An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Kyawawan Dabiu

Kyawawan Dabiu (42)

Monday, 29 June 2015 07:19

Shiri Na 41

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan kyakkyawar mu’amala da wanda yake kasa da kai, ma’ana wanda yake aiki kalkashinka a Ma’aikata ne ko kuma a gidanka ne, ammam kafin mu shiga cikin shirin ga wannan. *************************Musuc**************************** Hakika Allah madaukakin sarki  ya yi umarni a cikin ayoyi da dama na Alkur’ani mai tsarki ga kyakkyawar mu’amala tare da wadanda suke hidma a kalkashinka, misali a cikin Suratu Nisa’I Aya ta 36 Allah madaukakin sarki ya yi umarni da a kautatawa wasu gungu na Mutane, daga cikinsu har da wadanda sashinku  suka mallaka  wannan shine a matsayin misali na masu hidma a kalkashinku.kamar yadda a cikin Nassosi da dama aka yi hani da yin mumunar mu’amala da su tare da kuntata masu. Kamar yadda  tafarkin Ma’aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka yake wajen kyakkyawar mu’amala da masu yi masu hidma, a cikin Littafin Khara’ij an ruwaito hadisi daga Salman Muhamadi yardar Allah ta ttabata a gareshi ya ce Fatima diyar Ma’aikin Allah amincin Allah ya tabbata a garesu ta kasance a zaune tana nika Sha’ir  domin ta yi abincin da za su ci a wannan rana sai tayi rauni ga jini yana zuba daga hanunta , a bangare guda na gidan ga Danta Imam Husain (a.s) ya na kai kawo saboda yunwa,  sai na ce mata ya ‘yar Ma’aikin Allah  kin ji rauni ga jini ya na zuba a hanunki, mi zai hana ki bar aikin sai Fidda wato mai aikinta ta ci gaba da wannan aiki, sai Fatima (a.s) Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi wasici a gareni da ya kasance mu raba aiki da ita, jiya ranar  ta ce ita ta gudanar da aiyukan gidan kuma nima yau rana ta ce.) har ila yau an ruwaito wani hadisi daga  shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa:(a cikin Littafin Ma’aikin Allah (SAW) an ce idan ku sanya wadanda  sashinku ya mallaka aiki kuma aikin nan yayi masu tsauri to ku tayesu ma’ana ku yi aikin tare da su, Imam (a.s) kuma Babana ya kasance idan ya sanya su aiki ya kan zuwa wajen aikin yana kallon yadda suke aikin idan ya ga aiki ya yi masu tsauri sai yayi bismillah ya kama aikin tare da su, idan kuma aikin bas hi da yawa ko kuma bas hi da wahala, sai ya gyalu su ci gaba da aikin sannan ya koma Majalisinsa).a cikin littafin Irshad na Sheik Mufid an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa aka ce  Imam Sajjad (a.s)  ya kira Bawansa har so biyu ba tare da ya amsa ba sai a karo na uku ya amsa , sai Imam (a.s) ya ce masa ya dana shin  ba ka ji kiran da na yi maka ba? sai wannan bawa ya ce ba shakka na ji kiran, sai Imam (a.s) ya ce to minene ya hanaka amsawa? Sai wannan Bawa ya ce na yi imanin cewa ba za kayi mani ukuba ba, sai Imam (a.s) godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya sanya masu hidma a gareni suka yi imani da ni).a cikin littafin Kafi na shekh Kulaini an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa aka ce  Imam Sadik (a.s)  ya aiki mai yi masa hidma ma’ana bawansa  bayan wani lokaci ya ga ya jima bai dawo ba , sai Imam (a.s) ya bi sonsa, ya na tafiya sai gansa a wani guri a kwonce yana kwana sai ya zauna a kusa da kansa ya na yi masa filfitu har sai da ya tashi ) har ila yau an ruwaito wani hadisi daga Amiri mumunin Aliyu bn Abi talib(a.s) yana cewa:(kada ku yi tsawa ga masu yi muku hidma, ku kuma yafe masu  idan sun  saba maku).a cikin littafin Makarimul Akhlaq an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda ya zalunci wanda ya yi masa aiki, Allah madaukakin sarki zai bata kyawawen aiyuka sannan ya haramta masa jin kamshim Aljanna), har ila yau daga wasiyoyin Ma’aikin Allah (SAW) wadanda aka ruwito cikin littafin Shihabul Akhbar ya ce:(ku biya wanda yayi maku aiki tun kafin zufarsa ta bushe). *******************************Musuc********************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani  kan kirmama matanbayi ko kuma mu ce alamjiri, na neman abinci ko kuma matambayin ilimin addini ne da saurensu, a cikin suratu Duha Aya ta 10,Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma mai tambaya kada ka yi masa tsawa), a cikin tafsiru Nuru Sakalaini an ruwaito hadisi daga imam Bakir (a.s) ya ce :(ya kasance daga cikin wasiyoyin Allah madaukakin sarki ga Annabi Musa (a.s) ya ce masa Ka kirmama matambayi ko da da kadan ne ko kuma  ta hanyar amsa mai kyau) wannan na daga cikin misdakin  ni’imar Allah madaukakin na amsa bukatar matambayi da kuma taimaka masa da abinda ya sawwaka ko kuma karfafa masa gwiwa da maganar mai kyau. A wani hadisin kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(kadda ku yanke maganar Matambayi yayin da yake tambaya ka gyale shi ya  gama bayyana damuwarsa da kuma yanayinsa , idan Allah madaukakin sarki ya horemaka to ka taimaka masa idan kuma ba ka da shi ka yi masa kyakkyawan bayyani) har ila yau a wata riwayar ma’aikin Allah (SAW) ya ce:( ku dubi matanbayi yayin da yake tambayarsa idan zuciyarku ta ka raya to ku bashi hakika gaskiya yak e fada). Masu saurare daga cikin misdakin  kirmama matanbayi wadatar da shi tare kuma da kiransa ya rubuta bukantunsa idan ya kasance a bainar jama’a domin ya kare mutuncinsa a gabansu. Shek Saduk ya ruwaito hadisi a cikin littafinsa Amaly inda a cikin hadisin aka ce wani Mutune ya je wajen Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce ya Amiru mumunin inada bukata a gareka Sai Imam (a.s)  yace  rubuta bukatunka domin na fahimci cewa bayyana bukatunta a gaban jama’a zai cutar da kai, sai wannan matanbayi ya rubuta cewa ni Fakiri ne kuma ina bukatar taimakon sai Imam (a.s) ya bada umarni aka bashi sutura kala biyu tare da dinare 100, sai aka ce Ya Amiri mumunin (a.s) hakika ka arzuta shi, sai Imam (a.s) ya ce na ji ma’aikin Allah (SAW) na cewa ku taimakawa Mutane daidai da bukatarsa). Masu saurare, hakika tafarkin Iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka ya  kasance kiyaye karamar matanbayi kuma shaidu da dama sun tabbatar da hakan za mu takaitu da wannan hadisi da Sikatu islam Kulaini ya ruwaito a cikin littafinsa Alkafi,  wani Mutune ya je wajen Imam Rida (a.s) sai ya ce masa ni ina daga cikin masoyanka kuma masiyin iyaynaka da kakanunka, kuma matafiyi ne sai guzirina ya kare ba ni da abinda zai mayar da ni gida, ina bukatar ramtse, idan  Allah madaukakin sarki ya mayar da ni gida zan yi sadaka a memakonka bisa abinda ka ramta min,sai Imam (a.s) ya ce masa ya zauna tare da yi masa Addu’a sannan ya ci gaba da karantar da Mutane, har lokacin da aka kammala mutane suka watse , wadanda suka rage shi da Suleiman Ja’afari ya nemi izini sannan ya shiga cikin gidansa, bayan wani lokaci, sai ya fito da wata  jikar gudi a hanunsa  yayin da ya rufe fuskarsa sannan ya ce ina Dan Khurasan din nan, wannan  dinari 200 ne ka yi amfani da shi wajen bulaguronka , kuma na baka wannan  kauta ba a bukatar ka yi sadaka a memako na  idan ka koma gida. Sai wannan Mutune ya tafi yana ta godiya cikin jin dadi, salman ya ce minene ya sanya ka rufe fuskarka yayin da zaka bayar da taimakon sai Imam (a.s) ya ce na rufe fuskata ne domin gudun ganin kaskancin tambaya a fuskarka) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu damar koyi da irin wadannan kyawawen dabi’u. ********************************Musuc***************** Masu saurare a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon idan Allah ya yarda , a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, …..
Monday, 29 June 2015 07:18

Shiri 40

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan falalar nuna so ga miskinai tare da tallafa masu da kuma kyautata masu, amma kafin nan bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai. ***************************Musuc********************************** Masu saurare hakika cikin ayoyi da dama na Alkur’ani mai tsarki Allah madaukakin sarki ya yi wasici ga bayinsa na su kyautatawa  miskinai,a cikin suratu Nisa’a Aya ta 36 Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma ku bauta wa Allah kada ku hana wani da shi kuma kula ga kyautatawa ma’aifa, da dangi, da marayu, da miskinai, na makoci na nesa, da abokin tafiya, da matafiyi, da abinda hannayanku suka mallaka (watau Bayi)hakika Allah bay a son wanda ya kasance mai takama mai yawan alfahari)  masu saurare kamar yadda wannan Aya mai albarka ta yi umarni ,kyautatawa miskinai ko kuma tallakawa da ma sauren gungun da ta yi ishara kan su na daga cikin misdakin tsarkaka daga girman kai da kuma jiji da kai da ganin fifiko ga  wani saboda dukiya, Arziki ko kuma milki da saurensu, daga cikin wasiyar da shugaban Hallitu Muhamad dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi wa mashhurin sahbin nan mai suna Abu Zaril Gaffari ya ce masa(ka so miskinai ko talakawa kuma ka yawaita zama da su), sheik saduk ya ruwaito hadisi daga Salman Muhamadi yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce (masoyina ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi mini wasici a abubuwa guda 7 kuma ba zan bar sub a, cikin ko wani hali, daga cikin ababen guda 7 a kwai son miskinai ko tallakawa kuma in kasance cikin kusanci da su) har ila yau shek saduk a cikin littafinsa mai suna man La Yahduruhu Fakih ya ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce :(duk wanda ya kirmama tallaka mumuni zai hadu da Allah madaukaki sarki  yana kuma Yardadde a gareshi).a cikin Littafin Tuhuful Ukul an ruwaito Hadisi daga Ma’aikin Allah ya ce (madalla ga wanda ya kaskantar da kansa saboda Allah, kuma yaji kan miskinai ko tallakawa, madalla ga wanda ya samu kudinsa ta hanyar Halal ba ta hanyar sabo ba daga cikin mumunai kuma ya ciyar da tallakawa da su). Masu saurare a bangare guda kuma wasu hadisan sun yi galgadi da jan kunne mai tsanani wajen kin kulawa da tallakawa, misali a cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih na Sheik Saduk an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce :( ku saurara , duk wanda ya ki kulawa da tallaka musulmi ko kuma ya yi masa rikon sakainar kashi, hakika ya yi wasa da kuma ko inkula da hakin Allah, kuma Allah ba zai kula shi ranar Alkiyama idan ba tuba yayi ba).har ila yau a wata riwayar Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Allah ya la’anci wanda ya wulakanta tallaka saboda Talaucinsa, duk wanda ya wulakanta tallaka saboda talaucinsa, za a kira sa a sama da makiyin Allah da kuma makiyin Annabawa, kuma ba za a karbi Addu’arsa ba, ba za a biya kuma bukatunsa ba). *************************Musuc********************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne a kan falala na  tausayin marayu da kuma kiyaye cutar da su tare da yin mu’amala da su cikin wani nau’I na tausayi ,yin hakan na daga cikin  dabi’u masu kirma daga dabi’un Allah madaukakin sarki kamar yadda ya bayyanawa Annabinsa mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka a cikin Suratu Duha Allah madaukakin sarki ya ce :(Ina rantsuwa da Hantsi*da Dare a lokacin da ya lulluba (da duhu)*Ubangijinka bai maka bankwana ba kuma bai ki k aba*kuma lalle ta karshe ce( wato Lahira)mafi alheri a gare ka daga ta farko (wato Duniya).* kuma lalle ne, Ubangijinka , zai yi ta ba ka kauta sai ka yarda*Ashe bai same ka ba maraya ba, sa’an nan  ya yi maka makoma?)suratu Duha daga Aya ta 1 zuwa 6 hakika Allah madaukakin sarki ya yi wasici da kirmama Maraya da kuma marayu , a cikin suratu Duha Aya ta 9 Allah madaukakin sarki ya ce:(saboda haka kada ka yi wa maraya tilas) har ila yau a cikin suratu Nisa’a Allah madaukakin sarki ya yi wasaici da a kyautata masu ,kamar yadda yayi galgadi gami da jan kunne na a kiyayi muzguna masu tare da mumunar mu’amala a tare su, Allah madaukakin sarki ya ce:(idan kuma makusanta da marayu da miskinai suka halarci gurin rabon (rabon gado)to ku arzuta su daga gareshi, kuma ku fada musu sananniyar magana ta Alheri*kuma wadanda su ke da,sun bar zuriya masu rauni a bayansu (watau Yara kanana) za su rika jiye masu tsoron (a cuce su) to su ji tsoron Allah (a kan dukiyar marayun da take hanunsu) kuma su fadi magana madaidaiciya*Hakika wadanda suke cin dukiyar marayu da Zalunci, to wuta ce kawai suke ci a cikin cikkunansu,kuma za su shiga cikin wata wutar mai tsanani). suratu  Nisa’I Aya ta 8 zuwa ta 10, a cikin suratu An’ami Aya ta 152 Allah madaukakin sarki ya ce:( kada kuma ku kasanci dukiyar maraya face wadda take ita ce mafi kyau har sai ya kawo karfinsa , kuma ku cika mudu da sikeli da adalci,ba mu dora wa rai sai abinda yake iyawa,to idan kuma kuka ba da shaida, to ku fadi gaskiya ko da kuwa a kan dan’uwa ne,alkawarin Allah kuma ku cika (shi), da wannan (Allah) ya yi muku wasiya don ku wa’azanta). Masu saurare, hakika Allah ya yi alkawarin babban sakamako ga masu kyakkyawar mu’amala gami da tausayi tare da Marayu, a cikin littafin Makarimul Akhlaq an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da aimincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, daga cikin wasiyoyin da ya yi wa Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(ya Ali duk wanda ya wadatar da Maraya wajen ciyar da shi da dukiyarsa har ya wadatu, Aljanna ta wajabta a gareshi, Ya Ali duk wanda ya shafi kan Maraya saboda tausayinsa, Allah madaukakin sarki zai bashi haske kan  ko wani kwara daya na cikin gashinsa a ranar Alkiyama).a cikin littafin Kurbul Isnad an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah na cewa:(duk wanda ya dauki nauyi Maraya ya kuma dauki nauyin ciyar da shi zan kasance tare da shi a cikin aljanna kamar haka, sai ma’aikin Allah ya nuna yatsarsa manuniya da kuma ta tsakiya wacce suke tare)  har ila yau a cikin khudubar ma’aikin Allah na tunkarar watan Ramadana ya ce :(duk wanda ya kirmama maraya a cikin watan Ramadana Allah zai kirmama shi a ranar da zai hadu da Allah madaukakin sarki ), har ila yau a cikin Littafin  kafi, Amiri mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce (ku tarbiyatar da Maraya da abinda kuka tarbiyatar da ‘ya’yanku), da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon aiki da wadannan wasiyu masu Albarka *******************Musuc****************************** Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.  
Monday, 29 June 2015 07:17

Shiri Na 39

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan kyakkyawar mu’amala da wanda aka ke bi bashi yayin da yake cikin tsanani na babu  ta yadda ba zai iya biyan bashin ba, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda a kayi tanadi a kan faifai. ********************************Musuc***************************** Masu saurare, hakika Allah madaukakin sarki ya wajabtawa bayinsa mumunai da su jinkirtawa wadanda suke bi bashi yayin da ba su da halin biya, a cikin suratu Bakara Aya ta 280 Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan (wanda ake bin bashin) ya kasance cikin mawuyacin hali to sai a saurara masa har zuwa lokaci da ya wadata ko kuma ya samu, idan kuka bar masu a matsayin sadaka alheri ne a gareku idan kun kasance kun sani) a cikin littafin Majma’ul bayyani an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa aka tambayi Imam Sadik (a.s) kan wanda ake bi bashi da ya kamata a jinkirta masa har ya wadata, sai Imam (a.s) ya ce :(shine  abinda yake samu baya isarsa ya ciyar da kansa kuma ya ciyar da iyalansa).wannan a bangaren yi masu jinkiri har zuwa lokacin da Allah madaukakin sarki ya hore masu, wanda ya fi kuma shine kiran da Allah madaukakin sarki yayi mana na cewa a yefe masu bashin kwata kwata kamar  yadda ya  zo a karshen wannan Aya:( idan kuka bar masu a matsayin sadaka alheri ne a gareku idan kun kasance kun sani). Masu saurare hakika  hadisai da dama sun kwadaitar da mu falalar sassauti ga wanda ake binsa bashi yayin da ba shi da halin biya tare kuma da taimaka masa, a cikin littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Imam Sadik(a.s) ya ce: (wata rana Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalansa tsarkaka ya hau minbarinsa bayan ya godewa mahalicinsa ya kuma yi wa Annabawa (A.S) salati sai yace: Ya Ku Mutane wanda yake nan ya isar da wannan sako ga wanda baya nan (ma’ana wanda bai halarci wannan guri ba) ku saurara duk wanda ya jinkirawa wanda yake bi bashi yayin da yake cikin tsanani na biya  , Allah madaukakin sarki zai bashi lada ko wata rana har lokacin da Allah ya horewa  wanda yake bi bashin ya kuma biyashi)sannan Imam Sadik (a.s) ya karanto Ayar da ta gabata mai albbarka wacce ta cikin suratu Bakara sannan yayi ta’aliki yana mai cewa  idan kusan cewa wanda ake bi bashi yana cikin tsanani ba ya iya biya, ku biya masa daga cikin   dukiyarku hakan shine alheri a gareku). A cikin Tafsiri Ayashi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda yake son Allah ya sanya shi a cikin inuwar Al’arshinsa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa, to yayi sasauci ga wanda yake cikin tsanani idan yana binsa bashi   ya kuma  yafe masa daga cikin dukiyar da yake binsa), a cikin Tafsiru Burhan an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) ya ce :(duk wanda yake son Allah ya karesa daga wutar Jahanama   to yayi sasauci ga wanda yake cikin tsanani idan yana binsa bashi kuma ya yafi masa daga cikin dukiyar da yake binsa). Imam Sadik (a.s) na cewa:(hakika Allah madaukakin sarki yana son wadanda suke yin  sassauci ga wadanda suke bi bashi a yayin da suka shiga cikin tsakani).ma’ana ba sa matsa masu a kan cewa lallai lallai sun sun biya su , sukan kyale su har  sai lokacin da Allah ya wadata su sannan sub a su). A cikin littafin sawabul A’amal na shek Saduk (k.s) an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) ya ce :(ranar Alkiyama Allah zai tayar da wasu Mutane kalkashin Al’arshin ubangiji, fuskokinsu suna   haske, suturansu daga haske, kuraren zamansu zuna haske, sai hallitu su tambaya shin wadancan Annabawa ne? sai wani mai kira daga kalkashin Al’ashi ya ce a’a wadancan ba annabawa ba ne,sai hallitun su ci gaba da tambaya Shahidai ne, sai ace masu a’a ba shahidai ba ne sai wadancan da kuke gani Mutanan da suka kasance a duniya suna saukakawa mumunaine  kuma suna yi sassauci ga wadanda suke bi bashi a yayin da suke cikin tsanani ba sa tambayarsu har sai lokacin da Allah ya wadatar da su suka biya su  da kansu). ***************************Musuc********************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan mahimanci kula da kuma himma wajen biyan bashi.a cikin littafin safinatul Bihar an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa :(kokarin da kulawa wajen biyan bashi na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci) .an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce (ku rage daukan bashi dake kawunanku domin rage daukan bashi yana kara yawan kwanuka, saboda shi cin bashi yana yana sanya karaya a zukatan masu cin bashin kuma karayar zuciya na sanya damuwa gami da karamcin kwanuka).hakika masu saurare kin biyan bashi a yayin da mutune ke da halin biya na daga cikin misdakin cin amana da sata ko da kuma ba shin na wadanda ba mumunai ba ne kai ko da na firkar Marji’a ne wacce bani umaiyya suka kirkirota , an ruwaito hadisi daga Abi Samama ya ce na shiga wajen babban Ja’afar Imam Bakir (a.s) sai nace masa  na sanya fansar raina a gareka ina son zuwa Makka domin in sauke farari , sai dai a kwai bashi a kaina na mabiyin birkar Marji’a mi za ku ce dangane da hakan, sai Imam (a.s) ya ce ma saka koma ka biya bashinka, ka yi jiran saduwa da Allah madaukakin sarki babu bashi a kanka, hakika mumuni bay a cin amana). Imam Sadik (a.s) ya ce : (barayi kala uku ne daga cikinsu wanda ya dauki bashi kuma bashi da niyar biya).a wata riwayar kuma Imam (a.s) na cewa:(duk wanda ya rufe dan uwansa mumuni saboda yana binsa bashi kuma ya san ba shi da halin biya, wallahi ba zai dandana abincin Aljanna ba, kuma ba zai sha daga cikin kogin Rahikul Makhtum ba).har ila yau a cikin littafin Safinatul Bihar shahararen malamin tafsiri da hadisi shek Kummi (yardar Allah ta tabbata a gareshi)ya ce an  ruwaito hadisi daga Mu’awiya bn wahab ya ce: na cewa Imam Sadik (a.s) mun samu labarin cewa wani mutune daga cikin Ansar ya mutu da bashi a kansa sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ki ya yi masa Salla, sannan ya ce kadda ku yiwa dan uwanku salla har sai an biya bashin dake kansa, Imam Sadik (a.s) ya ce hakika wannan labari gaskiya ne domin Ma’aikin Allah ya yi haka ne don Mutane su yi yarjejjeniya ta gaskiya da wadanda suke bin dan uwansu bashi, kuma wadanda ake bi bashi su gaggauta biyan bashin dake kansu sannan kuma su fasa sako sako wajen biyan bashin). A karshe  bari mu karanto wani hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) inda yake cewa:(ko wani zunubi a kan karkare ne ga wanda ya rasa ransa ta hanyar Allah amma banda bashi, domin shi bashi sai an biyashi ko kuma wanda yake bi bashin ya yafe) *****************************Musuc******************************** Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.  
Monday, 29 June 2015 07:16

Shiri Na 38

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne kan karin ni’ima da kyautatawa ga wanda yake godiya, kafin mu shiga shirin ga wannan *******************Musuc*********************** Masu saurare godiya ga hallitun Allah madaukakin sarki na daga cikin kyawawen dabi’u kuma duk wanda yake godewa wanda ya kautata masa kamar ya godewa ubangijinsa ne kuma yayi aiki da hadisin Ma’aikin Allah tsira da amnicin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ne wanda yake cewa (ku dabi’antu da dabi’un Allah) Hakika daga cikin siffofin Allah shi mai godiwa da kuma gafara ne kuma yayiwa alkawarin karin ni’ima ga masu gode masa, a cikin suratu Ibrahimu Aya ta 7 Allah madaukakin sarki na cewa :(lallai idan kuka  gode wa Ni’imata ba shakka zan kara muku).a cikin littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake yiwa daya daga cikin ‘ya’yansa  nasiha yana mai cewa (ya kai Dana ka godewa wanda ya ni’imtar da ku, ka taimakawa wanda ya gode maka domin ni’ima ba za ta taba gushe maka mutukar kana godiya, kuma ba zama a tare da kai ba matukar ka kafircewa wanda ya baka ni’imar ba,mai godiya da gidarsa za a kara masa ni’imar da ta wajabta a gode masa sannan sai ya karanto wannan aya mai albarka (lallai idan kuka  gode wa Ni’imata ba shakka zan kara muku, idan kuwa kuka butulce, hakika azabata mai tsanani ce). Suratu Ibrahimu Aya ta 7, a cikin littafin kafi na sikatu islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Masma’a bn Abdulmalik ya ce mun kasance a zaune wajen shugabanmu Imam Sadik (a.s) a Mina a gabanmu a kwai Inabi muna ci ,sai wani Alamajiri  ya zo yayi bara,Imam (a.s) ya yi umarni da a dauki wani reshe daga cikin inabin da muke ci  a bashi, sai wannan almajiri ya ce shi ba ya bukatar Inabi, idan dai a kwai Dirhami ma’ana kudi a bashi, wato abinda ya bukata kudi , shi bay a bukatar  abinci,sai Imam (a.s) ya ce Allah ya buda maka sai wannan almajiri ya ta fi bayan ya dan wani lokaci ,sai ya dawo ya ce a bashi wannan inabi da aka bashi yaki karba a baya, Imam (a.s) ya ce Allah ya wassa’a maka bai ba shi ba, bayan dan wani lokaci sai ga wani Almajirin na daban ya zo yayi bara sai Imam (a.s) ya dauki Inabi kwara uku ya bashi, sai wannan almajiri ya karba da hanu biyu sannan ya ce na godewa Allah madaukakin sarki da ya arzitani da wannan, sai Imam (a.s) ya tsaida shi sannan ya cika masa hanunsa da Inabi,sai almajirin ya ci gaba da cewa godiya ga Allah madaukaki da ya kara arzuta ni da wannan.sai Imam (a.s) ya sake tsayar da shi, sannan ya tambayi yaronsa shin a kwai wasu Dirhami wato kudi na wancan lokaci   a gurinka? Sai ya ce masa a kwai Dirhami 20 , Imam (a.s) ya amsa ya baiwa wannan almajiri, almajirin ya kara da cewa  godiya ta tabbata ga Allah wannan daga wajenka ,kai kadai ne mai ikon yin haka ba kada abokin tarayya, sai Imam (a.s) ya sake tsayar da shi sannan ya cire wata riga a jikginsa ya meka masa , sai wannan almajiri ya ce na godewa Allah madaukakin sarki da ya suturtar da ni da wannan, a wata rawayar kuwa ya ce wa Imam (a.s)Allah ya saka maka da alheri).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon dabi’antuwa da irin wadannan kyawawen dabi’un musulinci. ********************Musuc**************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan kaskantar da kai ga mai aikata alheri ko kuma rashin girmar kai ga wadanda suke bayarwa a gaban mabukata  ,a cikin suratu Mudasir Aya ta 6 Allah madaukakin sarki ya ce :(kada ka ba da abu don ka nemi mafi yawa daga gareshi) An ruwaito hadisi a cikin littafin Kafi daga shugabanmu Imam Bakir(a.s) yayin da yake fassara wannan Aya ya ce:(kada ka bukaci mafi yawa kan alherin da ka aikata saboda Allah), a cikin littafin Nahjul balaga an ruwaito hadisi daga Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce ku kiyayi neman lada mai yawa saboda aiyukan da ku ka yi mutane ko kuma ku kanbama aiyuka da kuka yi Mutane ko kuma kin cika alkawarukan da kuka yiwa Mutane domin hakan ya na bata aiyukan da ku ka yi masu kyau kuma yana tafiya da hasken gaskiya). Masu saurare Alkur’ani mai girma ya hana bankama aiyuka da Bawa da aikata don neman mai yawa kan abinda ka bayar ko kuma ka aikata,hadisai da dama sun umarce mu da aiyukan alheri gami da kyautatawa kuma mu kallesu a matsayin wani dan aiki kadan, hakika Allah madaukakin sarki cikin tausayinsa ya sanya hakan a matsayin wani shi’ari ko alama ga wadanda aka kyautatawa daidai golgwadon matsayinsu da aiyukansu a wajensa.a cikin littafin Kafi na sikatu Islam kulaini an ruwaito Hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(shin b aka ganin cewa kyautatawa ba ta gyaruwa sai da abubuwa guda uku: kaskantar da ita, boyeta da kuma gaggautata,domin idan ka kaskantar da ita za ta, ka girmamata a wajen wand aka kyautata ma, kuma idan ka boye ta to ba shakka ka cika ta,ma’ana ka aikatata yadda ake bukata ka zo da ita idan kuma ga gaggauta aikatata to ka amintu daga waswasin shaidani kuma yak an sanya mabukaci yayi farin ciki ga kyautatawar). Masu saurare kamar yadda aka saurara a wannan hadisi kaskantar da kai ga mai taimako a gaban mabukaci na daga cikin cikar kyautatawa, haka zalika ma bayar da taimakon cikin sirri,hadisai da dama sun yi bayyani a kan cewa bayan da sadaka cikin sirri ka kiyaye mutuncin mabukacin da karamarsa kuma hakan na kawar da kirmar kai gami da jiji da kai ga mai bayarwa.kamar yadda bayar da sadakar cikin gaggawa kan sanyar farin ciki a cikin zukatan mabukan da wadanda suka taibaya kuma Allah madaukakin sarki yak an daga hajjarsa da wannan,abin al’ajabi da kuma Lutufinsa, Allah madaukakin sarki ya kaddarawa masu kyautata bin wadannan hanyoyin guda uku wajen bayan da taimako ko kuma sadaka domin yin hakan shi ze kirmama ladansu kuma ya bayyana mutuncinsu da karamcinsu a idanun mutane.a cikin Littafin Nahjul Balaga an ruwaito hadisi daga Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa:(biyan bukatu ba su tabbatuwa sai da ababe guda uku,da gaskantar da ita domin a girmamata, da boyeta domin a bayyana ta,da gaggautata domin ayi fara’a da ita).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon koyi da wadannan kyawawen dabi’u. *****************************Musuc************************** Masu saurare, ganin lokaci na hararenmu a nan zamu dakata, sai kuma a maku na gaba da yardar Allah madaukakin sarki za a jimu dauke da wani shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri,wassalama aleikum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.  
Monday, 29 June 2015 07:15

Shiri Na 37

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani ne  a kan godiya ga ni’imar Allah madaukakin sarki, amma kafin nan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai ********************Musuc*************************** Masu saurare, godewa N’imar Allah madaukakin sarki na daga cikin kyawawen dabi’u na addinin musulinci ya yi umarni da shi kuma Allah madaukakin sarki ya yi alkawarin kari ga duk wanda ya gode masa a kan ni’imar da ya basa, a cikin suratu Ibarhim Aya ta 7 Allah madauakin sarki na cewa:(kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar cewa: Lallai idan kuka gode wa (Ni’imata )ba shakka zan kara muku, idan kuwa kuka butulce, to hakika azabata mai tsanani ce.) Daga cikin misdakin godewa Allah madaukakin sarki godiya ga wanda Allah ya sanya daga hanunsa ni’imar Allah ta isa zuwa ga bawansa, a cikin littafin Kafi na sikatu Islam kulaini an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sajjad (a.s) na cewa :(hakika Allah madaukakin sarki ya na son zuciya mai nadama, kuma ya na son bawa mai godiya,a ranar Kiyama Allah madaukakin sarki  zai cewa wani bawa daga cikin bayinsa shin ka godewa wane? Sai wannan Bawa ya ce A’a sai dai godiyata a gareka ne kawai ya Ubangiji, sai Allah ya ce ba ka gode mani ba, matukar dai ba ka gode masa ba, sai Imam (a.s) godiyar ku ga Allah ita ce godewa mutanan da suka yi maku alheri) Masu saurare daga cikin falalar godiya ga ma’abota alheri shine karfafa su wajen ci gaba da yin alherin da suke yi  kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yi ishara da hakan a cikin wani hadisin da aka ruwaito cikin littafin Kafi inda Imam (a.s) ke cewa:(Allah ya la’anci wanda yake yanke hanyar alheri, sai aka tambayeshi su wane masu yanke hanyar alheri?mutuman da aka yi masa alheri ya kafirce ma’ana yarena alherin da aka yi masa ya ki godewa kuma hakan ya sanya wanda ya yi alheri ya yi sanhi ya ka sa yiwa waninsa alherin). A cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda aka kautata masa ya yi kokori wajen sakawa wanda ya yi masa da ma fi kyau, idan kuma ya kasa ya gode masa,duk wanda ya ki yayi wannan to ya kafircewa ni’imar Allah).har ila yau a cikin littafin Kafi Ma’aikin Allah (S.W.S) ya ce (Allah madaukakin sarki bai budewa Bawa kofar godiya ba sai da ya tanadar  masa hanyar  kari). A cikin littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Allah madaukakin sarki yana cewa:(hakika na daukawa kaina alkawarin ba zan karbi godiyar bawa ba a kan ni’imar da na yi masa har sai ya godewa wanda ta hanyar sa ce wannan ni’ima ta isa gareshi daga cikin bayina) *********************Musuc***************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da riwayar shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik(a.s) wacce aka ruwaito a cikin littafin Tahzibul Ahklaq inda Imam (a.s) ke cewa:(hakika Allah madaukakin sarki ya yi wa wasu Mutane daga cikin Bayinsa Ni’ima sai suka ki su gode masa, sai wannan ni’ima ta kasance bala’I a garesu, kuma wasu Mutane daga cikin bayinsa ya jarabce su da wahalhalu kala-kala sai suka yi hakuri bisa wannan Musaba ,daga karshe hakurinsu bisa wannan musiba ta kasance  Ni’ima a garesu).masu saurare hakika godiyar ni’imar Allah madaukakin sarki ga dukkanin ma’anarta sanadiyar isa ne zuwa ga samun albarkatun ni’imar kamar yadda raina ni’ima ko kuma kin godiya ga ni’imar Allah ya kan zamanto sanadin ukubar duniya tun kafin aje Lahirar ma,a cikin littafin Amaly na shek tusy an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah (s.a.w) na cewa:(zunubai kala uku a kan gaggauta ukubar su a nan duniya tun kafin aje lahira, na farko sabawa iyaye, na biyu zalunci da kuma cutar da Mutane, sai kuma na ukun su butulcewa ihsani ko kuma kautatawa) Har ila yau a cikin littafin Amaly na shek Tusy an ruwaito hadisi daga Imam Aliyu bn Husain Zainul abidin (a.s) yayin da yake wasaici ga dansa yana mai cewa:(ya kai dana ga godewa wanda ya kautata maku, ka kautatawa wanda ya gode maka,har abada  ni’ima ba za ta kushewa ba wanda yake godiya ga wanda ya kautata masa, kuma ni’ima ba za ta dore ba ga wanda ba ya godiya ko kuma ya kafircewa wanda ya kautata masa, mai godiya da godiyarsa Allah madaukakin sarki zai kara masa daukaka da kuma ni’imar da ta wajabci godiya sannan ya karanto wannan Aya mai albarka   :(kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar cewa: Lallai idan kuka gode wa (Ni’imata )ba shakka zan kara muku, idan kuwa kuka butulce, to hakika azabata mai tsanani ce.) suratu Ibrahim Aya ta 7. Da fatan Allah madaukakin sarki ya arzitamu da wannan dabi’a kyakkyawa mu zamanto masu godiyar Allah madaukakin sarki ga dukkanin ni’imar da ya hore mana ta hanyar godewa bayinsa da ya sanya ta hanyarsu ne Allah ya arzita da ni’imarsa . **************************Musuc*************************** Masu saurare a nan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Injeniyarmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya ni ke muku fatan alheri wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.
Monday, 29 June 2015 07:13

Shiri Na 36

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan kyautatawa wanda ya kyautata, ma’ana sakawa wanda ya kyautata maka da mafi kyakkyawan sakamako,amma kafin mu shiga shirin ga wannan. ************************Musuc************************** Masu saurare shirin na yau zai fara da Aya ta 60 cikin suratu Rahaman inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Ba Wani abu ne sakamakon kyakkyawa ba sai kyakkyawa), an ruwaito hadisi daga Hafiz Aljalil Husain bn Sa’ed cikin littafin Azuhud, ya ce an tambayi Imam Sadik (a.s) kan fadar Allah madaukakin sarki  (Ba Wani abu ne sakamakon kyakkyawa ba sai kyakkyawa) sai Imam (a.s) ya ce wannan Aya a kan iya zartar da ita kan mumuni da kafiri,mutuman kirki da fajiri, duk wanda ya yi abin kirki ko kuma kyakkyawan abu to shima a saka masa da kyakkyawa, sakamaka da kyakkyawa ba shi ba  ne a yi masa makamanci abin ya aikata  a’a, sai a diba abinda ya fi a sakama masa da shi).masu saurare wannan hadisi shaida ne bisa kyakkyawan sakamako ga wanda ya kyautata, mumuni ne ko kafiri, mutuman kirki ne ko fajiri ne ,kuma sakamakon ya kasance ya fi wanda yayi da farko, to amma ta yaya mutuman da ba shi, zai iya sakawa wanda ya kyautata masa?amsar wannan tambaya ita ce riwayar da aka ruwaito a cikin Littafin Zuhud daga shugaban halittu Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda ya ce:(duk wanda ya tambayeku saboda Allah ku bashi,kuma duk wanda ya kyautata maku  to ku saka masa da kyakkyawa, idan kuma ba ku da abinda za ku saka masa to ku roka masa Allah madaukakin sarki har sai kun ji cewa kun saka masa da mafi kyakkyawan alherin da ya yi maku).amsar wannan tambaya kamar yadda wannan hadisi ya yi ishaka shine yawaita addu’ar alheri ga wanda ya kyautata maka shine sakamakon mafi alheri ga wanda ya kyautata maka matukar dai ba ka da abinda zaka iya saka masa da shi ,a wata riwayar kuwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa daga cikin hanyoyin sakawa wanda ya kyautata maka shine gode masa da kuma ambatonsa da alheri, kamar yadda aka ruwaito cikin littafin Azuhud daga Husaini bn Sa’ed ya ce ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (ya isar maka yi wa dan uwanka addu’a da kuma ambatonsa da  alheri idan ya yi maka alherin, kamar ka ce Allah ya saka masa da alheri, idan kuma an ambace a guri baya nan sai ka ce Allah ya sakama da alheri, idan ka aikata haka, ya isar maka a matsayin kyakkyawan sakamako bisa alherin da ya yi maka).a cikin Littafin Amaly na shek tusy an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) na cewa:(hakin wanda ya kyautatawa mumuni ya saka masa da mafi alheri,to idan ya kasa da haka, wajibi ya kyautata masa ta hanyar ambato irin ni’ima da kuma soyayyar da ya gwada masa, idan ya kuma kasa da hakan to lallai shi ba irin mutanan da ya  kamata a kyautata masa ba ne).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon godiya ga wanda ya kyautata mana musaman ma ga shugaban ni’ima da kyauta, shugaban halittu baki daya. ****************************Musuc******************* Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai yi bayyani ne kan yin mu’amalar da ta dace ga hallitun Allah madaukakin sarki.a cikin littafin Musadikatul Ikhwan na shek Saduk(k,s) an  ruwaito hadisi daga imam sadik (a.s) na cewa:(ka dubi abinda ka samu daga cikin dukiyar ka sai ka bayar da shi ga ‘yan uwanka domin Allah madaukakin sarki na cewa(hakika kyakkyawa ya na kore mumuna)sannan ya ci gaba da cewa ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce abu uku ba za ya jure wa wannan al’umma ba, na farko mu’amala ta hanya da ya da ce cikin  dukiyar su, yi wa kansu adalci wajen mu’amala da mutane, sai kuma ambaton Allah madaukakin sarki cikin ko wani hali, ba ambaton Allah ba kawai a harshe,duk lokacin da wani abu na sabon Allah ya tunkaresu su kauce masa su ce mu muna tsoron Allah ubangijin talikai).masu saurare mu’amala da mutnae ta hanyar da ya dace na daga cikin kyawawen aiyukan da suke kawar da munana kuma na daga cikin hanyar tsarkaka daga aiyuka munana, kamar yadda yake daga cikin alamomin gasganta Imani, a cikin littafin khisal an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa(duk wanda yayi mu’amalar da ta dace da wanda baya da shi, ma’ana duk wanda ya taimakawa fakiri daga cikin dukiyarsa kuma ya daidata mutane da kansa wannan shine hakikanin mumuni).har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) na cewa:(amiru mumunin (a.s) ya kasance ya na cewa mu iyalan gidan Ma’aikin Allah (s.a.w) an umarce mu da mu ciyar da abinci, mu tabbatar da wakilci a cikin mutane, mu kuma yi sallah yayin da mutane ya kwana).har ila yau a cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga imam sadik (a.s)na cewa:(hakki ne ga musulmi su yi kokari wajen taimakawa masu rauni daga cikinsu, su yi kyakkyawar mu’amala da kuma taimako, su taimakawa mabukata kuma su tausaya masu, sai su kasance bisa umarnin Allah madaukakin sarki na cewa, masu tausayi a tsakaninsu) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon taimako da kuma kyakkyawar mu’amala tare da bayin Allah baki daya. *******************************Musuc*********************** Masu saurare,a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injeniyamu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar ni ke muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatu llahi wa barkatuhu.    
Monday, 29 June 2015 07:12

Shiri Na 35

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan soyyaya da juna a tsakanin Mutane  , amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. ***************************Musuc************************* Masu saurare, daga cikin kyawawen dabi’un musulinci da Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa,shine sun nunuwa junana soyayya da kauna wanda hakan shi ke nuna falala, karamci, rahama da kuma son gafara a garesu, hakika hadisai da dama sun yi bayin Allah  wasaicin da nunawa juna soyayya a tsakaninsu, kamar yadda aka ruwaito a cikin Littafin Kafi daga shugabanmu Babban Ja’afar Imam Bakir (a.s) ya ce:(hakika wani balaraban kauye daga kabilar Bani Tamim ya je wajen ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce masa Ya Ma’aikin Allah yi mini galgadi, daga cikin irin galgadin da ya yi masa ya ce mas aka so Mutane sai su ma Mutanan zai su so ka). Masu saurare wanzuwar soyayya a tsakanin Mutane wata ibada ce da mumuni yake dabi’antuwa da ita domin samun kusanci zuwa ga Allah madaukakin sarki,kamar yadda ta ke hanya ce ta samun soyayya a tsakanin halittu, kuma wannan shi ke kare su da cutuwa domin haka ne wani hadisi ke bayyani sa a matsayin rabin hankali,Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(wanzuwar soyayya da kuma goda soyayya ga mutane rabin hankali ne).a cikin Littafin kafi na sikkatu islam kulaini an ruwaito  hadisi daga Imam Kazim (a.s) ya ce (bayanna soyayya ga Mutane rabin hankali ne, tausayi kwa rabin rayuwa ce).har ila yau a cikin wata riyawa kwa Imam Hasan Mujtaba (a.s):(kusanci shine kusancin soyayya ko da kwa dan uwantaka na tsakaninku ya nada nisa, nisanci shine wanda ya nisanta daga soyayya ko da a kwa dan uwantaka dake tsakaninku ta kusa ce sosai).kamar yadda Ma’aikin Allah (S.A.W) ya shiryar da mu yadda Mutane ya kamata su bayyana Soyayya tsakaninsu a aikace, a cikin riwayar da Imam Sadik (a.s) ya ruwaito a cikin Littafin Kafi ya ce Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ababe uku ne ke kwada soyayyar musulmi a kan dan uwansa musulmi, na farko, ya tarbe shi da milmishi, ya giramashi wajen wanzar  masa da guri a yayin da suka zauna tare, sai kuma na uku ya kira shi da sunan da fi so).har ila yau a cikin wata riwayar Imam Sadik (a.s)ya ce:(idan kana son dan uwanka to ka sanar da shi, domin Annabi Ibrahim (a.s)ya ce:(Ya tuna lokacin da Ibrahimu ya ce:Ya Ubangijina ka nuna mini yadda kake raya matattu, (sai Allah) Ya ce :shin ko ba ka ba da gaskiya ba ne? sai Ya ce A’a bah aka ba ne,don dai raina ya kwanta kawai..)sai Imam (a.s) ya ce idan kana son Mutune to bayyana masa soyayyarka domin hakan shi zai tabbatar da soyayyar dake tsakaninku).masu saurare,Kyautatawa,alheri,kyakkyawar mu’amala , kaucewa cutarwa, giramamawa,Afuwa ga kurakure da makamantansu na daga cikin misdakin bayyana Mutune irin son da ake yi masa kamar yadda wadannan riwayoyi da ma makamantansu suka bayyana mana. ***********************Musuc********************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai yi bayyani ne dangane da kyawawen wasani gami da zolaya a tsakanin Al’umma,a cikin littafin Yunus Shaibani an ruwaito hadisi daga Imam Ja’afaru Sadik(a.s) na cewa:(shin ba ku zolayar junanku ne, hakika zolaya na daga cikin kyawawen dabi’u, domin za ka sanya farinciki a zuciyar dan uwanka, kuma hakika Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yak an zolayi mutune idan ya na so ya sanya shi  dariya). Imam Bakir (a.s) ya ce:(hakika Allah madaukakin sarki ya na son mai baiwa al’ummar dariya ba tare da aibata wani ba). A cikin littafin Kafi sikatu Islam kulaini ya ruwaito hadisi daga Mu’amar bn Khalad ya ce (na tambayi Babban Hasan (a.s) dangane da mutumane da yake yin abuban ban dariya cikin al’umma tare da zolaya wanda hakan yak an sanya su dariya sai Imam (a.s) ya ce babu laifi matukar babu alfasha ko kuma aibanta wani ba domin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan balaraban kauye ya kawo masa kauta, sai ya ce masa to ya bashi biyan kautar da ya kawo masa sai ya yi dariya, idan an sha kwanaki sai ma’aikin Allah ya tuna da abinda wannan balaraben kauyen ya ce sai ya ce ina ma balaraben kauyen nan ya zo mana).masu saurare, zolaya ko kuma wasan da babu cin tsarfi, fallasa ku kuma aibata juna shine wasan da musulinci ya amince da shi.an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:(babu wani mumuni da ba ya wasa da dan uwansa). Har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Kazim (a.s)na cewa :(Annabawan Allah madaukakin sarki da wasiyansu sun kasance suna wassani tare da baiwa juna dariya da sahabansu).bayan haka masu saurare wani irin wassani ko zolaye ne addinin musulinci ya hana ? sai a tarbemu a maku na naga domin jin irin hadisin za mu karanto mu ku dangane da wannan maudu’i.   **********************Musuc************************* Masu saurare, a nan za mu dasa aya ganin lakacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka tallafawa shiri, musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu
Monday, 29 June 2015 07:12

Shiri Na 34

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, shirin na yau zai yi bayyani ne dangane da girmama dattijain mumunai  da kuma irin falalar da Allah madaukakin sarki ya yiwa masu irin wadannan kyawawen dabi’u, amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai. ***********************Musuc**************************** Hakika masu saurare daga cikin kyawawen dabi’un musulmi da Allah madaukakin ya fi so ga bayinsa a kwai girama dattijain mumunai kuma hadisai da dama sun bayyana shi a matsayin misdakin karamci da kuma kirmamawa Allah madaukakin sarki, hakika  a cikin littafin Sawabul a’amal na shek Saduk (k.s) an  ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(daga cikin girmama Allah madaukakin sarki, karamma dattijo mumuni), hadisai da dama sun yi bayyanin falalar girmama datijawan mumunai tare da bayyana shi a matsayin garkuwa mumuni daga tashin hankali da wahalhalu na ranar Alkiyama, a cikin litattafan sawabul a’amal da Kafi an ruwaito hadisi daga shugaban hallitu mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda ya son falalar dattijo mai yawan shekaru ya kuma kirmama shi a matsayinsa na dattijo Allah madaukakin sarki zai amintar da shi daga tsoron ranar Alkiyama). Wasu hadisan kwa sun bayyana cewa girmama masu yawan shekaru na mumunai  na daga cikin kyawawen dabi’un da suke tsarkake mutune daga daudar nifaki, kamar shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya fada a riwayar da aka ruwaito a cikin littafin Kafi na sikatu islam kulaini: (ababe guda uku babu wanda zai jahilci hakokinsu sai munafiki wanda yayi fice a nifaki, na farko hakin mai yawan shekaru ko kuma dattijo a cikin addinin islama, na biyu hakin hafizin Alkur’ani mai tsarki, na uku kuwa hakin shugaba adili).har ila yau a cikin wata raiwayar kwa Imam Sadik (a.s) ya ce sanin hakin dattijo da kuma kirmama shi ya kan zamanto sanadiyar sassauci na dan adam wahalhalu a lokacin da shi kansa bawa ya samu yawan shekarun wato a yayin da ya tsufa. A cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:(ya na daga cikin girmama Allah, girmama mumuni mai yawan shekaru, duk wanda ya girama mumuni to hakika ya sani ya fara ne da girmama Allah madaukakin sarki, kuma duk wanda ya tausayawa mumuni mai yawan shekaru, ba shakka Allah madaukakin sarki zai aiko wanda zai kirmama shi kafin mutuwarsa).da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu iko gudanar da wannan dabi’ar kyakkyawa saboda darajar shugaban hallitu Muhamad dan Abdullah da iyalan gidansa tsarkaka. ******************Musuc************************* Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,masu saurare tausayi da girmama mumunai kanana daga cikin ko manya, masu yawan shekaru ko dattijai na daga cikin kyawawen dabi’un musulnci kuma rikon sakainar kashe da wannan dabi’a bay a daga cikin dabi’un manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka kamar yadda aka ruwaito daga shugabanmu Imam Sadik (a.s): (bay a daga cikinmu wanda baya girmama manyanmu kuma ba ya tausayin kananamu). A wata riwauar kwa Imam (a.s)ya ce:(, ku sada zumunci ga makusantanku, ku kuma girmama manyanku da na gaba da ku domin babu wani abu da za ku iya masu face kiyaye zutar da su).masu saurare hakika daga cikin kyawawen dabi’un musulmi a kwai girmama nag aba da kuma dattijan mumunai wanda hakan kan sanya mutune tsarkaka daga duk wani jiji da kai gami da alfahari,A cikin  littafin Ma’anil Akhbar an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa :(duk wanda bai san falalar wani ba hakika shi mai jiji da kai ne kuma ya tabbata ya nada girman kai kuma hakan shi ke nuna cewa ya yaudari kansa da kansa), a cikin littafin minazul hikma na Ayyatullahi Muhamad Ray Shahri an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(hakika duk wanda ya girmama dattijo daga cikin Al’ummata kamar ya girmama ni ne). Daga karshe masu saurare bar i mu karanto muku wani bangare daga hakin dattijai wanda aka ruwaito a cikin Littafin Risalatul Hukuk na Imam Zainul Abidin (a.s) (ka sani hakin babba a kanka, ka girmama shi saboda wajen shekarunsa kuma ka girmama musulincinsa idan ya kasance daga ma’abota falala a musulinci wajen gabatar da shi a kan abinda ya shafi addini, kadda kuma ka shiga gabansa a yayin da kuke tafiya  kadda ka ki saurarensa , ko da shi ya ya ki saurarenka sai ka dake, ka yi hakuri kuma ka kirmama shi saboda hakin musulinci da shekarunsa hakika hakin shekaru na makamancin hakin Musulunci). *********************Musuc************************** Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a Maku na daga za a jimu dauke da ci gaban shirin ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri,wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.    
Monday, 29 June 2015 07:11

Shiri Na 33

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi, a shirin da ya gabata munyi bayyani kan mahimancin kyakyawar abotaka da mu’amala tare da Mutane, a shirin na yau kwa za mu yi bayyani ne kan falalar amincewa ko kuma karbar Nasihar dan uwa musulmi ko mumuni, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan. ***********************Musuc**************************** Masu saurare hakika kur’ani mai tsarki ya umarce mu da yin Nasiha da kuma karbarta daga wajen mutanan da suka dace, ayoyi da dama sun shiryer da mu bisa wannan kyakkyawar dabi’a, za mu takaitu da Aya guda wacce take bayyana mumunan sakamako ga wadanda suka kauracewa karbar Nasiha, a cikin suratu Bakara Aya ta 206 Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan kuwa aka ce da shi ka ji tsoron Allah sai girman kai ya hau kansa saboda sabon (da aka hana shi yi)to jahannama ta ishe shi makwanta,kai lallai makwantar kuwa ta munana). Hakika masu saurare babban abinda yake janyo kin karbar Nasiha shine girman kai, bautar zuciya da kuma son rai, duk wanda ya kasance ya dabi’anto da sauraren nasiha ba shakka zai rubanto da wata falala ta daban, falalar kuwa ita ce tsarkakar zuciya daga girman kai da kuma rage aikata sabo ,da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon sauraren nasiha daga wajen mutanan da suka dace.hadisai da dama sun kwadaitar da mu wajen saurare da kuma karbar Nasiha kuma sun bayyana cewa wannan kyakkyawar dabi’a na daga cikin ni’imar da Allah madaukakin sarki ya horewa bayinsa salihai, hakika  a cikin littafin Assara’ir na Allama bn Idris Alhilly an ruwaito hadisi daga Ayub bn Nuh ya ce  hakika Imam Ali Alhadi (a.s) ya rubuta wasika zuwa daya daga cikin mabiyansa yana mai cewa:(ka tunatar da wani, duk wanda Allah madaukakin sarki ya nufe sa da Alheri sai ya bashi damar saurare da kuma karbar Nasihar ‘yan uwansa mumunai ko musulmai).a cikin litattafan Kafi , Almahasin da kuma Attahzib  an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce (ka bi mutuman dake sanya ka kuka a yayin da yake yi maka Nasiha, kadda kabi mutuman dake sanya ka dariya a yayin da yake yaurarka, kuma baki dayanku za ku koma zuwa ga Allah madaukakin sarki sannan ya sanar da ku abinda kuka kasance kuna aikatawa). ******************Musuc********************************* Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Nasihar shugabanmu Imam Aliyu bn Husain Zainul Abidin (a.s), a cikin littafin Amaly na sheik Tusy (K,S) an ruwaito hadisi daga shugabanmu Zainu Abidin (a.s) yayin da ya ke yiwa dan Dansa Nasiha yana mai cewa:(Ya Kai Dana ka kiyayi abotaka da wawa,domin Shi Wawa, idan ya aikata wani abu zai bata shi, ba ya wani aiki na kashin kansa wanda zai wadatar da shi, kuma ilimin waninsa ba ya amfanar da shi,sannan ba ya biyayya ga mai yi masa Nasiha). Masu saurare shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana cewa karbar Nasiha na daga cikin dabi'un da mumuni ba ya wadatuwa da shi matukar ya na bukatar kyakkyawar rayuwa, a cikin littafin Almahasin na sheik Ahmad Barki an ruwaito hadisi dag Imam Sadik(a.s) na cewa:(hakika mumuni ba ya wadatuwa daga wadannan ababe guda uku, na farko,taufiki ko kuma dace daga Allah  madaukakin sarki, na biyu ya kasance mai yiwa kansa Nasiha, na uku kuma amincewa ko kuma karbar Nasiha daga wanda yayi masa Nasiha). Har ila yau shugaban Imam Sadik(a.s) ya bayyana karamar Nasihar ga dan uwa, a cikin littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa: ( wanda na fi so daga cikin 'yan uwa ne shine wanda ya yi mini kyauta da bayyana mini aibi na ko kuma ababen da nuke yi marassa kyau ) a wani hadisin kuwa ya na cewa wanda ya tuna tar da ni bisa wata barna da ya ga zan aikata ko kuma na aikata domin in gyra). A wani bangare kuwa Alkur'ani mai tsarki na umartar mu da muka sance masu yi umarni da alheri  kuma masu hani da abun ki, a cikin Suratu Ali Imran Aya ta 104, Allah madaukakin sarki ya ce:(Lallai ne wata Al'umma ta kasance daga cikinku (wadanda)za su rika kira zuwa ga alheri, kuma su rika umarni da aikata abin kirki, su rika kuma hani ga mumunan aiki.wadancan kuwa sune masu samun babban rabo) A wani bangare kuwa Alkur'anin ya umarce da kadda mu manta kawunanmu wajen aikata alheri kadda mu zamanto masu yin Nasiha sannan mu kuma muna aikata sabanin hakan, a cikin Suratu bakara Aya ta 44 Allah madaukakin sarki ya ce:(Yanzu kwa rika umartar Mutane da kyakkyawan aiyuka kuna kuma mantawa da kanku, alhali kuwa ku kuna karanta littafin (Attaura)? Yanzu ba za ku hankalta ba?). **********************Musuc************************* Masu saurare, a nan za mu dasa aya ganin lakacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka tallafawa shiri, musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.       
Monday, 29 June 2015 07:10

Shiri Na 32

Written by
Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci wanda sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai yi bayyani kan kyakyawar abotaka da mu’amala tare da Mutane , amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai. ******************Musuc********************************* masu saurare hakika ayoyi da daman a cikin Alkur’ani mai tsarki su yi  umarni da kyakyawar mu’amala da bangarori na Mutane daban-daban makusanta ne ko kuma  wadanda babu alakar jini a tsakaninmu da su, kamar yadda aka umarce mu da yin biyayya ga ma’aifa da kuma kyakkyawar mu’amala da iyalanmu. Hadisai da dama sun umarcemu da riko da kyawawen dabi’u wadanda suke gina kyakyawar alaka ta yau da kulun tare da Al’umma wacce ta ginu bisa soyayya da girmama juna a tsakanin Al’umma. A cikin littafin Nahjul Balaga, shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya bayyana sakamakon kyakyawar mu’amala tare da Al’umma:( Mu’amalarku da mutane ta kasance idan kun koma ga Allah, Al’ummar za ta yi kukan rashin ku, idan kuma kuna raye za a dinke koyi da ku). Har ila yau a cikin littatafan , Almahasin da Man La yahdurul fakih an ruwaito hadisi daga Imam Sadik(a.s) ya ce:(Ya Ku mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka, ku sani cewa ba ya daga cikinmu wanda ba ya mallakar kansansa a yayin da yayi fishi, da kuma wanda bai yi kyakkyawar abotaka ba da abokaninsa da kuma wanda yayi mumunar mu’amala da abokanin zamansa). Kyakkyawar mu’amala hanya ce ta shiga cikin karamar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka kuma hanya ce ta shiga cikin karamar Allah madaukakin sarki kamar yadda shugabanmu Iman Bakir (a.s) ya yi ishara da shi, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Bakir(a.s) na cewa:(babu ruwan Allah ga wanda ya kama wannan hanya,(wato hanyar zuwa aikin hajji) matukar ba yanada wadannan ababe guda uku ba, na farko tsantseni wanda zai hana shi sabon Allah,na biyu hakurin da zai sanya ya mallaki kansa yayin da rai ya bace, sai kuma na uku kyakkyawar abotaka da kyakkyawar kuma mu’amala da Mutane) Imam Bakir (a.s) na cewa duk wanda ba shi da wadannan sifoffi guda uku to  bai hallita ba ma ya kama hanya zuwa aikin hajji ba har sai ya gyara halayansa. ***********************Musuc*************************** Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hakika ko wani mumuni ana bukatar ya dabi’antu da irin wadannan kyawawen dabi’u, ya zamanto mai hakuri, mai tsantseni da kuma kyakkyawar abotaka tare da ko wani mutune , abokin tafiya ne a ko kuma abokin mu’amala ne na yau da kulun, tare da iyalan ne ko kuma abokanai ne na aiki ko kuma makobtane ne nay au da kulun da sauransu,a cikin littatafen Kafi da Almahasin an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa:(ka kasance mai kyakkayawar mu’amala tare da wanda ka ke tare da su, ka kiyaye firta kalaman da za su cutar da abokinka ko kuma wanda ka ke tare da su, ka kasance mai hadiye fishi yayin da rai ya bace , ka rake yawan wassani da zolaya wanda hakan na iya batawa abokinka rai, ka zamanto mai shunfuda afuwa da yafiya a ko wani lokaci……..) Daga cikin misdakin kyakkyawar abotaka ka kasance mai taimako da abin hanunka daidai gwalgwado, imam Bakir (a.s) ya ce (duk mutuman da ke  abotaka da shi, kuma idan har za ka iya ya kasance hanunka ne kulun a sama wato kai ne mai bayarwa ko kuma mai taimaka ma sa ,to ka bayar ko kuma ka taimakama sa).maluman hadisi sun yi ta’aliki dangane da wannan hadisi sun ce idan kuna abotaka da mutune to ka zamanto a wani lokaci ka shiga gabansa wajen yi masa karamci, kautatawa, da kuma kokarin shafe masa hawaye duk lokacin da hajar hakan ta taso a cikin ko wani yanayi  da makamantansu. Har ila yau daga cikin misdakin kyakkyawar abotaka,boye sirrin aboki da kuma aibinsa,yafemasa a bisa kurakuran da yai maka, kiyaye abinda zai cutar da shi, da kuma giramama shi, Imam Bakir (a.s) ya ce:(ku giramama abokaninku,ku boye sirrinsu kadda ku cutar da junanku kada ku kasance masu hassadar junanku,ina galgadinku da ku kiyayi rowa kuma ku zamanto bayin Allah muhklisai) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzitamu da kyakkyawar mu’amala tare da abokane da ma mutane baki daya da kuma samun kusanci a gareshi don albarkar Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka. ******************Musuc************************** Masu saurare, a nan za mu dasa aya ganin lakacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka tallafawa shiri, musaman ma Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.    
Page 1 of 3