An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 31 January 2016 05:17

Suratul Naml Aya Ta 86-88 (Kashi Na 693)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 86 a cikin suratul Namli:

 

 أَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا اللَّيْلَ لِيَسْكُنُوا فِيهِ وَالنَّهَارَ مُبْصِرًا إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

 

86-Yanzu ba sa gani cewa: Mu Muka samar da dare don su nutsu a cikinsa ,da kuma rana mai haskakawa don su yi harka? Hakika a game da wannan lallai akwai ayoyi ga mutanen da suke ba da gaskiya.

A cikin ayoyin da suka gabata sun yi nuni da Magana kanranar tashin kiyama da kuma yadda kafirai da mushrikai suka musanta wannan rana kuma duk da bayani gamsasseh bayyananne sun ci gaba da yin riko da wannan tunani  gurbatacce na karyata ranar tashin kiyama to wannan ayar da muka saurara na bayani da nuni kana bin da yake a fili karara kan kudurar Allah da cewa;  Shin zuwa yanzu kun lura da wannan lamari cewa: da a ce haske da  da tsafin rana ya ci gaba  ta yaya za mu samu nucuwa da hutu da kwanciyar hankali a rayuwa? Ko kuma idan dare zai ci gaba har abada  ta yaya za mu yi aiki da jin dadin rayuwa? Kuma ta yaya tsirre da itatuwa za su ci gaba da binkasa. Shin kun yi tunani da nazari  kan yadda wannan duniya ke kewaya kanta a cikin awa 24  ba tare da an dagula maku ayyukanku da barci da hutu da kuke bukata  komi yana tafiya cikin tsari da kwarewa kuma bah aka kwacam wannan duniya ta sami kanta ba. A yau an ci gaban ilimi da gano cewa  duhun dare  yana samar da kwanciyar hankali da zucciyar mutum da kara samar da nucuwa ga mutum.Kur’ani ta hanyar maimaita irin wadannan ayoyi na ilmantar da mutum hanyoyi na ilimi da fahimatar gaskiya da kara yin imani da kudura da hikimar mahalicci kuma mu kara yin imani da ranar kiyama.

A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:sassabawar dare da rana na nuni da ilimi da tsari da hikimar mahaliccin wannan duniya kuma dole mu zurfafa tunani da nazari kan haka a rayuwarmu.

Na biyu: ambaton barci da farkawa a tsakanin ayar da ke bayani kan kiyama domin fadakar da mu ne da fahimtar mutuwa da rayuwa.

Na uku: tsarin rayuwar mutum dole ya kasance da yin daidai da tsari na dabi’a dare don hutawa  da rana kuwa lokaci ne na aiki idan mutum ya sabawa wannan tsari na iya fuskantar matsala a rayuwa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 87:

 

وَيَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَفَزِعَ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ إِلَّا مَن شَاء اللَّهُ وَكُلٌّ أَتَوْهُ دَاخِرِينَ

 

87-Ka tuna kuma ranar da za busa kaho sai duk mahalukin da yake cikin sammai da wanda yake cikin kassai ya halaka,sai dai wanda Allah ya toge.Kuma gaba dayansu za su zo masa suna masa mika wuya.

Wannan ayar ta sake yin bayani ne kan tashin kiyama  da busa kawo da yananin da za mu samu kanmu cikinsa.Sau biyu ne dai za a busa kawo na farko a karshen rayuwa a wannan duniya inda kowa zai mutu sai mahalicci rayayye dawwamamme ,busa kaho kuwa na biyu a ranar hisabi da sake rayar da mu bayan mutuwa hatta su kansu mala’iku bas u kebantu da mu mutane ba za sum utu da sake tayar da su.A wannan rana kowa yana cikin tsaro da firgita ne  da taruwa a gurin mahalicci cikin kaskantarwa da firgita da tsoro.Kamar yadda wannan ayar ke yin bayani bayan tayar da mu bayan mutuwa a ranar tashin kiyama kowa na cikin tsoro da firgita sai wadanda suka aikata ayyukan alheri da tsarkakae aikinsu da kuma mala’ikun Allah  da suke cikin aminci da tsaro karkashin falalar Allah.

A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko: Karkashin ayoyin kur’anikomi da ke rayuwa a wannan duniya bayan busa kawo da kara mai firgitarwa zai mutu . Allah ne kawai zai yi saura a wannan duniya .

Na biyu:a cikin sammai ma kamar a doran kasa da karkashin kasa akwai halittu da ke rayuwa su ma za sum utu da sake tarayar da su a ranar tashin kiyama.

Na uku: mutuwa ba ta kebantu da mutane su kadai ba ta hada da sauran halittu  kamar mala’iku.

*****************MUSIC**********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 88 a cikin wannan sura ta Nami:

 

وَتَرَى الْجِبَالَ تَحْسَبُهَا جَامِدَةً وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ السَّحَابِ صُنْعَ اللَّهِ الَّذِي أَتْقَنَ كُلَّ شَيْءٍ إِنَّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَفْعَلُونَ 

 

88-Kuma kana ganin duwatsu ka zaci  a tsaye suke cak ,alhali kuwa su suna tafiya ne irin tafiyar giragizai.Aikin Allah ke nan Wanda Ya kyautata halittar kowane irin abu.Haklika Shi Masanin abin da kuke aikatawa ne.

Wannan ayar ma tana nuni ne da daya daga cikin abubuwan al’ajabi  na halitta da cewa;a ganinku duwatsu a guri daya suke ko  alhali su ma kamar gajimare suna tafiya cikin tsari ba tare da hayaniya da kara ba kuma wannan na nuni da karfin kudura da hikimar mahaliccin wannan duniya wanda ya tsara wannan duniyar da ke juyawa  cikin sauri ba tare da mutum ya fahimci hakan ba  ko haddasa wa halittun da ke cikinta wata matsala  ba . a tsawon tari shekaru da dama mutane hatta masana sun yi zaton wannan duniya tana guri guda ne rana da wata ne ke juyawa a bayanta. Amman yanzu sun gane kuskuran su da karamcin iliminsu.

Daga wannan aya za mu ilmantu da daukan darasin abubuwa hudu:

Na farko:tafiya da motsin duwatsu yana tafiya ne kafada da kafada da tafiyar wannan duniya.

Na biyu: Abin mamaki ,kur’ani kimanin sherkaru dubu biyu da suka gabata ya bada labarin wannan dunya na juyawa abin da masana suka gagara ganowa ta hanyar ilimi  sai a yan shekarun baya bayan nan.

Na uku:Tafiyar duwatsu da tsonuka cikin sauri ne tamkar tafiyar gajimare kuma cikin ikon Allah mu sauran halittu ba mu fuskantar wata matsala da fahimtar hakan.

Na hudu:Dukan halittun Allah an halicce su ne cikin tsari da kamala babu wani da aka yiwa kobro a cikin halittarsa.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh