An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 30 May 2015 02:49

Iran A Mako 28-05-2015

Iran A Mako 28-05-2015
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi, da fatan kuna cikin koshin lafiya kuma za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman lamurran da suka farun da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau.

 

Daga cikin abubuwan da suka dau hankula cikin makon har da jawabai guda biyu masu muhimmanci da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi dangane da batun hadin kan al’ummar musulmi da kuma tattaunawar da Iran take yi da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya. Har ila yau akwai kuma ci gaba da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyan na Iran. Haka nan kuma a karshen makon ne dai aka kawo karshen gasar karatun Alkur’ani karo na 32 da aka gudanar a nan Iran. Har ila yau a cikin makon kuma jami’an sun bayyanar da matsayar Iran kan fada da kungiyar nan ta Da’esh a Iraki da Siriya. Batun kasar Yemen ma ba’a bar shi a cikin makon ba inda al’ummar Iran din suka ci gaba da nuna goyon bayansu ga al’ummar na Yemen a hare-haren wuce gona da irin da Saudiyya take kai musu. Haka nan kuma a fagen wasanni ma dai cikin makon Iran ta taka rawar a zo a gani a bangarori daban-daban.

 

Wadannan watakila da wasunsu ma suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yanzu. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

-------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin  a ranar Asabar din da ta gabata wacce ta yi daidai da ranar haihuwar mai girma Abul Fadhl al-Abbas, dan Amirul Muminin Ali (a.s) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da mahaddata da makaranta Alkur'ani mai girma da sauran mahalarta gasar karatun Alkur'ani mai girma karo na 32 da aka gudanar a birnin Tehran.

 

A jawabin da ya gabatar a wajen ganawar, Ayatullah Khamenei ya jaddada wajibcin gabatar da Alkur'ani mai girma cikin dukkanin bangarori na rayuwar daidaiku da na al'ummar musulmi a matsayin hanyar isa ga babbar manufar da suke da ita inda ya ce: Hanyar magance matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta a halin yanzu, ita ce mika wuya ga umurni da koyarwar Alkur'ani mai girma, bugu da kari kan rashin mika kai ga abubuwan da ma'abota sabuwar jahiliyyar duniya suka dora wa al'umma, sannan da kuma tsayin daka wajen tinkarar wannan bakar jahiliyyar.

 

Yayin da ya koma kan batun kokarin da makiya suke yi wajen rarraba kan al’umma musulmi kuwa Jagoran ya bayyana cewar duk wani bakin da ke kokarin haifar da sabani tsakanin al'ummar musulmi lalle ya zamanto mai magana da yawu kuma amsa kuwwar makiya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Haifar da sabani da sunan Shi'a da Sunna, ko Balarabe da Ba'ajame, ko kuma da sunan al'ummomi da kabilu da akidar ‘yan kasa, to kuwa hakan wani aiki ne wajen cimma manufar masu bakar aniya kan al'ummar musulmi. A saboda haka wajibi ne a yi amfani da "basira" da "azama" wajen tinkarar hakan.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana amfani da basira da kuma gano ‘masoyi' da ‘makiya' a matsayin wani lamari da ya zamanto wajibi. Jagoran ya bayyana riko da Alkur'ani a matsayin abin da zai lamunce makoma mai kyau ga al'umma da kuma tabbatar mata da sa'ada da farin ciki, don haka sai ya ce: Alhamdu lillahi a yau yunkurin kusatar Musulunci da kuma Alkur'ani mai girma ya kunno kai a cikin al'ummar musulmi wanda daya daga cikin sakamakon hakan shi ne irin wannan farkawa ta Musulunci da aka samu.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Babu yadda za a iya iya kawar da farkawa ta Musulunci ta hakika, sannan kuma tasirin hakan zai ci gaba da fadaduwa ne a kullum.

 

--------------------------------------/

 

Har ila yau kuma a ranar Larabar da ta gabata, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci bikin yaye daliban jami'ar jami'an dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da aka gudanar a jami'ar soji ta Imam Husaini (a.s) inda yayi bayani mai muhimmancin gaske dangane da tattaunawar da Iran take yi da manyan kasashen duniya.

 

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da sabbin maganganun da wasu daga cikin kasashen da Iran take tattaunawa da su kan shirin nukiliyanta suke gabatarwa da suka hada da bukatar gudanar da bincike kan cibiyoyin sojin kasar Iran da kuma tattaunawa da masanan kasar masu gudanar da ayyukansu a fagen nukiliyan, inda yace: Ko da wasa ba za a taba ba da wannan izinin ba. Sannan kuma ya kamata makiya su san cewa al'umma da jami'an kasar Iran ba za su taba yin kasa a gwiwa wajen tinkarar duk wani wuce gona da iri da kokarin nuna karfi a kansu ba.

 

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar daya daga cikin kalubalen da ke fuskantar gwamnatin Musulunci ta Iran ita ce tinkaho da karfi da son wuce gona da irin da daya bangaren da ake tattaunawa da shi din yake da shi don haka sai ya ce: Har ya zuwa yanzu makiya ba su fahimci al'umma da jami'an gwamnatin Iran ba don haka suke fadin irin wadannan maganganu na tinkaho da karfi. To amma har abada al'ummar Iran da kuma gwamnatinsu ba za su taba mika kai ga maganganun nuna karfi ba.

 

Jagoran ya bayyana cewar gwargwadon yadda aka mika wuya ga ma'abota girman kan gwargwadon yadda za su ci gaba da kokarin nuna karfin don haka sai ya ce: Wajibi a gina wata karfaffiyar katanga ta azama da dogaro da Allah da kuma jingina da karfi na kasa a gaban irin wannan kokarin nuna karfi.

 

---------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda watakila kuka ji a farkon shirin a ranar Juma’ar da ta gabata ce shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani ya rufe gasar karatun Alkur’ani mai girma na kasa da kasa karo na 32 da aka gudanarwa a nan Iran.

 

A karshen gasar dai mahaddata da makarantar Alkur’ani da suka wakilci Iran sun sami nasarar zama na daya a gasar a bangaren hadda da tilawar Alkur’ani mai girma da aka gudanar.

 

Rahotannin sun ce a bangaren haddar Alkur’ani mai girma, Hujjatul Islam Muhammad Mahdi Rajabi shi ne ya zo na daya, sai kuma wakilan kasashen Libiya, Nijar, Uganda da Somaliya wadanda suka dauki matsayi na biyu zuwa na biyar.

 

Haka nan kuma a bangaren tilawar Alkur’ani, Hasan Danesh daga Iran shi ne ya zo na daya sai kuma wakilan kasashen Masar, Pakistan, Indonusiya da Iraki wadanda suka zo a matsayi na biyu zuwa na biyar.

 

An dauki mako guda ne dai ana gudnar da wannan gasar ta Alkur’ani da ta samu halartar wakilai daga kasashe kimanin 80 na duniya.

 

-----------------------------------/

 

A bangaren wasannin motsa jiki ma dai, cikin makon Iran ta sami nasarori a bangarorin wasan Taekwando da kuma kwallon kafa.

 

A cikin makon ne tawagar wasan Taekwando na iran ta sami nasarar zama zakaran zakaru na duniya a gasar da aka gudanar a kasar Rasha inda ta samu lambobin girma na zinare guda 3 da tagulla guda 2 da kuma maki 65.

 

Sakamakon wannan nasara, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da wata sanarwa inda ya taya tawagar ta Iran da sauran al’ummar kasar murnar wannan nasarar da aka samu.

Har ila yau a bangaren kwallon kafa ma kungiyar kwallon kafa ta Perspolis ta Iran wacce take wakiltar kasar a gasar zakaran zakarun nahiyar Asiya ta  samu nasarar lallasa kungiyar kwallon kafa ta al-Hilal na Saudiyya da ci daya da sifili a zagaye na biyu na gasar.

 

--------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Ministan harkokin cikin gidan Iran Abdurridha Rahmani Fazli ya bayyana cewar babu wata tantama Iran za ta yi amfani da karfi matukar ‘yan kungiyar ta’addancin nan na Da’esh (ISIL) suka kusato kan iyakan kasar da kasar Iraki.

 

Ministan harkokin cikin gidan na Iran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce: Tun a baya mun sanar da cewa matukar ‘yan kungiyar ISIS suka kusato kan iyakan kasar mu da kimanin kilomita 40 da  nufin wuce gona da iri, to ko shakka za mu shigo cikin yakin da ake yi da kungiyar kai tsaye.

 

Mr. Fazli ya kara da cewa har ya zuwa yanzu dai kungiyar ta’addancin ta Da’esh ba ta aikata  wani abin da ke barazana ga kan iyakokin kasar ta Iran ba sakamakon kasantuwar sojojin Iran a kan iyakokin, yana mai kakkausar suka kan kasantuwar sojojin Amurka a yankin da sunan fada da kungiyar ta ISIS wanda ya ce sun gaza wajen dakile ayyukan ‘yan kungiyar a kasar Irakin.

 

Ministan harkokin cikin gidan na Iran ya ce a duk inda sojojin Iraki suka sami nasara kan ‘yan kungiyar ta ISIS, to sun sami wannan nasarar ce kuwa albarkacin hadin kan da suke samu daga wajen dakarun sa kai na kasar ba wai taimakon Amurka ba.

 

-------------------------------------/

 

A ci gaba da nuna goyon bayan da al’ummar Iran suke yi ga al’ummar kasar Yemen da Saudiyya take ci gaba da ruwan bama-bamai a kansu, dubban mata ne da suka fito daga bangarori daban-daban na kasar ta Iran suka taru a gaban ofishin MDD da ke birnin Tehran don yin Allah wadai da wannan danyen aiki na gwamnatin Saudiyyan.

 

Kamfanin dillancin labaran hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran ya bayyana cewar matar wadanda suka taru a gaban ofishin MDD sun yi Allah wadai da halin ko in kula da MDD take nunawa kan hare-haren wuce gona da irin Saudiyya kan al’ummar ta Yemen.

 

Matayen dai wadanda suke rera taken Allah wadai da HKI da Amurka da kuma gwamnatin Al Sa’ud ta Saudiyya da suka kira da sunan maha’inta sun yi Allah wadai da ci gaba da zaluntar al’ummar Yemen din da Saudiyya karkashin sanya ido da jagorancin Amurka da HKI.

 

A karshen zaman dirshan din nasu matan sun fitar da wata sanarwar bayan taro inda  suka bayyana ci gaba da kai hare-haren kan al’ummar Yemen da Saudiyya take yi a matsayin watsi da koyarwar Ubangiji, suna masu cewa ko shakka babu gwamnatin Saudiyyan ba za ta cimma manufarta a kan al’ummar Yemen din don kuwa karya ba ta ‘ya’ya inji su.

Add comment


Security code
Refresh