An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 June 2015 07:06

Shiri Na 29

Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani dangane da mahimancin hadiye fishi tare da irin kyawawen sakamokon dake tattare da shi, domin mahimancin wannan maudu'in shirin na Yau ma zai ci gaba daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. *******************Musuc********************************** Masu saurare, a cikin littafin Man La Yahdurul Fakih, an ruwaito hadisi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsaraka na cewa:(duk wanda ya hadiye fishinsa a yayin da Rai ya bace Allah madaukakin sarki zai sakamaka da lada mai yawa kuma duk wanda ya yi hakuri a kan wata Masifa da ta same shi  Allah zai canza masa da mafi alheri). A wata riwayar kuwa Manzon Allah (S.W.S) ya ce:(wanda ya hadiye fishinsa bisa wani zalunci,ya ki yin ramako alhali yanada ikon ramawa,Allah madaukakin sarki zai bashi ladan daidai da na Shahidi (ma’ana wanda ya rasu a kan hanyar Allah)). Duk wanda ya kasance halinsa ne yin hakuri tare da hadiye fishi yayin da aka bata masa rai, zai yi ta samun irin wannan lada mai tarun yawa kuma wannan na daga cikin karamcin Allah madaukakin sarki. A karshen khudbar da Ma’aikin Allah (S.W.S) yayiwa  Al’ummar musulmi kafin kaurarsa ya ce (wanda ya hadiye fishinsa yayin da rai ya bace,kuma ya yafewa dan uwansa Allah madaukakin sarki zai bashi ladan shahidi(ma’ana wanda ya rasu ta hanyar yaki saboda Allah ). Masu saurare hakika hadiye fishi na daga cikin kyawawen aiyuka da Allah madaukakin sarki yake arzuta masu shi da dabi’u masu girma irin na Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, hakika a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa:(Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce shin kuna son in baku labarin wanda ya fi kama da ni daga cikinku?sai sahabai suka ce Na’am Ya Ma’aikin Allah. Sai ya ce wanda ya fi kama da ni daga cikinku wanda ya fi ku kyawawen dabi’u, kuma ya fi ku tausasawa ‘yan uwansu, ya fi kuma kyautatawa na kusa da shi, ya fi ku bayyana tsananin soyayarsa ga ‘yan uwansa na addini, kuma ya fi ku hakuri a kan gaskiya, ya kuma fi ku hadiye fishinsa yayin da rai ya bace, kuma ya fi kautatawa wajen yin afuwa da yafiya, ya fi kowa yiwa kansa adalci wajen yarda da fishi). **************************Musuc*************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa,a ci gaban shirin za mu fara da kalaman Amiru mumunin Aliyu ban Abi Talib (a.s).a cikin littafin Algurar, Shek Amadi yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ruwaito hadisi daga Amiri mumunin Aliyu bn abi talib (a.s) na cewa(dabi’ar mumuni yi yin Nasiha kuma kyakyawar halinsa hadiye  fishi a duk lokacin da ya fuskanci fashin rai ko kuma ya yi fishi) A cikin wanin Hadisi kuwa Imam Ali(a.s):(mafi fifiko daga cikin Mutane, wanda ya hadiye fishinsa yayin da ya fuskanci wani bacin rai kuma yayi hakuri a kan kan wani zalunci ko kuma wani laifi da aka yi masa yayin da ya keda ikon ramawa). Har ila a cikin wata riwayar kuma ya na cewa:(duk mai tsoron Allah ba bayyana fishinsa  a kan dan uwansa ba). Masu saurare daga cikin albarkar da Allah madaukakin sarki ya yi wa halaye na masu hadiye fishi, tsarkake Zuciya daga duk wani rauni tare da karfafata daga fuskantar duk wani kaidin shaidan kuma wannan shi zai sanya mai wannan dabi’a ya samu babban rabo da karamar Ubangiji madaukakin sarki,Amiru muminin Aliyu bn Abi talib (a.s) kamar yadda ya zo cikin littafin Algurar (mai hakuri shine wanda ya kawar da duk wani rauni da yake da shi cikin zuciyarsa). Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Ya rabauta, ga wanda yake hadiye fishinsa bai bayyana shi ba, kuma ya sabawa zuciyarsa bai hallaka ba). Daga cikin wasikoki da yake rubuta sahabansa an ruwaito wasikar da Imam Ali(a.s) ya rubutawa Haris Hamdani a cikin Littafin Nahjul-balaga ya ce Ya Haris ka hadiye fishinka yayin da Rai ya bace ka yafe a yayin da kake karfin ramawa kuma kayi hakuri a yayin da kayi fishi ka zamanto mai sakin fuska da faraha yayin da kake kan karagar milki sai ka samu lafiya daga duk wani koke koken wadanda kake jagoranta) Daga karshe bari mu karanto hadisin da aka ruwaito daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) inda yake cewa (duk wanda ya rike fishinsa Allah madaukakin sarki zai boye masa aibinsa) *************************Musuc*************************** Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe ………………………………………..
More in this category: « Shiri Na 28 Shiri Na 30 »

Add comment


Security code
Refresh