An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 20 December 2014 05:06

Iran A Mako 18-12-2014

Iran A Mako 18-12-2014
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

 

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Daga cikin batutuwan da suka dau hankula cikin makon har da bukukuwan ranar Arba’in na shahadar Imam Husain (a.s) da aka gudanar a nan Iran da kuma birnin Karbala na kasar Irakin inda sama da mutane miliyan guda daga Iran suka sami halarta; wani batun kuma da ya dau hankali shi ne taron kasa da kasa kan fada da tsaurin ra’ayi da kuma tashin hankali da aka gudanar a nan birnin Tehran; wani batun kuma shi ne taron da aka gudanar tsakanin jami’an kasar Iran da na kasar Rasha kan fada da batun fasa kwabrin muggan kwayoyi; sai kuma batun sake zama teburin tattaunawa tsakanin Iran da kasashen 5+1 kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar, bugu da kari kan wasu batutuwan na daban da za mu kawo muku su cikin shirin na mu na yau.

 

Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

A ranar Asabar  din da ta gabata wato 13 ga watan Disamba wacce ta yi daidai da ranar 20 ga watan Safar ne aka gudanar da bukukuwan ranar Arba’in na shahadar Imam Husain (a.s), Limamin Shi’a na uku da sahabbansa a Karbala.

 

Kamar kowace shekara dai miliyoyin al’ummar Iran ne a duk fadin kasar suka gudanar da wadannan bukukuwan don tunawa da kuma juyayin wannan danyen aiki da Umayyawa karkashin jagoranci Yazidu bn Mu’awiyya suka aikata a kan zuriyar Ma’aikin Allah (s.a.w.a).

 

A nan birnin Tehran ma baya ga Husainiyoyi da masallatai daban-daban da aka gudanar da irin wadannan tarurruka na juyayi, har ila yau dubun dubatan daliban jami’oin birni ne suka gudanar da irin wannan taro na Juyayi a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda Jagoran ya halarci wannan taron.

 

A wannan shekarar ma kamar shekarun da suka gabata, miliyoyin al’ummar musulmi ne daga kasashe daban-daban na duniya suka kai ziyara birnin Karbala na kasar Iraki don ziyartar hubbaren Imam Husain (a.s) da ke birnin da kuma gudanar da wannan biki na Arba’in; duk kuwa da matsalar tsaro da yiyuwar kai musu hare-haren ta’addanci.

 

Daga nan Iran kawai, an kiyasta cewa sama da mutane miliyan guda da dubu 300 ne suka tafi Karbala din don gudanar da ziyarar.

 

Taron na bana dai ba a taba yin irinsa ba tsawon tarihi inda aka bayyana cewar sama da mutane miliyan 19 ne suka halarci birnin na Karbala a bana sakamakon kiraye-kirayen da maraja’an duniyar Shi’a suka yi na a halarci taron na bana don kalubalantar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi da suke barazanar kawo hare-hare wa  wajaje masu tsarki na ‘yan Shi’a na kasar ta Iraki.

 

----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a karshe-karshen makon da ya gabata ne aka gudanar da taron kara wa juna sani na kasa da kasa na farko kan fada da tashin hankali da tsaurin ra’ayi a nan birnin Tehran. Shi dai wannan taro na kwanaki biyu ya sami halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da masana daga sama da kasashe 50 na duniya.

 

Manufar  wannan taro dai ita ce tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen fada da tushe da dalilan tsaurin ra’ayi da kuma tashin hankalin da a halin ya fara zama karfen kafa ga duniya baki daya inda mahalarta taron suka tattauna kan batutuwa da  suka shafi hanyoyin da za a bi wajen aiki tare wajen kawo karshen talauci da rashin aikin yi a matsayin wasu daga cikin dalilan da suke haifar da tsaurin ra’ayi da kuma tashin hankali. Kamar yadda kuma aka tattauna kan hanyoyin da za a taimakawa kasashen da suke fuskantar wannan matsalar tsaurin ra’ayi da kuma ayyukan ta’addanci bugu da  kari kan sanya ido sosai a kan iyakokin kasashen duniya don hana yaduwa da shige da ficen ‘yan ta’adda.

 

Har ila yau a yayin zaman taron kuma an kafa kwamitoci daban-daban da za su yi dubi kan wadannan batutuwa duk dai da nufin fada da wannan annoba.

 

A jawabin bude taron da ya gabatar, shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana wajibcin fada da tashin hankali da tsaurin ra’ayi da nufin karfafa irin alaka ta ‘yan’uwantaka tsakanin kasashen duniya.

 

Har ila yau yayin da yake magana kan kasashen da a baya suke taimakon ‘yan ta’adda sannan a halin yanzu kuma  suke ta kumfan baki kan fada da ta’addanci, shugaba Ruhani y ace idan har da gaske suke yi suna son fada da ta’addancin ne, to wajibi ne su fito fili su yi Allah wadai da ‘yan ta’addan, sannan kuma su taimaki kasashen da suke fuskantar annobar ta’addanci, kamar yadda kuma wajibi ne su katse duk wata hanyar da ‘yan ta’addan suke samun taimakon da suke samu.

 

Har ila yau kuma daga cikin shawarwarin da shugaban na Iran ya gabatar wajen fada da ta’addancin sun hada da: karfafa bangaren koyarwa da kuma bayyanar wa da al’umma da hakikanin koyarwar addinin musulunci; aiki tare tsakanin kasashen duniya cikin kuwa har da musayen bayanai da kuma karfafa irin rawar da kafafen watsa labarai za su taka wajen wayar da kan al’ummomin duniya kan hatsarin da ke cikin ayyukan ta’addanci da kuma hasarar da ke janyo wa ga rayuwar al’umma.

 

A watannin baya ne dai shugaban kasar ta Iran, a jawabin da ya gabatar a babban zauren majalisar dinkin duniya ya gabatar da shawarar hada karfi waje guda don fada da tsaurin ra’ayi da tashin hankali a duniya lamarin da kasashen duniya daban daban suka yi maraba da shi.

 

-----------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da  sake saduwa.

 

A jiya Laraba ce dai aka sake komawa teburin tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya na kungiyar nan da ake kira 5+1 kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran. Taron na jiya dai an gudanar da shi tsakanin mataimakan ministocin harkokin wajen wadannan kasashen a birin Geneva na kasar Swiss.

 

Wannan taron dai shi ne irin sa na farko da aka gudanar tsakanin bangarorin biyu tun bayan da aka cimma matsayar kara wa’adin tattaunawar da ke gudana tsakaninsu bayan gushewar wa’adin ranar 24 ga watan Nuwamban da ya gabata da aka cimma tun farko a matsayin ranar da za a cimma matsaya kan shirin nukiliyan na iran amma dai aka gagara cimma wannan matsayar.

 

Kafin wannan lokacin dai kafafen watsa labaran kasashen yammacin sun ta yada labarurruka marasa tushe don cimma wasu manufofi na su da suka hada da batun cewa Iran ta amince a tattauna batun makamanta masu linzami masu cin dogon zango lamarin da mataimakin ministan harkokin wajen na Iran Dakta Abbas Araqchi ya musanta inda ya ce babu gaskiya cikin wannan ikirari da ake yi.

 

Har ila yau kuma cikin makon ne dai wasu kafafen watsa labaran suka fara yada wani labara da ke nuni da cewa Iran ta gudanar da wani gwaji na nukiliya a daya daga cikin cibiyoyin nata na nukiliya lamarin da jakadar Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniyan (IAEA) Ridha Najafi ya musanta yana mai cewa Iran a shirye take ta tabbatar wa da hukumar da rashin ingancin wannan ikirarin.

 

Wannan ikirarin dai ya fara fitowa ne daga bakin jakadar kasar Kanada a hukumar ta IAEA lamarin da ya fuskanci mayar da martani mai kaushi daga wajen jakadan na Iran inda y ace kasar Kanada, wacce ta yi gum da bakinta kan shirin nukiliyan HKI wanda shi ne ma babbar barazana ga yankin Gabas ta tsakiya, ba ta da hakkin ma ta yi magana da kuma nuna damuwarta dangane da yaduwar makaman nukiliya a duniya. Inda  y ace manufar yada irin wadannan labarurruka marasa tushe ita ce wasa da hankalin hukumar kula da makashin nukiliyan ta duniya da kuma kasashe membobinta ne.

 

------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a karshe-karshen makon da ya gabata ne ministan cikin kasar Iran Rahamani Fadhli ya kai ziyarar aiki kasar Rasha inda ya gana da takwararsa na kasar Vladimir Kolokoltsev da nufin tattaunawa kan yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a baya dangane batun fada da fasa kwabrin muggan kwayoyi, ayyukan ta’addanci, tsaurin ra’ayi da kuma muggan laifuffuka.

 

Har ila yau kuma ministan cikin gidan na Iran wanda kuma shi ne babban sakataren hukumar  fada da muggan kwayoyi ta Iran ya gana da shugaban hukumar fada da muggan kwayoyi ta kasar Rashan Victor Evanov. A yayin wannan ganawar dai ministan cikin gidan na Iran ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da rikon sakainar kashin da wasu kasashen yammaci ciki kuwa har da kasar Amurka suke yi dangane da batun fada da muggan kwayoyin.

 

Ministan cikin gidan na Iran yayi ishara da irin karuwar nomawa da kuma samar da muggan kwayoyi a kasar Afghanistan tun bayan da Amurka ta mamaye kasar wanda y ace hakan lamari ne da ke tabbatar da rashin gaskiyar Amurkan a ikirarin da take yi na fada da muggan kwayoyin don haka yayi kiran da a dau matakan da suka dace wajen fada da wannan annobar wacce take barazana ga zaman lafiyar duniya.

 

Tun a shekara ta 2005 ne dai Iran da kasar Rasha suke gudanar da ayyuka tare wajen fada da fataucin muggan kwayoyin bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsu.

 

-----------------------------------/

 

END

Add comment


Security code
Refresh