a.s) na cewa:(ina yi maku wasiya da tsoron Allah madaukakin sarki ,masu kiyaye addininsu,ijtihadi da kokari saboda Allah, masu gaskiya cikin kalamansu, kuma  ku zamanto masu rikon amana) ku zamanto masu rikon amana ga shugabaninku masu tsoron Allah ne ko fajirai ne, ku kiyaye hakinsu, hakika duk mutuman da ya kiyaye addininsa, mai gaskiya cikin kalamansa, ya cika amanar da aka bashi kuma ya kyautata mu’amalarsa da mutane daga cikin ku, sai ake ce wannan ja’afari ne ma’ana mabiyin mazahabar Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ne ko kuma mabiyin tafarkin iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka ne wannan abu na sanya farin cikin a cikin zuciya ta kuma shima zai yi farin ciki da hakan, ko kuma an ce wannan shine dabi’un Imam ja’afaru Sadik (a.s), wallahi  na ji babana (a.s) na cewa madalla ga mutuman da ya kasance a tsakanin kabilarsa ko kuma mutanan sa mai rikon gaskiya da kuma rike amana mai fadar gaskiya a kalamansa, yayin da ya bar  duniya , jama’arsa  ko kabilarsa  za ta dingaambatansa da alheri tana cewa kamar wane, ya rike mana amanar mu kuma ya kasance mai gaskiya a kalamansa, wannan kyawawen dabi’u sune ake bukata ga duk wani mabiyin tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka, da duk wani musulmi da ma duk wani ma wanda yake muwahidi ma’ana wanda yake kadaita Allah madaukakin sarki guda daya wajen bautarsa . *************************Musuc**************************** Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe a nan za mu dasa Aya sai kuma a Maku na daga za a jimu dauke da wani shirin a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri,wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.  
More in this category: « Shiri Na 31 Shiri Na 32 »

Add comment


Security code
Refresh