An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 31 January 2016 05:21

Suratul Naml Aya Ta 89-93 (Kashi Na 694)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 89 da kuma ta 90 a cikin suratul Namli:

 

مَن جَاء بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ خَيْرٌ مِّنْهَا وَهُم مِّن فَزَعٍ يَوْمَئِذٍ آمِنُونَ

 

89-Duk  wadanda suka zo da kyakkyawan aiki,to suna da lada fiye da shi,kuma su amintattu ne daga firgitar wannan ranar.

 

وَمَن جَاء بِالسَّيِّئَةِ فَكُبَّتْ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

 

90-Wadanda kuwa suka zo  da mummunan aiki,to an kifar da fuskokinsu cikin wuta,to ba za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa.

A cikin shirin da ya gabata ayoyin da muka saurara na bayani ne kan karshen wannan duniya da rayuwa a cikin da ranar tashin kiyama. To wadannan ayoyi da muka saurara yanzu  na bayani ne kan yanayi na hisahi  da sakamako ayyukan da muka aika da kuma azabar da ke jiranmu idan mun aikata sabo  a wannan rana ta kiyama  da cewa: ilimi da hikimar Allah mahalicci  ta sanya kowne mutum da ya rayu a wannan duniya zai amsa abin da ya aikata saboda Allah Madaukakin sarki ya bawa kowa ne daya daga cikin mu hankali da zabi  da niyar aikatawa da zabin aikin da zai aikata . Kuma a gaskiya ba dukan aikin da muka aikata za mu ga sakamakonsa a wannan duniya saboda ita wannan duniya ba ta da karfi da ikon amsawa  da sakawa kowa aikin da ya aikata a cikinta ba amma ita lahira tana da wannan karfi da iko da lokacin da bay a karewa  da fadin guri da ya dace da kowa  kowa zai iya ganin sakamakon aiki da ya aikata  ko alheri ko lala.

Karkashin wannan ayar duk wanda ya aikata aikin alheri zai ga sakamakonsa na alheri  amma da sharadin tsarkin niya  ba ta hanyar nuna kai da girman kai da riya ba don wannan dabi’;a na rusa aikin alheri duniya da lahira.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko: abin da yafi aikata alheri muhimmanci shi ne kare aikin alheri daga riya  da jiji da kai da ke rusa ayyukan alheri tun a wannan dunya.

Na biyu: kyauta da sakayyar  da Allah key i mana kan aikin alher tafi aikata alheri daukaka da binkasa da yawa don falalarsa amma azaba daidai aikin da mutum ya aiakata ne

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 91 da 92:

 

إِنَّمَا أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ رَبَّ هَذِهِ الْبَلْدَةِ الَّذِي حَرَّمَهَا وَلَهُ كُلُّ شَيْءٍ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ

 

91-Ka ce da su: Ni dai an umarce ni ne da kawai da in bauta wa Ubangijin wannan garin na makka Wanda ya Mayar da shi mai alfarma,Kuma komai da komai nasa ne,kuma an umarce ni da in zama cikin Musulmi.

 

وَأَنْ أَتْلُوَ الْقُرْآنَ فَمَنِ اهْتَدَى فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ وَمَن ضَلَّ فَقُلْ إِنَّمَا أَنَا مِنَ الْمُنذِرِينَ

 

92-An kuma umarce ni da in  karanta Alkur’ani,sannan duk wanda ya shiriya,to ya shiriya ne don amfannin kansa,wanda kuwa ya bace s aka ce da shi: Da ma ni ina cikin masu gargadi ne kawai.

Wadannan ayoyi da ayar da za mu saurara a nan gaba gadan  karshen ayoyin da suka zo ne a cikin wannan sura ta Namli da kuma suke bayani kan bayani na karshe da manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa yayi  da Mushrikan makka cewa idan ba ku daina bautawa gomaka ba to ku sani ni na sabke nauyin da aka daura mani na isar da sakon allah da yi maku kashedi da galgadi dari bisa dari. Amma kun bijire cikin zabin da kuke da shi kuma kuna da zabin daya daga cikin hanyoyi biyu ko ku bi da zabar sakon Allan  da samin tsira da aminci ko kuma ku zabi hanyar tabewa da bijirewa da fadawa tarkon shaidan da bata. Kuma ku sani duk wnayar da kuka zabe akwai sakayya ko ta alheri ko ta lala kuma kar ku yi zaton idan kuka yi imani zan samu wani abu ko idan kuka kafirce wani abu zai same ni. Ni na isar da sakon da aka turo ni  da bin umarninsa amma a maimakon ku bautawa Allah kun gammace ku bautawa gumakan da kuka sassaka daga itace da duwatsu  da kuka tara a kewayen dakin Allah da sauran gurare a fadin birnin Makka.

Wadannan ayoyi na nuni da matsayin manzo guda biyu na farko nauyin isar da sako na kadaita Allah da bauta  da bin umarnin Allah  sai kuma na biyu matsayinsa kamar na sauran musulmi  isar da sakon Allah ga mutane da galgadinsu ba kamar mahukumta da sarakuna ba da shugabanni bas u bada umarnin a yi ko ana so ko ba a so dole mutane su aikata. Addinin musulunci da manzonsa sun nuna mana da koyar da mu hanya mai kyau ta zabi da daukan nauyi na koyar da sauran musulmi hukumce-hukumce na addini.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko: Manzonni masu bin umarnin Allah ne dari bisa dari ,babu wani abu da suke fadi sai abin da Allah ya umarce su haka bas u wani aiki da sai wanda ya umarce su da neman yardarsa.

Na biyu:Nauyin manzonni isar da sakon Allah da addinin Allah zuwa ga mutane amma amincewa ko kafircewa ya ragewa mutanan yin imani ko kafirci ya ragewa kowa ne mutum ne ba waninsa ba.

Na uku:Mutane muna cikin gafala ta tunawa da Allah Mahaliccinmu don haka nauyi ne na jagororin addini na fadakar da mu da nuna mama munin aikin banna da tanadin da aka yi mana .

*****************MUSIC***********

Masu saurare daga karshe za mu saurari karatun aya ta 93 kuma aya ta karshe a cikin jerin ayoyin da ke cikin wannan sura ta Namli:

 

 وَقُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمْ آيَاتِهِ فَتَعْرِفُونَهَا وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ 

 

93- Ka kuma ce: Dukkan yabo ya tabbata ga Allah: ba da dadewa ba zai nuna muku ayoyinsa,za kuma ku san su ,Ubangijinka kuma ba marafkani ba ne daga abin da kuke aikatawa.

Wannan it ace aya ta karshe a cikin wannan sura ta Namli da kuma ta rufe surar da yin godiya da Allah madaukakin sarki wanda yayi mana ni’imar kur’ani  mai girma  da ke shiryar da mutum  zuwa ga Allah da hanya maidaiciya bayan haka ya huwace mana da manzo mai girma da daraja da koyar da mu  da kuma damuwa da dare da rana  kan tunanin yadda zai isar da mu zuwa ga sa’ada ta karshe da ci gaba da yin riko da tafarkin Allah.

Ci gaban ayar na cewa: a nan gaba za mu gani da fahimtar ilimi da kudurar Allah  da kuma hikimarsa kuma hatta a zarra daga cikin halittun Allah za mu ga wannan alama  kamar yadda za mu ga hakan a cikin babbar halittarsa a wannan duniya da sauran duniyoyin da suke nesa da mu a sammai da kassai . Kuma kowa da fahimtar da yake da ita da lura da lamura daidai da fanninsa  kamar yadda likita  mai yin fida da fasa cikin mutum  yana ganin abubuwa na al’ajabi da ilimi haka lamarin yake a cikin kwalluwa da sauran gabobobi da gangar jikin mutum da sauran halittu.Idan  wannan duniya halittar ta aka yi  to ya kamata mu sani duk wani abu da muka gani a cikinta na nuni da mahaliccin wannan duniya da abin da ke cikinta idan kuwa muna tunani wannan duniya ta samar da kanta haka kwacam  ba wani burin a halittarta  to za mu gafala da sanin Mahalicci a cikin tunani da ayyukanmu da yin tasiri a rayuwarmu.

A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko: Sabkar da kur’ani da aiko da manzo mai girma ni’imomi ne biyu masu girma   da dole mu godewa Allah.

Na biyu: zuwa yanzu duk ni’imomin  da ayoyin Allah da muka gani wani bangare ne na dinbin ni’imon Allah a kowace rana za mu kara samin ilimi da binkasarsa da ganin ayoyin Allah  sabbi da kara sanin karfi da kudura da hikimar Allah a fili.

Na uku: kara mana dama da lokaci bay a nufin Allah ya gafala da  mu ne ba saboda Allah  masani da ilimi ne kan komi da kowa da ayyukan da muke aikatawa da sa ido kan mu a kullum  kuma wannan karkshin kulawarsa ne.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh