An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 04 September 2015 06:54

Ranar Yaki Da Ta'addanci A Iran

Ranar Yaki Da Ta'addanci A Iran
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da kua  cikin wannan shiri na Iran a Mako, shirin da kan yi dubi a kan wasu daga cikin muhimamn lamurra da suka wakana a Iran a cikin mako, daga cikin abubuwan da shirin zai yi dubi a kansu a yau har da batun ganawar da jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya yi da manyan kwamndojin sojin kasar masu kula da bangaren tsaron sararin samaniyar kasar, da taron ranar yaki da ta’addanci ta kasa a Iran, sai kuma batun ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya kai a kasashen Tunisia da Aljeriya, sai kuma batun kaddamar da sabon fim din nan na Muhammadu Rasulluh wanda Majid Majidi ya shirya, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu. ……………………………………….

 

A ranar Talatar da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da kara kaimi a dukkanin fuskoki na tsaro, musamman ta fuskar tsaron sararin samaniyarta.

Jagoran wanda shi ne babban kwandan askarawan kasar ta Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manyan kwamandojin sojin kasar masu kula da ayyukan tsaron sararin samaniyar kasar, inda ya jaddada musu cewa, duk da irin ci gaban da Iran ta samu a wanann bangare, amma za ta ci gaba da rubunya kokari ta wannan fuska, musamman ma idan aka yi la’akari da irin kalu bale da kuma barazanar da take fuskanta a kowane lokaci daga makiya.

A nasa bangaren babban kwamandan rundunar Khatamul Anbiya Brigadier Janar Farzad Isma’ili ya bayyana cewa, a kowan lokaci za su ci gaba da zama cikin shirin domin yin amfani da dukaknin karfin da Allah yah ore musu domin kare kasarsu da al’ummarsu daga duk wata barazana daga makiya.

Wannan ganawa ta zo ne bayan da rundunar sojin Iran ta yi gwajin wasu sabbin na'urori na radar da ma'aikatar tsaron kasar ta kera, wadanda ke tantance duk wani abu da ke shawagi a cikin sararin samaniyar kasar, da nufin kara karfin tsaron sararin samaniya daga duk wata barazana daga makiyan kasar.

……………………………………

A cikin wannan mako ne aka gudanar da wani taro na tunawa da cika shekaru 34 da kisan gillar da kungiyar ‘yan ta’adda ta MKO ta yi wa shugaban kasar Iran na lokacin Ali Raja’i da kuma Firayi ministansa Muhammad Jawad Bahonar a ranar 30 ga watan Agustan 1981, wadnada suka yi shahada sakamakon saka musu bama-bamai da kungiyar ta yi shekaru 34 da suka gabata.

Kungiyar MKO wadda kasashen yammacin turai suke daukar nauyinta kai tsaye domin gudanar da ayyukanta na ta’addanci a cikin Jamhuriyar Muslunci ta Iran, musamman ma kisan manyan malamai da jami’ai, kafin kisan shugaban kasa Ali Raja’i da Muhammad Bahonar, kungiyar ta kashe wasu manyan jami’ai 72 a lokaci guda a lokacin da ta tayar da bama-bamai a cikin majalisar dokokin Iran a birnin Tehran a ranar 28 ga watan Yunin 1981, inda alkalin alkalan jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma wasu daga manyan jami’ai da suka hada da ‘yan majalisar dokoki suka yi shahada, bayan nan kuma ta kashe dubban fararen hula a cikin kasar ta hanyar kisan gilla da bindiga da kuma tayar da bama-bamai.

Kasashen yamamcin turai sun yi amfani da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Iraki a lokacin Saddam Hussai wajen yin amfani da wannan kungiyar domin gudanar da irin wadannan ayyuka na ta’addanci, inda Amurka da Isra’ila da ma wasu kasashen yammacin turai musamman ma Birtaniya da Faransa, suka taimaka ma Saddam Hussai wajen kafa sansanin Ashrafiyyaha kasar Iraki domin mayar da shi sansanin mayakan kungiyar ‘yan ta’addan MKO.

Kamar yadda kuma suka yi amfani da wasu daga cikin kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya wajen aiwatar da wanann manufa, ta hanyar baiwa kungiyar muggan makamai da kudade da kuma horar da mayakanta a cikin kasar Iraki domin rusa kasar ta Iran.

…………………………….

A lokacin gudanar da babban taron na ranar yaki da ta’addanci a Iran, manyan jami’ai sun gudanar da jawabai a wurin, daga ciki kuwa har da shugaba Hassan Rauhani, wanda ya bayyana cewa tun kafin wannan lokaci da duniya ta mayar da hankali kan batun yaki da ta’addanci, Iran tana yaki da ta’addanci, domin kuwa Iran ta fara hakan ne tun bayan juyin juya halin muslunci, inda kungiyar MKO ta zama babban misalign hakan tun shekaru 35 da suka gabata a Iran.

Shugaba Rauhani ya ce a halin yanzu kasashen duniya suna fama da wata matsalar ta bullar wasu kungiyoyin na ta’addanci da suka addabi al’umma baki daya, da suka hada da su IS, Alkaida, Taliban, Boko Haram da sauransu, ya ce mai yiwuwa abin da irin wadannan kungiyoyin ta’addanci suke yi ya zama sabon abu ga al’ummomin duniya, amma ba bako abu ne ba ga al’ummar Iran, domin kuwa sun saba ganin munanan ayyuka na ta’addanci a daga kungiyar MKO.

Ya ce wadannan kungiyo  ba su da wata alaka da wani addini ko wata akida, balantana akidar jihadi a cikin muslunci, wanda ta ginu a kan  kaidoji da sharudda.

Rauhani ya ce ta yaya wasu kasashe za su hadu su ce suna yaki da ta’addanci alhali su ne suke da hannu wajen samar da wadannan yan ta’addan? Haka nan kuma ya yi kakkausar suka dangane da yadda majalisar dinkin duniya take nuna halin ko in kulak an lamurra da dama da ya kamata ta taka rawa a kansu, musamman ma batun ta’addanci da cin zalun a kan al’ummomin yankin gabas ta tsakiya, wanda ya ce Isra’ila tana yin kisan kiyashi kan al’ummar palastinawa wanda hakan shi ne ta’addanci mafi muni da yankin gabas ta tsakiya ya fara shedawa, amma har yanzu majalisar dinkin duniya ta kasa tabuka komai domin kare hakkokin palastinawa.

Daga karshe shugaba Rauhani ya kirayi kasashen yankin gabas ta tsakiya da cewa da su daina yaudarar kansu kan batun yaki da ta’addanci, domin kuwa an san su wanen ne wadanda ‘yan ta’adda, kuma na san kasashen da suke daukar nauyinsu da makamai da kudade da kuma tunzura su da fatawowi na kafirta musulmi, wanda kuma suna amfani da hakan wajen aitar da ta’addancinsu kan al’ummomi na gabas ta tsakiya da ma wasu kasashen duniya da sunan suna jihadi bisa fatawoyin da malaman wasu kasashen larabawan yankin suke ba su.

…………………………………………………….

A cikin wannan mako ne ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya ziyarci wasu daga cikin kasashen larabawan yankin arewacin Afirka, da suka hada da Tunisia da kuma Aljeria, inda ya gana da manyan jami’an wadannan kasashe kan batutuwa da suke da alaka tsakanin kasashensu da kuma jamhuriyar muslunci ta Iran, musamman a bangarori na tattalin arziki, siyasa da kuma yaki da ta’addanci.

Zarif ya fadi a birnin Algiers cewa kasashen yankin za su iya yin aiki kafada da kafada wajen tababtar da tsaro da kuma dawo da zaman lafiya a kasashen da aka haifar da rikici da tashin hankali, musamamn ma a kasashen Iraki, Syria da kuma Yemen, ya ce Iran za ta hada karfi da kasashen yankin domin tabbatar da cewa an cimma wannan buri wanda zai amfani kowa.

Music……………………………………

A cikin wannan mako ne aka kaddamar da fin din nan na Muhammad Rasulullah (SAW) a birnin Tehran, wanda ya kunshi tarihin manzon  Allah (SAW) da kuma irin gwagwarmayar da ya yi wajen isar da sakon addinin muslunci gad an adam, gami da kuma darussan da ke cikin rayuwarsa mai albarka ga dukkanin musulmi da ‘yan adam baki daya, kasantuwar cewa shi manzo ne da Allah ya aiko a matsayin rahama ga talikai baki daya.

Wannan fim yana mayar da martini ne kan abubuwa na batunci da aka yi ta yi ga manzon Allah a cikin kasashen turai a cikin ‘yan shekarun nan, inda suke kokarin danganta ayyukan ta’addanci da rashin imani da su ke aikatawa da sunan addini zuwa ga manzon Allah (SAW) haka nan kuma fim din yana nuna rayuwa ta zamantakewa irin ta manzon Allah, yadda ya zauna da jama’a musulmi da wadanda ba musulmi, ta yadda wasu da dama sun musulunta ne saboda kyawawan dabiun da suka gani daga gare shi.

Majid majidi shi ne wanda ya shirya fim din tare da taimakon wasu daga cikin malamai da masana kan tarihin addinin muslunci, ma’aikatar kula da harkokin al’adun muslunci ta Iran ce ta dauki nauyin shirya fim din baki daya, inda aka kashe tsabar kudi da suka kai dalar Amurka miliyan 40 wajen shirya fin din, ta hanyar yin mfani da na’urori na zamani da kuma kyautata shi yadda zai bayar da ma’anar da ake bukata.

Music………………………………….

To jama’a masu saurare a nan muka kawo karshen shirin na wannan mako, sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani sabon shirin, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassamu alaikum wa rahmatullah.

End

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh