An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:07

Shiri Na 30

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin zai yi bayyani a kan kyakkyawan mu’ala da dukkanin Al’umma, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. ********************Musuc******************************** Masu saurare kyakkyawar mu’amala da Mutane na daga cikin kyawawen dabi’u da Nassi da dama suka yi umarni da shi, a cikin suratu Bakara Aya ta 83 Allah madaukakin sarki na cewa:(kuma (ku tuna) lokacin da muka daura alkawari da Bani-Isra’ila (kan) kada ku bauta wa (kowa) sai Allah, kuma ku kautata wa mahaifa da makusanta da Marayu da Miskinai kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyawar magana, ku tsai da salla ku bada zakka, sannan kuka bada baya sai kadan daga cikinku,alhali kuwa ku kuna masu bijerewa da (alkawarin).) a cikin wannan Aya mai albarka hakika Allah madaukakin sarki ya bada umarni da kyakkyawar mu’amala ta musaman da kuma kyautatawa ga wasu kebabun Mutane kamar iyaye, makusanta, Marayu da kuma Miskinai sannan kuma ya yi umarni da kyakkyawar mu’amala da sauren Mutane baki daya. A cikin Tafsirin Majma’ul Bayan an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayin da yake fassara fadar Allah madaukakin sarki:( kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyawar magana).sai Imam (a.s) ku fada wa Mutane abinda ku kanku ku kafi so a fada maku domin Allah madaukakin sarki ya na fishi da masu La’anta, zaki da kuma fadar mumanar kalamai a kan mumunai, mai yawan alfahasha, mai yawan roko da tambayar mutane kuma Allah madaukakin sarki ya na son mai hakuri kuma mai kamun kai). Masu a cikin wannan hadisi za mu fahimci cewa fadar Allah madaukakin sarki na cewa:( kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyawar magana) bai takaita kawai a kan magana ta baki , har da aiki ya shafa kamar yadda aka ruwaito wani hadisi a cikin Tafsiru Ayyashi inda aka ce daya daga cikin sahaban Imam sadik (a.s) ya tambayeshi yaya matsayin mutuman da ya ciyar da matanbayi ba tare da ya san cewa musulmi ne ko kuma kafiri ne? sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa babu laifi ga Mutuman da ciyar da Mutune ba tare da yasan wilayarsa ba, ko kuma kiyayyarsa ba, ma’ana musulmi ne ko kafiri ne mai bin tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka ne ko kuma aksin haka domin Allah madaukakin sarki na cewa:( kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyawar magana) *********************Musuc***************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai fara da hadisin shugabanmu Imam Sadik (a.s), a cikin littafin Usul Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwaito wani dogon hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s),inda a cikin wani bangare na wannan Hadisi Imam (a.s) na cewa:(hakika Allah madaukakin sarki ya wajabta Imani bisa gabobin bani-adama kuma ya rarraba su  a kan wani gaba(ma’ana ko wani gaba na bani-adam a kwai umarnin da kuma hani a kansa) kuma aka wajabtawa harshe yin magana da firta abinda yake cikin zuciya sannan ya umarce shi da firta kyawawen kalamai, Allah madaukakin sarki na cewa:( kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyawar magana) hakika a cikin wannan hadisi za mu fahimci cewa kyakyawar magana da Mutane  na daga cikin misdakin kyakkyawar mu’amala da Nassi masu yawa suka yi umarni a kansa.a cikin littafin Assara’ir na Allama Ibn Idriss Alhilly an ruwaito hadisi daga Imam Sadik:(ina yi maku wasiya da tsoron Allah kada kuma ku dora Mutane a bisa kafadunku sai ku kaskanta, domin Allah madaukakin sarki yana cewa (kuma ku rika yi wa Mutane kyakkyawar magana) sannan ya ce ku ziyarci marassa lafiyar su, ku halarci bisne matatunsu kuma ku yi kyakyawar shaida a kan su bisa abinda kuka sani na alheri kuma idan kun san wani abu a kansu da zai cutar da addini ku ba shaida a kansu,ku yi salla tare da su ku halaci masallatansu ba tare da gwada wani babbanci ba). Masu saurare dangane da fadar Imam Sadik (a.s) na cewa kada kuma ku dora Mutane a bisa kafadunku sai ku kaskanta ma’ana kada ku wulakanta su, hakika kyakkyawar mu’amala tare da Mutane har ma da wadanda ba akidar ku guda bay a kan zamanto sanadiyar kare wa mai shi da cutuwa da kaskanci a tsakanin Al’umma, kuma hanya ce ta tantance abu mai kyau, yayin kyakkyawar mu’amala da Mutane.domin yin hakan yak an janyo zukatan mutane su karkata a gare shi kuma ta wannan hanya ce  za a gane kyakyawar mahangarsu, da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya mu daga cikin su ma’ana cikin masu kyakkyawar mu’amala da Mutane domin shi Allah mai ji ne kuma mai karbar Addu’a ne. *************************Musuc*************************** Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe a nan za mu dasa Aya sai kuma a Maku na daga za a jimu dauke da wani shirin a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammal musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri,wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.
More in this category: « Shiri Na 29 Shiri Na 31 »

Add comment


Security code
Refresh