An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 05 January 2015 12:35

Iran A Mako…Iran A 2014 (1)

Iran A Mako…Iran A 2014 (1)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shiri na Iran A Mako dake leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan dukkanin masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare a mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

 

Kamar yadda muka saba a kowace shekara idan karshen shekara ta miladiyya ko kuma ta hijira shamsiyya ta zo mu kan yi dubi cikin muhimman al’amurran da suka dau hankali cikin shekarar. Don haka a shirinmu na yau da kuma mai zuwa mako mai zuwa za mu yi dubi ne cikin wasu batutuwa masu muhimmanci da suka faru cikin shekara ta 2014 a nan Iran.

 

Shirin na mu na yau zai yi dubi ne cikin shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran da kuma tattaunawar da ta gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan wannan shiri tsawon shekara ta 2014. Don haka sai a biyo mu bayan wannan mabudin kunnen.

 

---------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Cikin shekara ta 2014, Iran ta aiwatar a wasu abubuwa masu muhimmanci wajen tabbatar da kyakkyawar aniyarta da kawo karshen kace nace na sama da shekaru goma da kasashen yammaci suka kirkiro kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran.

 

Lamari na farko da Iran ta fara yi a wannan bangaren shi ne yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniyan da ake kira kasashen 5+1 (wato Amurka, Rasha, China, Faransa, Birtaniyya bugu da kari kan kasar Jamus) a birnin Geneva na kasar Swiss. A farko-farkon shekara ta 2014 ne, bayan zaman tattaunawa daban-daban da masanan bangarorin biyu suka yi, aka sanar da cimma yarjejeniya ta gaba daya kan wannan lamarin. A yayin wannan zaman dai an tsaida ranar 24 da watan Nuwamba a matsayin wa’adin da za a cimma matsaya da yarjejeniya ta gaba daya tsakanin bangarorin biyu kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen Iran Dakta Abbas Araqchi ya sanar. A cikin wannan yarjejeniyar dai bangarorin biyu za a aiwatar da wasu ayyuka cikin wannan lokacin wanda zai share fagen kai wa ga yarjejeniya ta gaba dayan. Daga cikin abubuwan da aka amince da shi din har da cewa za a dage wasu daga cikin takunkumin da aka sanya wa Iran, ita kuma a nata bangaren za ta dakatar da tace uranium kasha 20 cikin dari. Kamar yadda kuma an tsaida cewa za a sako dala biliyan 4.2 na kudaden Iran da manyan kasashen duniyan suka kwace tsawon wata shida.

 

Tsawon wannan lokacin Iran ta ci gaba da ba da hadin kan da ta saba yi wa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Don haka ne ma masana da jami’an hukumar suka kawo ziyara nan Iran da nufin share fage da samar da yanayin da za a aiwatar da wannan yarjejeniya ta Geneva da aka cimma. Ta haka ne wannan tattaunawar ta kai wani matsayin da ke nuni da cewa dukkanin bangarori biyu a shirye suke su aiwatar da abin da aka cimma yayin yarjejeniyar ta Geneva.

 

A hakikanin gaskiya ana iya cewa yarjejeniyar ta Geneva ta ginu ne bisa wani tushe mai muhimmanci; shi ne kuwa amincewa da hakkin Iran na mallakar fasahar nukiliya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya NPT. Ta haka ne aka ayyana abubuwan da za a tattauna da Iran a kansu da kuma tabbatar da cewa hakkin al’ummar Iran na mallakar fasahar nukiliya wani lamari ne da ba za a iya rufe ido kansa ba sannan kuma duk abin da jami’an Iran suke yi ba watsi da wannan hakkin ba ne face dai wani kokari ne tabbatar da kyakkyawar aniyar da Iran din take da shi cikin wannan shiri na ta sabanin ihu bayan harin da kasashen yammacin suke yi.

 

A saboda haka ne a son ranta Iran ta fara taka wasu matakai daga cikinsu har da dakatar da tace uranium kashin 20 cikin dari da sauran don share fagen daya bangaren ma ya sauke nauyin dake wuyansa. Daga cikin nauyin da ke wuyan daya bangaren kuwa sun hada da dage takunkumin da suka sanya wa harkar sayar da man fetur na Iran gwargwadon abin da aka cimma; dage takunkumin da suka sanya wa fitar da man fetur da dangoginsa na iran ciki kuwa har da inshore da kuma shige da ficensa, dage takunkumin da suka sanya wa bangaren kasuwancin zinariya da takunkumin shigo da motoci da wasu kayan gyaran jiragen sama.

 

Da haka ne tattaunawar da ake yi da manyan kasashen duniyan don kai wa ga yarjejeniya ta gaba daya ta ci gaba sannan kuma aka dinga taka mataki daya bayan daya.

 

---------------------------------/

 

Tsawon wannan lokacin dai an gudanar a zaman tataunawa har sau goma tsakanin bangarori biyu a biranen Geneva, New York da Muscat inda aka tattanawa kan batutuwa masu muhimmanci cikin shirin nukiliyan na Iran da kuma yadda za a magance masalar.

 

A yayin wannan tattaunawar dai, daya daga cikin batutuwan da suka fi daukan hankali shi ne batun tace sinadarin uranium. A bisa yarjejeniyar da aka cimma Iran za ta ci gaba da wannan shiri na ta na nukiliya da ya hada tace sinadarin uranium din kasha biyar cikin dari don samar da makamashin da take bukata. Haka nan kuma ya zo cikin wannan yarjejeniya ta farko farko cewa matukar dai Iran ta yi aiki da hakan da kuma girmama yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya NPT, to za a yi mu’amala da ita kamar sauran kasashen da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniyar.

 

A bangaren guda kuma tsawon wannan lokacin Iran ta gudanar da tattaunawa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya dangane da adadin bututun tace sinadarin uranium da kuma wasu cibiyoyin nukiliyan na iran wadanda aka gina su da kuma wadanda ake ci gaba da ginawa.

 

To sai dai kuma duk da kokarin da bangarorin biyu suka yi wajen cimma matsaya kafin ainihin lokacin da aka tsara na watanni shida, lamarin ya ci tura don haka bangarorin biyu dai suka amince da a kara wa’adin tattaunawar zuwa ranar 24 ga watan Nuwamba. Shi din ma dai bayan ci gaba da tattaunawar musamman a ranakun karshe-karshe na watan Nuwamban, bangarorin biyu ba su cimma matsaya ba don haka bangarori biyu suka cimma matsayar kara wa’adin lokacin tattaunawar har zuwa 1 ga watan Yulin shekara ta 2015 ko za a sami damar cimma matsaya kan wannan tatttaunawar da ake yi.

 

Tsawon wannan lokacin, babban abin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi shi ne tabbatar a hakkin da take da shi na amfani da fasahar nukiliya a tafarkin zaman lafiya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliyan NPT, amma ba wai batun jan lokaci kamar yadda wasu masu bakar aniya suke son nunawa ba. Don kuwa ita wannan yarjejeniyar ba wai ta shafi wasu kasashe ba ne ban da wasu. A saboda haka ne Iran take bayyana cewar wajibi ne yarjejeniyar da za a cimma ta zamanto karkashin wannan inuwar wannan yarjejeniya ta NPT.

 

-----------------------------/

 

A halin yanzu dai shekaru 12 kenan kasashen yammaci suke ta ihu bayan hari da kuma tada jijiyoyin wuya da gangan kan wannan shiri na nukiliyan zaman lafiya na Iran. Tsawon wadannan shekaru Amurka ta yi kokari wajen sanya tsoron Iran cikin zukatan kasashen duniya da bayyana ta a matsayin wata barazana ga sulhu da zaman lafiyan duniya. To sai dai kuma bayan tsawon wadannan shekaru na nuna kiyayya da kirkiro kissoshi na karya kan shirin nukiliyan, bugu da kari kan sanya takunkumi da sauran, daga karshe dai ta fara fahimtar cewa Annabi fa ya faku, don haka ta nemi zama teburin tattaunawa da Iran don kuwa ta fahimci cewa dukkanin wadannan abubuwa ba za su haifar mata da da mai ido ba.

 

Masana dai suna ganin cewa wannan matsaya da Amurka ta dauka na neman zama teburin tattaunawa da Iran, ya samo asali ne saboda bukatar da gwamnatin Amurkan ta Barack Obaman take da ita ga hakan musamman ganin irin matsaloli daban-daban da ta sami kanta. To amma a bangare guda kuma akwai wasu bangarorin da suke ci gaba da matsa wa gwamnatin ta Obama lamba musamman HKI da kuma wasu cibiyoyin yahudawa masu fadi a ji cikin siyasar Amurkan kai ciki ma har da wasu kasashen larabawa wadanda ba sa fatan ganin an cimma wata yarjejeniya kan shirin nukiliyan ta Iran.

 

Don haka tsawon shekara guda din da ta gabata, sabanin yarjejeniyar farko-farkon da aka cimma, Amurka ta sake kakaba wa Iran wasu sabbin takunkumin wanda ko shakka babu hakan Karen tsaye ne ga yarjejeniyar da aka cimma din na cewa ba za a sake sa wa Iran wasu sabbin takunkumin ba face ma dai wadanda aka sanya su za a cire su a hankali a hankali.

 

A bangare guda kuma tsawon lokacin wannan tattaunawar tawagar Iran ta tabbatar da tsayin dakan al’ummar Iran a gaban irin wadannan matsin lamba ta siyasa daga wajen kasashen yammacin sakamakon irin goyon bayan da suke samu a wajen Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei sannan da uwa uba kuma al’ummar Iran din.

 

Masana dai suna ganin tsawon wannan lokaci na tattaunawar, Iran ta cimma nasarori masu muhimmanci daga cikinsu kuwa ko kuma ma a ce mafi muhimmancinsu shi ne ci gaban wannan shiri nata ba tare da dakatar da shi ba, sannan kuma a hukumance kasashen yammacin sun amince da hakkin da Iran take da shi na mallakar fasahar nukiliya.

 

-------------------------------------/

 

Masu saurare lokacin da aka diba wa shirin ya kawo jiki don haka a nan za mu yi ban kwana da ku sai kuma a mako na gaba inda za mu kawo muku kashi na biyu kuma na karshe na wannan shirin inda za mu yi dubi ikin irin rawar da Iran ta taka fagen siyasar wannan yankin da kuma na kasa da kasa.

 

Kafin lokacin na ke cewa ku zama lafiya.

 

wassalam

Add comment


Security code
Refresh