An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 29 November 2014 17:04

Iran A Mako 27-11-2014

Iran A Mako 27-11-2014
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

 

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau har da taron kasa da kasa dangane da hatsarin akidar kafirta musulmi da aka gudanar a birnin Qum da ya sami halartar malamai da masana daga kasashe sama da 80 na duniya. Wani batun kuma da ya dau hankula a ciki da wajen Iran shi ne batun tattaunawar da ta gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya a birnin Vienna gabannin kusatowar wa’adin da aka tsayar na cimma yarjejeniya; lamarin da ya sanya wasu daliban jami’oi na Iran shirya wani jerin gwano don nuna goyon bayansu ga masu tattaunawar da kuma sake jaddada matsayar Iran na hakkin mallakar fasahar nukiliya. Wani batun da za mu yi dubi cikinsa a shirin na mu na yau har da ziyarar aiki da shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya kai kasar Djibouti da kuma ziyarar da alkalin alkalan kasar Qatar ya kawo nan Iran.

 

Wadannan nan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali don jin yadda shirin zai kasance.

 

------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Lahadin da ta gabata ce aka bude taron kasa da kasa dangane da hatsarin kungiyoyin ‘yan Takfiriyya masu kafirta musulmi a birnin Qum na Iran mai taken “Kungiyoyi Masu Tsaurin Ra’ayi Da Kafirta Musulmi A Mahangar Malaman Musulunci”.

 

Ayatullah al-Uzma Sheikh Nasir Makarem Shirazi, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shi’a da ke birnin na Qum ne ya bude taron.

 

A jawabin da ya gabatar Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana cewar wajibi ne al’ummar musulmi su gudanar da bincike dangane da akidun kungiyoyi takfiriyya masu kafirta musulmi da kuma yin dukkanin abin da za su iya wajen kawo karshen wannan bakar akida da ke ci gaba da shafa wa addinin Musulunci kashin kaji.

Ayatullah Makarem Shirazi ya kara da cewa Musulunci dai addini ne na so da kauna hatta ga wadanda ba musulmi ba, don haka wajibi ne a nuna wa duniya cewa masu wannan akida ta kafirta musulmi baki ne a tsakanin musulmi.

 

Yayin da yake magana dangane da yaki da ‘yan wannan kungiyar kuwa, Ayatullah Makarem Shirazi ya ce fada ta makami bai wadatar ba, wajibi ne malaman duniyar musulmi su tsaya kyam wajen fada da tushen akidar ta su.

 

Bayan jawabin Ayatullah Makarem Shirazi, malamai da masana daban-daban ne suka gabatar da jawabinsu ciki har da tsohon firayi ministan kasar Iraki kuma ministan harkokin wajen kasar a halin yanzu Dakta Ibrahim Ja’afari da shugaban majalisar siyasa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Ibrahim Amin Sayyid da dai sauransu.

 

A yayin wannan taron dai an kafa kwamitoci guda hudu wadanda za su tattauna kan batutuwa guda hudu da taron zai fi ba su muhimmanci su ne: Tushen ‘yan Takfiriyya da kungiyoyi masu tsaurin ra’ayi; dubi cikin tushen da akidar takfiriyya ta ginu a kai; alala tsakanin siyasa da ‘yan takfiriyya sai kuma hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen akidar takfiriyya da hanyoyin da za a bi wajen fada da su.

 

A rana ta biyu na taron ma malamai da masana daga kasashen daban-daban na duniya sun gabatar da jawabansu dangane da irin hatsarin da wannan akida ta kafita musulmi take da shi da kuma barazanar da take yi wa zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar musulmi.

 

A yammacin ranar Litinin din ne dai aka rufe taron da jawabin da da Ayatullah al-Uzma Ja’afar Subhani, daya daga cikin maraja’an Shi’a da ke birnin Qum, ya gabatar inda daga karshe dai mahalarta taron suka fitar da sanarwar bayan taro.

 

-------------------------------/

 

Sanarwar bayan taron wadda Sheikh Nabil Na’im, daya daga cikin malaman Ahlusunna na kasar Masar ya karanta ta kumshi:

 

(1). Addinin Musulunci dai addini ne na  rahama da ‘yan’uwantaka da kyautatawa, don haka wajibi ne dukkanin musulmi su yi koyi da koyarwar wannan addini wajen kyautata alakarsu ta ‘yan’uwantaka da tausayawa ba wai kawai ga musulmi ba, hatta ga mabiya sauran addinai.

 

(2). Addinin Musulunci, addini ne da ke kira zuwa ga girmama akida da taunanin sauran mutane cikin hikima da girmamawa. A saboda  haka duk wani cin mutumci da keta hurumin ababe masu tsarki na mazhabobin Musulunci da ma na sauran addinai lamari ne da ya saba wa koyarwar Musulunci; don haka wajibi ne musulmi su nesanci hakan. Don haka mahalarta taron sun yi Allah wadai da keta hurumin ababe masu tsarki na Musulunci da wadanda ba na Musulunci ba da ‘yan kungiyoyin takfiriyya suke aikatawa a kasashen Iraki da Siriya wanda yake ba wa makiya damar ci gaba da shirinsu na bakanta Musulunci a idon al’ummomin duniya.

 

(3). A bisa koyarwar Musulunci duk mutumin da ya yi kalmar shahada, musulmi ne don haka jini da dukiyarsa da mutumcinsa sun haramta; kuma babu wanda ya ke da hakkin ya cire shi daga cikin Musulunci.

 

(4). A bisa koyarwar Musulunci mutum yana fita daga Musulunci ne sakamakon karyata tushen imani da Allah, Annabi (s.a.w.a) da ranar Lahira ko kuma karyata abin da Allah ya sauko da shi, don haka mahalarta taron suna Allah wadai da gurbatattun akidun da ake yawo da su na kafirta musulmin da suka yi riko da wasu koyarwar da mafi yawan musulmi suka yi amanna da su, da kuma cewa ba akidu ne da za a amince da su ba.

 

(5). Yada akidar kafirta musulmi a tsakanin al’umma wata fitina ce kana kuma abar kyama a wajen musulmi. Don haka wajibi ne musulmi su yi Allah wadai da hakan sannan kuma su yi dukkanin abin da za su iya wajen kashe wutar wannan fitinar.

 

(6). Bisa la’akari da haramcin zubar da jini da keta hurumin ma’abota Alkibla, don haka kashe musulmi babban zunubi ne da ba za a rufe ido kansa ba kana kuma Allah ya la’anci mai yin hakan. A saboda haka duk aiwatar da wannan akida ta masu kafirta musulmi da suka hada da hare-haren kunar bakin wake da sauran ayyuka na ta’addanci bugu da kari kan rusa wajajen bauta na musulmi da wadanda ba musulmi ba da ke bakanta fuskar musulmi haramun ne. Don haka wajibi ne musulmi su yi fada da hakan, kamar yadda kuma wajibi ne dukkanin gwamnatoci da kungiyoyin da suke goyon bayan ‘yan wannan kungiyar su kawo karshen irin taimako na kudi da siyasa da suke ba su.

 

Taron dai ya sami halartar malamai da masana kimanin 315 da suka fito daga kasashe 81 na duniya.

 

------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, a ranar Litinin din da ta gabata ne aka kawo karshen taron tattaunawa na kwanaki bakwai tsakanin Iran da manyan kasashen duniya (wato kasashen Amurka, Rasha, China, Faransa, Ingila da kasar Jamus kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran a birnin Vienna, babban birnin kasar Austria; inda dukkanin bangarorin suka amince da sake sabunta wa’adin tattaunawar zuwa 1 ga watan Yulin shekara ta 2015.

 

A da dai bisa abin da aka tsayar a tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu wacce aka faro ta a watan Nuwamban 2013, an tsayar da ranar 24 ga watan Nuwamban nan da muke ciki a matsayin wa’adin da za a cimma yarjejeniya ta gaba daya kan shirin nukiliyan zaman lafiyan na Iran. To sai dai sakamakon rashin cimma matsaya tsawon wannan lokacin da ba a yi ba, bangarorin suka amince da a kara tsawaita wa’adin ko watakila za a cimma matsaya.

 

Tsawon wannan tattaunawar dai ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya jaddada wa takwarorinsa na kasashen kungiyar 5+1 hakkin Iran na mallakar fasahar nukiliya ta zaman lafiya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT); kamar yadda jami’an Iran suka bayyana dauke wa Iran dukkanin takunkumin zalunci da aka sanya wa kasar a matsayin sharadin cimma yarjejeniya ta gaba daya a yayin wannan tattaunawar.

 

Tun dai bayan cimma yarjejeniyar Genevan, Iran ta yi aiki da dukkanin nauyin da ke wuyanta don tabbatar wa da duniya kyakkyawar niyyarta da take da ita na cewa shirin nukiliyan nata na zaman lafiya ne da ba ta da wani abin boyewa. Sai dai kuma sauran bangarorin da ake tattaunawa da su din musamman kasar Amurka, ba ma wai kawai ba ta yi aiki da nauyin da ke wuyanta ba ne face ma dai ta kara kakabawa Iran din wasu sabbin takunkumi din ne. Saboda bisa yarjejeniyar Genevan, kasashen 5+1 sun amince da cewa ba za su sake sanya wa Iran wani sabon takunkumi ba, to amma Amurka ta ci gaba da wannan aiki na ta na adawa da kasar Iran.

 

Masana a Iran da ma wasu kasashen suna ganin amincewar da Iran ta yi da tsawaita lokacin tattaunawar wata dama ce da Iran din ta sake ba wa kasashen yammacin musamman Amurka wajen dubi cikin siyasarta da kuma matsin lambar da ‘yan koren sahyoniyawa suke mata don ta dau matsayar da ta dace wacce kuma ta yi daidai da manufofin masu tattaunawar. Don kuwa kowa ya yi amanna da cewa cimma yarjejeniya kan wannan batu wani lamari ne da zai amfani dukkanin bangarorin da suke tattaunawar da kuma sulhu da zaman lafiyan duniya.

 

-------------------------------/

 

A daidai lokacin da tawagar ta Iran take ci gaba da tattaunawar, a cikin gida ma suna ci gaba da samun goyon bayan al’umma baya ga na manyan jami’an kasar. A ranar Lahadin da ta gabata ce dubun dubatan daliban jami’oin Iran suka gudanar da jerin gwano a gaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar da ke nan Tehran don nuna goyon bayansu ga ‘yan tawagar masu gudanar da tattaunawar karkashin jagorancin ministan harkokin waje Dakta Muhammad Jawad Zarif  suna masu jaddada hakkin da Iran take da shi na mallakar fasahar nukiliya ta zaman lafiya.

 

Su dai wadannan masu jerin gwanon, wadanda suke rike da hotunan manyan shahidan nukiliyan na Iran wadanda makiya suka kashe su sakamakon irin gudummawar da suka ba wa shirin nukiliyan na Iran, sun bayyana cewar sun fito ne don ba da goyon baya da kuma karfafa jami’an Iran din da suke tattaunawar kan su ci gaba da tsayin daka kan hakkin al’ummar Iran.

 

Har ila yau kuma daliban jamioin sun sake bayyana aniyarsu ta kare hakkin da Iran take da shi na mallakar fasahar nukiliya ko ana ha maza ha mata suna masu jan kunnen manyan kasashen duniyan da su yi taka tsantsan da irin maganganu da matakan da suke dauka kan al’umma Iran don kuwa ko da wasa al’ummar Iran ba za su yi watsi da irin nasarorin da suka samu a wannan bangaren ba.

 

-----------------------------------/

 

END

Add comment


Security code
Refresh