An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 24 February 2016 17:24

Ko Kun San Na (345) 09 Ga Watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia.

Ko Kun San Na (345) 09 Ga Watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia.
Yau Lahadi 09 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia. Wacce Ta yi dai dai da 19 Jamada -Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamarai. Har'ila Yau Wacce ta yai dai dai da 28 Febrerun Shekara Ta 2016 Miladia.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru da suka 526 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19 ga watan Jamada Ula-911Hijira kamaria. Abul-Fadle Abdurrahaman bin Suyudi wanda ake wa lakabi da Jalaluddeen, malamin fikihu da tafsiri ya rasu a birnin alkahira na kasar Masar. An haifi suyudi a shekara ta 849 hijira kamaria. sannan ya fara karatu tun yana matsahi sannan ya haddace alqur'ani tun yana matashi. Bayan haka ya shiga karatun ilmin tafsiri hadisi da ilmin qur'ani. Bayan kammala karatu ya fara karantarwa da kuma wallafa littafai. Malaman tarihi sun ce yawan littafan da jalaludden suyudi ya rubuta sun kai 300-500. Daga cikin su akwai «الکتاب الکبیر» و «تاریخ الخلفاء» .

02- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28 ga watan Febrerun -1991. Aka dakatar da bude wuta tsakanin sojojin kawance da kuma sojojin kasar Iraqi a yakin tekun farisa na daya. Shugaban kasar Amurka na lokacin Goege W Bush da kawayensa ne suka fara yakin a cikin watan Febrerun shekara 1991 bayan da Sadam Husain na kasar Iraki ya tura sojojinsa suka mamaye kasar Kuwai. A yakin dai sojoji kawance sun tialstawa sojojin sadam fita daga kasar Iraqi da kuma yarda da kudurorin majalisar dinkindu guda 7 wadanda suka takurawa mutanen kasar. Bayan haka kasashen Amurka da Britania sun kifar da gwamnatin sadan a shekara ta 2003 da suna neman makaman kare dangi. Wadanda basu same su ba bayan mamayar da kuma kifar da gwamnatin sadan.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 100 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28 Febrerun- 1916M. Henry James wani marubuci dan kasar dan kasar ya rasu a birnin newyork. An haife shi a birnin Newyork din a shekara 1843. Iyayensa sun yi hijira ne zuwa kasar Amurka daga kasar Island. Bayan kammala karatunsa na jami'a ya koma kasar Britania da zama inda ya ci gaba da rubuce rubuce. Fitattu daga cikin rubutunsa sun hada da "Jakadu" Benen hakoran giwa.

Add comment


Security code
Refresh