An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 16 October 2014 06:52

Iran A Mako 16-10-2014

Iran A Mako 16-10-2014
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

 

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Daga cikin batutuwan da suka dau hankula cikin mako har da bukukuwan ranar idin Ghadir da aka gudanar a duk fadin Iran da kuma jawabi mai muhimmanci da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi a wannan rana inda ya ja hankalin al’ummar musulmi dangane da makircin da makiya suke kulla musu wajen rarraba kansu. Har ila yau kuma a cikin makon ne dai shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ya kai birnin Geneva, ci gaba da tatttaunawar da ake yi dangane da shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran, wani harin ta’addanci da wasu ‘yan ta’adda suka kai wa dakarun ‘yan kare kan iyaka na Iran, martanin da jami’an Iran suka yi ga wani sabon rahoton kwamitin kare hakkokin bil’adama na MDD da kuma wasu nasararori da aka samu a fagen ilimi a Iran, duk suna daga cikin lamurran da suka dau hankula da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Litinin din da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban al’ummar Iran don tunawa da ranar Idin Ghadir mai girma. A jawabin da ya gabatar a yayin wannan taron, Jagoran ya yi ishara da bakar farfagandar da makiya musulmi suke yadawa da nufin raba Musulunci da siyasa da kuma takaita addinin Musulunci kawai ga lamaru da suka shafi daidaikun mutane, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Lamarin Ghadir Khum, wata hanya ce mai karfin gaske da Musulunci ya rika wajen kore wannan mahanga ta raba addini da siyasa. Don kuwa Ghadir Khum wata alama ce da ke nuni da irin muhimmancin da Musulunci ya ke ba wa lamarin kafa hukuma da kuma aiwatar da siyasar gudanar da rayuwar al’umma.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana bullar kungiyoyi masu kafirta musulmi a kasashen Iraki da Siriya da wasu kasashen na daban a matsayin sakamako na shirin da ma’abota girman kai suka jima suna yi wajen haifar da rarrabuwan kai tsakanin musulmi inda ya ce: Sun samar da kungiyoyin Al-Qa’ida da Da’esh (ISIS) ne da nufin haifar da rarraba da kuma fada da Jamhuriyar Musulunci ne. To sai dai a halin yanzu kaikayi ya fara komawa kan mashekiya.

 

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa kokarin fada da tunani mai jan hankali da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar a matsayin babban dalilin da ya sanya ma’abota girman kai kara himma wajen haifar da sabani tsakanin musulmi, daga nan sai ya ce: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran Amurka, sahyoniyawa da gwamnatin Ingila lalatacciya, wacce ta yi kaurin suna a fagen rarraba kan al’umma, sun ninninka irin kokarin da suke yi na haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi da kawar da hankulan ‘yan Shi’a da Sunna daga makiyansu na asali.

 

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne duk wanda yayi imani da Musulunci sannan kuma ya yarda da ikon Alkur’ani, shin Shi’a ne shi ko kuma Sunna, wajibi ne ya farka ya kuma fahimci cewa abokiyar gabar Musulunci da musulmi na hakika, ita ce siyasar Amurka da Sahyoniyawa.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana sanya ido da kuma nesantar duk wani abin da zai sosa rai da zukatan wata kungiya ko mabiya wata mazhaba ta Musulunci a matsayin wani nauyi mai muhimmanci da ke wuyan dukkanin musulmi inda ya ce: Wajibi ne Shi’a da Sunna su san cewa duk wani aiki ko kuma wata magana, ciki kuwa har da cin zarafin ababe masu tsarki na sauran mutane da ya yi sanadiyyar sosa rai da rura wutar fitina (a tsakanin musulmi), ko shakka babu hakan zai amfani makiyan dukkanin musulmin ne.

 

---------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani, ya jagoranci wata tawaga ta ‘yan majalisar kasar zuwa birnin Geneva na kasar Swiss don halartar taron hadin gwiwan majalisu na duniya.

 

A ranar Litinin din da ta gabata ce aka bude wannan taro wanda za a dau kwanaki 4 ana yinsa. Tawagar ta Iran dai wacce ta kumshi ‘yan majalisa goma wadanda aka karkasu tsakanin kwamitoci daban-daban da za su tattaunawan da suka shafi kwamitocin na su a yayin wannan taro kafin a fitar da matsaya guda.

 

Daga cikin batutuwan da aka tsara tattaunawa a yayin zaman sun hada da hakkokin bil’adama, ayyukan ta’addanci, akidar amfani da karfi da tsaurin ra’ayi, sulhu da zaman lafiya ta duniya da dai sauran batutuwa da suke ci ma kasashen duniya daban-daban imma ba a ce dukkansu tuwo a kwarya da ake bukatar gano hanyoyin da za a magance su.

 

A yayin wannan taron dai, tawagar ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da batun da ya shafi kare hakkokin bil’adama na duniya da kuma alakar da hakan yake da ita ga batun iko na kasa da kuma haramcin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe masu ‘yanci na duniya.

 

Iran ta gabatar da wannan batu ne don samo hanyar da za a bi wajen toshe kafar da manyan kasashen duniya suke amfani da ita wajen tsoma baki cikin lamurran sauran kasashen duniya da sunan kare hakkokin bil’adama alhali su kuma ba sa barin duk wata kafa ta tattauna irin take hakkokin bil’adaman da suke a kasashensu da kuma wadanda suke da alaka ta kut da kut da su.

 

--------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a daren ranar Larabar makon da ya gabata ne ‘yan kungiyar ashararai ‘yan ta’adda da suke gudanar da ayyukansu a kan iyakokin kasar Iran da kasashen Pakistan da Afghanistan suka kai hari ga wasu ‘yan sandan kan iyaka na Iran a garin Saravan da ke lardin Sistan-e-Baluchestan da ke kudancin kasar Iran inda suka kashe hudu daga cikin ‘yan sandan.

 

Jim kadan bayan fitar da sanarwar wannan hari na ta’adanci da kuma shahadar wadannan ‘yan sanda guda hudu, babban mai shigar da kara na Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya ce koda wasa jami’an tsaro da ‘yan sandan kasar Iran ba za su yi shiru kan irin wadannan ayyukan ta’addancin da ake yi musu ba, ba tare da mayar da martani ba.

 

Babban mai shigar da karar ta Iran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Pakistan dangane da nuna halin ko in kula da take yi dangane da yadda ‘yan ta’addan suka mayar da kasar ta zamanto wata tunga ta ayyukansu na ta’addanci, don haka ya kirayi ma’aikatar harkokin wajen Iran da ta ba da himma wajen amfani da hanyoyi na diplomasiyya wajen ganin an dakatar da irin wadannan ayyuka na ta’addanci.

 

Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan ta’addan da suke shigowa daga kasar Pakistan suke aikata irin wadannan ayyuka na ta’addanci ba.

 

-----------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, a makon da ya gabata ne Ahmad Shahid, babban mai tsara rahotanni kan kare hakkokin bil’adama na MDD ya fitar da wani sabon rahoto maras tushe kan abin da ya kira take hakkokin bil’adama da ake yi a Iran inda ya ce yanayin take hakkokin bil’adaman a Iran sai kara muni yake yi.

 

A cikin wannan rahoton na sa, Ahmad Shahid ya sake nanata abubuwan da ya sha fadi irin su take hakkokin mabiya ‘yan tsirarrun addinai; zartar da hukumcin kisa kan mutanen da aka same su da laifuffukan da suke da alaka da fasa kwabrin muggan kwayoyi;, amfani da azabtarwa da tilasci wajen neman bayanai daga wajen mutane da ake tsare da su, zartar da hukumcin kisa ba tare da laifi na gaskiya ba da dai sauran abubuwan da ya fadi wadanda babu wata gaskiya ko tushe cikin hakan.

 

Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan mutumin ya ke shirya irin wadannan rahotanni kan Iran da ba su dogara da wani ingantaccen tushe ba, face dai dogaro da wasu majiyoyi na makiya da masu tsananin adawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran din tun farkon kafa ta.

 

Yayin da yake mayar da martani ga wannan rahoton, babban sakataren hukumar kula da hakkokin bil’adama na ma’aikatar shari’a ta Iran Dakta Muhammad Jawad Larijani yayi kakkausar suka ga wannan rahoton inda yace wannan rahoto dai ya saba wa doka kuma ba shi da wata kima a ido ta dokoki.

 

Har ila yau Dakta Larijani ya ce manufar irin wadannan rahotanni ita ce haifar da wani yanayi na rashin fahimtar juna a cikin wannan majalisa ta kare hakkokin bil’adama wanda aka shirya za ta dinga dubi cikin lamurran da ya shafi hakkokin bil’adama a Iran a lokaci lokaci.

 

---------------------------------------/

 

END

Add comment


Security code
Refresh