An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 13 November 2014 06:50

Iran A Mako 13-11-2014

Iran A Mako 13-11-2014
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

 

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a wannan makon har da nada sabon shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wanda yana daga cikin lamuran da suka ja hankula. Har ila yau a fagen watsa labaran kuma a cikin makon ne aka gudanar da wata kasuwa ta baje koli ta kafafen watsa labarai don gabatar da hanyoyin da ya kamata kafafen watsa labarai su bi wajen isar da sakonninsu ga al’ummomi. Wani batun da kuma ya dau hankali a kasar shi ne batun sake zamar tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar; da kuma rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya fitar kan shirin nukiliyan kasar Iran.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a cikin shirin na mu na yau, sai a biyo mu sannu a hankali.

 

------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, a ranar asabar din da ta gabata ce cikin wata sanarwa da ya fitar, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada Dakta Muhammad Sarafraz a matsayin shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin ta Iran na shekaru biyar. Wannan nadin dai ya biyo bayan karewar wa’adin shekaru goma na tsohon shugaban hukumar gidan radiyo ta talabijin din Injiniya Izzatullah Zarghami ne wanda Jagoran ya jinjina masa saboda irin aiki ba kama hannun yaro da ya yi a yayin da yake rike da shugabancin hukumar.

 

A cikin sanarwar nadin sabon shugaban, Jagoran yayi ishara da irin gagarumin nauyin da ke wuyan hukumar radiyo da talabijin din wajen kiyayewa da kuma fadada ‘yanci da matsayi da al'adu da matsayin juyin juya halin Musulunci na Iran ya ke da shi, kan yada addini, kyawawan halaye, fata, wayar da kai da yada salon rayuwa na Musulunci da Iran a tsakanin al'umma.  Don haka sai Jagoran yayi fatan alheri da kuma neman dacewa ta Ubangiji ga sabon shugaban wanda ya kasance daga cikin iyalan shahidan juyin juya halin Musulunci na kasar Iran.

 

Har ila yau kuma a wata sanarwar ta daban, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamenei ya nada tsohon shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran din Sayyid Izzatullah Zarghami a matsayin memba a majalisar koli ta al’adu da juyin juya hali da kuma majalisar kula da sanya ido kan hanyar sadarwa ta internet ta Iran.

 

-------------------------------------/

 

An haifi Dr. Sarfraz ne a cikin shekara ta 1961, ya yi karatunsa na firamare da sakandare da jami'a a birnin Tehran, ya kuma samu shedar kammala karatun digirin digirgir a bangaren ilmimin kimiyyar siyasa a jami'ar Beirut da ke kasar Lebanon, yana jin harsunan Turanci da larabci da kuma harshensa na Farisanci.

 

Kafin a nada shi shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin ta Iran din, Dakta Sarafraz yana rike ne da bangaren kasashen waje na hukumar gidan radiyo da talabijin din na Iran sama da shekaru 20 din da suka gabata. A tsawon wannan lokaci dai ya samu nasarori daban-daban da suka hada da bude gidajen radiyo da dama da suke watsa shirye-shirye a cikin harsuna daban-daban zuwa kasashe duniya daban-daban ciki kuwa har da gidan radiyon Hausa wanda aka bude shekaru 19 da suka gabata. Haka nan kuma ya bude gidajen talabijin da suke watsa shirinsu zuwa kasashen ketare a cikin harsunan daban-daban da suka hada har da tashar Press TV da ke watsa shirye-shiryen ta harshen turanci, Al-alam da ke watsa shirye-shiryenta da harshen larabci Hispan TV da ke watsa shirye-shiryenta da harshen Espaniyanci da sauransu.  

 

Ko shakka babu ya taka gagarumar rawa wajen isar da sakon juyin juya halin musulunci na kasar zuwa ga kasashen duniya ta hanyar kafofin sadarwa, wanda ake lissafa hakan a matsayin daya daga cikin muhimman ayyukansa ga jamhuriyyar Musulunci ta Iran. 

 

A lokacin kallafaffen yakin da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafawa wa Iran ma, Dr. Sarafraz ya kasance a sahun gaba gaba a lokacin yakin, wanda a yayin yakin ne ma ya rasa dan’uwansa wanda yayi shahada. Kamar yadda kuma daya daga cikin ‘yan’uwan nasa ma yayi shahada bayan nasarar juyin juya halin Musulunci lokacin da makiya suka sanya bom a helkwatar jam’iyyar Jamhuriyar Musulunci lamarin da ya yi sanadiyyar shahadarsa tare da wasu manyan jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikinsu kuwa har da Ayatullah Shahid Beheshti, wanda a lokacin shi ne shugaban ofishinsa.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

A farko-farkon wannan makon ne aka sake zaman tattaunawa kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran na bangarori uku  tsakanin ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif da takwararsa na Amurka John Kerry da kuma wakiliyar tarayyar Turai a wajen tattaunawar Catherine Ashton a birnin Muscat, babban birnin Oman.

 

Daya daga cikin batutuwan da aka tattaunar shi ne batun dauke takunkumin zaluncin da manyan kasashen duniyan suka sanya wa Iran da kuma batun tace sinadarin uranium da Iran  take yi wanda har ya zuwa yanzu ba a cimma matsaya kan hakan ba sakamakon ci gaba da kafar ungulun da wasu kasashen yammacin suke yi bisa matsin lambar HKI.

 

Daya daga cikin hanyoyin da HKI da ‘yan Koran nata suke ci gaba da bi wajen yin kafar ungulu da kokarin cimma matsaya kan wannan lamari shi ne ci gaba da kokari sake takura wa kasar ta Iran. Ga misali a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar sai ga kungiyar Tarayyar Turai ta sake kakaba wa wasu cibiyoyi na Iran din ciki kuwa har da jami’ar nan ta  Sharif takunkumi lamarin da jami’an Iran din suka yi Allah wadai da shi da kuma bayyana shi a matsayin wani lamari da zai iya cutar da tattaunawar da ake yi.

 

Yayin da take magana kan hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Malama Marzieh Afkham ta bayyana wannan sabon mataki da tarayyar Turai din ta dauka a matsayin wani lamari mai cike da alamun tambaya wanda kuma ya saba wa ruhi na tattaunawa don neman fahimtar juna da ke gudana tsakanin Iran da kasashen yammacin.

 

A bangare guda kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar, ‘yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran din, cikin wata sanarwa da suka fitar, sun bukaci kasashen yammacin da su soke dukkanin takunkumin da suka sanya wa Iran, kamar yadda kuma suka ce Iran ba za ta taba amincewa da duk wani kaidi da iyaka da za a sanya mata cikin wannan shiri na nukiliyan zaman lafiya nata ba.

 

An tsayar da ranar 24 ga wannan wata na Nuwamba a matsayin wa’adin karshe da ya wajaba a cimma matsaya kan shirin nukiliyan na Iran wanda dukkanin bangarorin suke bayyanar da fatansu kan cimma matsaya kafin wannan lokacin duk kuwa da kiran da wasu suke yi na kara wa’adin lamarin da Iran din ya zuwa yanzu dai ta nuna rashin amincewarta da hakan.

 

--------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a safiyar ranar Litinin din da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da mataimakin shugaban kasar Iraki Dakta Nuri al-Maliki da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma. A yayin wannan ganawar, Jagoran ya jinjinawa irin jaruntaka da tsayin dakan da Nuri al-Malikin ya nuna a yayin da yake rike da matsayin firayi ministan kasar Irakin da kuma gagarumar hidimar da ya yi wajen tabbatar da tsaro da ‘yanci da kuma ci gaban kasar Iraki inda ya ce masa: Yayin mika mulkin da ya gudana a kasar Iraki, lalle ka aikata gagarumin aiki wajen hana faruwar rikici da rashin tsaro a kasar Iraki. Ko shakka babu ba za a taba mancewa da wannan babban aikin a kasar Iraki ba.

 

Yayin da yake ishara da irin masaniyar da Dakta Nuri al-Malikin yake da ita kan yanayin kasar Irakin da kuma matsalolin da take fuskanta, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Kokarin da kake yi wajen taimakon sabuwar gwamnatin Dakta Haidar al-Ibadi da kuma kokari wajen samar da hadin kai tsakanin al'ummar Iraki, lalle hakan wani lamari ne mai kyaun gaske, da wajibi ne ka ci gaba da yinsa.

 

Shi ma a nasa bangaren, mataimakin shugaban kasar Irakin Nuri al-Maliki, ya bayyana gagarumin farin cikinsa da ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci yana mai cewa: A koda yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai taimakon gwamnati da al'ummar Iraki a fadar da take yi da ayyukan ta'addanci da kuma tsoma bakin ‘yan kasashen waje.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin an gudanar da kasuwar baje kolin kafafen watsa labarai karo na ashirin na Iran da suka hada da jaridu, kamfanonin watsa labarai da shafukan internet da suke gudanar da aikin watsa labarai a nan birnin Tehran.

 

A jawabin da ya gabatar a yayin bude kasuwar, ministan al’adu da shiryarwa ta Musulunci na Iran Ali Jannati ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi amanna da ‘yancin da kafafen watsa labarai suke da shi karkashin dokokin kasa da nufin isar da sakonni da abubuwan da suke faruwa ga al’ummomi.

 

Taken kasuwar baje kolin na bana dai shi ne ‘yancin fadin albarkacin baki tare da la’akari da nauyin da ke wuyan mutum.

 

Manufar wannan taro dai ita ce dubi cikin yadda ‘yan jarida suke gudanar da ayyukansu da kuma share musu fagen da zai ba su damar gudanar da ayyukan na su cikin ‘yanci amma kuma tare da kula da dokoki da kyawawan halaye na al’umma bugu da kari kan nesantar yada labarurruka marasa tushe da kuma duk wani abin da zai cutar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.

 

Kafafen watsa labarai na jaridu da gidajen talabijin da radiyo bugu da kari kan cibiyoyin shafuffukan labarai na Internet daga cikin Iran da wajen kasar ne da suka fito daga kasashen Jamus, Amurka, Rasha, Faransa, China, Labanon, Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait, Iraki, Afghanistan, Siriya da Qatar suke halartar wannan kasuwa da za a rufe ta a gobe Juma’a.

Add comment


Security code
Refresh