An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 17 January 2015 02:38

Iran A 2014 (2)

Iran A 2014 (2)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shiri na Iran A Mako dake leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan dukkanin masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare a mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

Idan masu saurare suna tare a mu a makon da ya wuce, kamar yadda muka saba a kowace shekara idan karshen shekara ta miladiyya ko kuma ta hijira shamsiyya ta zo mu kan yi dubi cikin muhimman al’amurran da suka dau hankali cikin shekarar. Don haka ne a shirinmu na makon da ya wuce muka yi dubi cikin shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran da kuma tattaunawar da ta gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a wannan bangaren.

 

To shirin mu na yau zai yi dubi yi dubi ne cikin irin rawar da Iran ta taka a fagagen kasa da kasa a shekarar da ta gabatan ta 2014. Sai a biyo mu bayan wannan mabudin kunnen.

 

--------------------------------------,

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Duk da kokarin da kasashen yammaci suka yi tsawon shekarar da ta gabata ta 2014 wajen mayar da Iran saniyar ware, to amma duk da haka Iran ta sami nasarar daukar bakuncin tarurrukan kasa da kasa da na kasashen wannan yanki daban-daban masu muhimmanci.

 

A shekarar da ta gabatan ce dai shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya kai ziyara birnin New York don halartar taron babban zauren MDD karo na 69 wanda ita ce ziyara ta biyu da shugaban na Iran ya kai birnin New York din tun bayan da ya dare karagar mulkin Iran.

 

A yayin wannan zaman, shugaba Ruhani yayi wa duniya karin haske kan mahanga da kuma siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bangarori daban-daban da suka shafi kasashen yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya. Shugaba Ruhani ya bayyana cewar yankin Gabas ta tsakiyan dai ya gaji da yakukuwan da aka kirkiro masa inda ya ce irin kura-kuran da kasashen yammacin suka yi ya sanya yankin Gabas ta tsakiyan ya zamanto wata tunga da ‘yan ta’adda da ayyukan ta’addanci.

 

Har ila yau kuma yayin da yake jan kunne dangane da karuwar tashin hankali da tsaurin ra’ayi a yankin Gabas ta tsakiyan, shugaban na Iran ya bayyana cewar: Ingantacciyar hanyar fada da wannan annoba ita ce tattaunawa tsakanin kasashen yankin bugu da kari kan hadin kan sauran kasashen duniya.

 

Shugaba Ruhani ya kara da cewa idan har ana son fada da wannan annoba ta ta’addanci wajibi ne a gano tushen hakan da kuma tumbuke shi don kuwa ta’addancin yana samun gindin zama ne karkashin inuwar talauci, rashin aikin yi, nuna wariya, rashin adalci da kokarin kaskantar da wata al’umma. Don haka wajibi ne a tumbuke tushen haka ta hanyar tabbatar da adalci da kuma kawo karshen jirkita koyarwar saukakkun addinai don cimma wata haramtacciyar manufa.

 

A Shekaru biyun da suka gabata, a zaman babban zauren MDD karo na 68, ne shugaba Ruhanin ya fara jan kunnen duniya dangane da hatsarin ta’addanci ga duniya. Don haka ne ma shawarwarin da shugaba Ruhanin ya bayar a matsayin hanyoyin da za a bi wajen fada da ta’addancin ya samu amincewar kasashen duniya inda aka amince da shi a matsayin wani kudurin babban zauren MDDn. To sai dai abin bakin cikin shi ne kasashen yammacin ba su rungumi wannan jan kunne da shugaban na Iran ya yi musu hannu bibbiyu ba, hakan kuwa shi ne dalilin da ya sanya su fadawa tarkon ta’addancin wanda kuma a halin yanzu ya fara zama musu karfen kafa, duk kuwa da cewa suna da hannu cikin kirkiro shi, don haka ne ma wasu suke ganin kaikayi ne ya fara komawa kan mashekiya.

 

A jawabin da ya yi a shekarar baya a babban zauren MDD, shugaba Ruhani ya sake gabatar da wasu shawarwari da kuma sabbin tunani kan hanyoyin da za a magance matsalolin da suka yi wa duniya daurin has, duk kuwa da cewa wadannan kasashen masu neman yaki da kuma taimakon ‘yan ta’addan ba su ba wa wannan lamarin muhimmnaci ba, don kuwa sun fi fifita tunanin amfani da karfin soji a kan duk wani tunani da yayi daidai da hankali.

 

-----------------------------------------------/

 

Wani taron na daban da shugaban kasar ta Iran ya halarta da kuma kara bayanin mahangar Iran kan lamurra daban daban shi ne taron duniya kan tattalin arziki karo na 44 da aka gudanar a birnin Davos. A yayin wannan taron dai shugaban na Iran ya yi karin haske kan siyasa da kuma tsare-tsaren Iran a fagen tattalin arziki. Har ila yau shugaba Ruhani ya bayyana ta’addanci a matsayin wani lamari mai hatsarin gaske ga duniya. Don haka ne ma ya ce matukar aka bari ta’addanci ya yadu, to ba wai yankin gabas ta tsakiya ne kawai zai cutu ba, face dai kasashen Turai da ma duniya baki daya ba za su tsira ba.

 

Har ila yau shugaba Ruhani ya bayyana cewar kulla kyakkyawar alaka da kasashen da ke makwabtaka da Iran yana daga cikin siyasar da Iran ta sanya a gaba. Sai dai shugaban na Iran bai tsaya nan ba kawa inda ya kara da cewa a kullum Iran tana maraba da kyautata alakarta da sauran kasashe masu tasiri a duniya.

 

A tarurruka daban-daban dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana wa duniya cewa babu wani ta’addanci mai kyau da mara kyau, ta’addanci dai ta’addanci don haka wajibi ne a yi dukkanin abin da za a iya wajen kawo karshen wannan annoba ta ta’addanci a yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

 

A saboda haka ne ma tsawon shekarar barar Iran ta yi abubuwa daban-daban don sauke wannan nauyin da kuma karfafa alakar da ke tsakaninta da sauran kasashen wannan yankin musamman kasashen musulmi wajen magance matsalolin da suka kunno kai ba tare da share fagen tsoma bakin ‘yan kasashen waje ba.

 

Don cimma wannan manufar ce ma ya sanya a farko-farkon shekara ta 2014, a daidai lokacin shigowar sabuwar shekara ta hijira shamsiyya, shugaba Ruhani ya kai ziyara kasar Afghanistan don halartar taron kasa da kasa na sabuwar shekarar. Inda a taron da aka gudanar tsakanin shugabannin kasashen Iran, Pakistan, Afghanistan da Tajikistan, shugaba Ruhani da sauran takwarorinsa suka jaddada wajibcin fada da tsaurin ra’ayi da kuma ta’addanci kamar yada suka ci duk wani rikon sakainar kashi ga hakan, lamari ne da zai share fagen kara yaduwar ayyukan ta’adancin. A nan ma dai shugaban na Iran ya sanar da aniyar Iran na aiki tare da kasashen wajen fada da ta’addanci.

 

-----------------------------------------/

 

Bayan ga tarurrukan da jami’an Iran suka halarta a kasashe daban-daban, har ila yau kuma a shekarar da ta gabatan Iran ta dauki bakunci tarurruka daban-daban masu muhimmancin gaske. Daga cikin irin wadannan tarurrukan har da taron kasa da kasa kungiyoyi masu kafirta musulmi a mahangar malaman Musulunci da aka gudanar da a birnin Qum wanda ya shafi halartar malamai da masana daga kasshen duniya daban-daban.

 

A wata ganawa da ya yi da mahalarta taron Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar: Samar da wani yunkuri na ilimi na gama gari da yayi daidai da hankali wajen tumbuke tushen wadannan kungiyoyi masu kafirta mutane, haka nan da kuma wayar da kan mutane dangane da siyasar ma'abota girman kai na sake rayar da wannan kungiya da kuma sake rayar da lamarin Palastinu a matsayin babbar matsalar duniyar musulmi, daya ne daga cikin mafiya girman nauyin da ke wuyan malaman duniyar musulmi a wannan lokaci da muke ciki.

 

Ayatullah Khamenei ya bayyana rusa tushen ababe masu kima da tsarki na kasahen musulmi da ‘yan takfiriyyar suke yi a matsayin wani misali na daban na irin ayyukan da suke aikatawa wajen biyan bukatun makiya Musulunci, inda ya ce: Wani aikin na daban mai munin gaske da ‘yan takfiriyyan suke aikatawa shi ne shafa wa wannan addini mai cike da rahama da hikima na Musulunci kashin kaji ta hanyar nuna wasu hotuna masu muni irin su sare kawukan mutanen da ba su ci ba su sha ba, ko kuma ciro zuciyar wani musulmi da tauna ta a gaban kyamarori sannan kuma da sunan Musulunci.

 

-----------------------------------------/

Har ila yau kuma daga cikin tarurruka masu muhimmanci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki bakuncinsu a shekara ta 2014 din shi ne Taron kara wa juna sani na kasa da kasa na farko don fada da tashin hankali da tsaurin ra’ayi da ke  yaduwa a duniya.

 

Shi dai wannan taro na kwanaki biyu, wanda aka shirya shi bisa shawarwarin da shugaban kasar Iran ya gabatar a jawabin da ya gabatar a babban zauren MDD ya sami halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da masana daga sama da kasashe 50 na duniya.  Manufar  taro ita ce tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen fada da tushe da dalilan tsaurin ra’ayi da kuma tashin hankalin da a halin ya fara zama karfen kafa ga duniya baki daya.

 

A jawabin bude taron da ya gabatar, shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana wajibcin fada da tashin hankali da tsaurin ra’ayi da nufin karfafa irin alaka ta ‘yan’uwantaka tsakanin kasashen duniya.

 

Har ila yau yayin da yake magana kan kasashen da a baya suke taimakon ‘yan ta’adda sannan a halin yanzu kuma  suke ta kumfan baki kan fada da ta’addanci, shugaba Ruhani y ace idan har da gaske suke yi suna son fada da ta’addancin ne, to wajibi ne su fito fili su yi Allah wadai da ‘yan ta’addan, sannan kuma su taimaki kasashen da suke fuskantar annobar ta’addanci, kamar yadda kuma wajibi ne su katse duk wata hanyar da ‘yan ta’addan suke samun taimakon da suke samu.

 

Har ila yau kuma daga cikin shawarwarin da shugaban na Iran ya gabatar wajen fada da ta’addancin sun hada da: karfafa bangaren koyarwa da kuma bayyanar wa da al’umma da hakikanin koyarwar addinin musulunci; aiki tare tsakanin kasashen duniya ciki kuwa har da musayen bayanai da kuma karfafa irin rawar da kafafen watsa labarai za su taka wajen wayar da kan al’ummomin duniya kan hatsarin da ke cikin ayyukan ta’addanci da kuma hasarar da ke janyo wa ga rayuwar al’umma.

 

---------------------------------/

 

Irin wadannan tarurruka na kasa da kasa da Iran ta dauki bakuncinsu da kuma wadanda ta dinga halarta tsaron shekara ta 2014 bugu da kari kan yadda jami’an gwamnatoci daban-daban suka dinga kawo ziyarar aiki nan Iran da nufin karfafa alakarsu da ita da dai sauransu alamu ne da suke nuni da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance cikin fagagen lamurra na kasa da kasa sannan kuma wannan kokari na Amurka da kawayenta na mai da ita saniyar ware ya ci kasa.

 

Masu saurare da haka muka kawo karshen shirin na mu na yau sai kuma a mako na gaba. Kafin nan nake cewa ku huta lafiya. wassalam

Add comment


Security code
Refresh