An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 31 January 2016 05:10

Suratul Naml Aya Ta 82-85 (Kashi Na 692)

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka Mai Sanda, inda mukan kawo muku bayani dangane ayoyin kur’ani mai tsarki, da kuma abubuwan da suke koyar da mu, har yanzu muna a cikin surat Naml, inda  a yau za mu kawo muku bayani kan ayoyi na 82 zuwa 85 a  cikin surat Naml, da fatan za a kasance tare da mu.

 

……………………………………………

To yanzu sai a saurari karatun ayoyi na 82, da kuma 83 daga surat Naml:

 

 وَإِذَا وَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ أَخْرَجْنَا لَهُمْ دَابَّةً مِّنَ الْأَرْضِ تُكَلِّمُهُمْ أَنَّ النَّاسَ كَانُوا بِآيَاتِنَا لَا يُوقِنُونَ

 

82-Kuma aidan lokacin da aka alkawarta musu ya cika ,to z Mu fito musu da wata dabba daga kasa da za ta rika fada musu cewa: Lallai mutane sun zam bas a sakanakancewa da ayoyinmu.

 

وَيَوْمَ نَحْشُرُ مِن كُلِّ أُمَّةٍ فَوْجًا مِّمَّن يُكَذِّبُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ يُوزَعُونَ

 

83-Kuma ka tuna ranar da za Mu tattara jama’ mai yawa daga wadanda suke karyata ayoyinmu na kowacce al’umma ,sannan za a cakuda su.

////////////////////////////

Wadannan ayoyi ci gaban ayoyin da suka gabace da suke baya nai kan kiyama, a karshen duniya Allah zai tayar da wasu mutane bayan sun mutu zai fito da su daga cikin kasa a matsayin aya, amma duk da haka wadanda suka yi nisa  a cikin musu da ayoyin Allah da tsunduma a cikin tafarkin shedan, duk da hakan ba a shirye suke su bi tafarkin shiriya.

Batun tayar da mutane bayan sun mutu a duniya ya zo a wurare daban-daban a cikin kur’ani, daga ciki har da kisser wani annabi da ya bukaci Allah ya nuna masa yanayin yadda tashin kiyama zai kasance, sai aka karbi ransa na tsawon shekaru dari, sa’annan aka sake dawo masa da ransa, aya ta 259 a cikin suratul Bakara ta yi bayani kan hakan.

Haka nan kuma kisser wani mutum daga cikin Bani Isra’ila da aka kashe a lokacin annabi Musa (AS) inda Allah ya umarci Bani Isra’ila da su yanka saniya kuma su buge mamacin da wani bangaren naman saniyar, ta haka kuma Allah ya tayar da mutumin bayan ya mutu, aya ta 73 a cikin suratul Bakara ta yi bayani kan hakan.

Haka nan kuma tayar da mutane bayan sun mutu yana daya daga cikin mu’ujizozi da annabi Isa (AS) ya zo da su domin shiryar da mutane zuwa ga tafarkin gaskiya, kamar yadda ayoyin alkur’ani suka tabbatar da hakan, kamar yadda ayoyi na 243 da kuma na 56 a cikin suratul bakara suka bayyana hakan a fili, kan cewa a cikin al’ummomin  da suka gabata akwai mutanen da Allah ya tayar bayan sun mutu.

Wadannan ayoyi suna yin ishara ne zuwa ga batun ‘Raja’a’ wao dawowar wasu mutane zuwa gidan duniya bayan sun mutu, baya ga ayoyin kur’ani akwai ruwayoyi ingantattu da suka zo kan hakan, duk kuwa da cewa an yi amfani da Kalmar dabba a cikin ayar, amma kuma hakan baya kore cewa wasu mutane ne Allah zai tayar, domin kuwa Allah ya yi amfani da Kalmar dabba a cikin aya ta 22 a surat Anfal, inda ma’anar ayar ke ishara da cewa; mafi sharrin dabbobi a wurin Allah su ne wadanda suka kasance kurame bebaye kuma ba su hankalta. Wato wadanda suka ki bin tafarkin shiriya, Allah ya kira su da mafi sharrin dabbobi, alhali kuwa mutane ne.

Akwai ruwayoyi da ke cewa daga cikin mutanen da za a sake dawo da su akwai mutanen da suka aikata laifuka masu girma, da suka kai kololuwa wajen zalunci kan bayin Allah, inda za su dawo su fara fuskantar hukunci a nan duniya a karkashin daular Imam Mahdi (AS) kafin hukuncin na karshe a gaban kotun Allah a ranar kiyama. Haka nan kuma wasu daga cikin salihan bayi za su dawo domin zama daga cikin masu taimakonsa wajen kafa daular adalci a duniya.

A cikin wadannan ayoyi za mu koyi darussa kamar haka:

1 – Allah yana tayar da mutane a duniya bayan sun mutu bisa wata hikima tasa.

2 – Zalunci da mulkin kama karya zai zo karshe a duniya baki daya, kuma adalci a karkashin daular imani zai mamaye duniya.

 

Yanzu kuma sai a saurari karatun ayoyi na 84 da 85 daga surat Naml:

 

حَتَّى إِذَا جَاؤُوا قَالَ أَكَذَّبْتُم بِآيَاتِي وَلَمْ تُحِيطُوا بِهَا عِلْمًا أَمَّاذَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

 

84-Har yayin da suka zo sannan Allah Y ace da su : Yanzu ku kuka karyata ayoyina,alhali kuwa ba ku tantance da saninsu ba? Ko kuwa me kuka zamanto kuna aikatawa ne a duniya?.

 

وَوَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِم بِمَا ظَلَمُوا فَهُمْ لَا يَنطِقُونَ 

 

85-Kuma abin da aka alkawarta musu ne azaba ya fada musu,saboda kafurcinsu,sannan ba za su iya tankawa ba.

 

/////////////////////////////////////

 

Ayoyin da suka gabata sun yi ishara a kan batun dawo da mutanen da suka shahara da kafirci , fajirci da kuma zalunci, kamar yadda kuma za a dawo da mutanen manyan salihan bayi.

Duk da irin ayoyi da Allah ya yi ishara da su, da kuma almomi da suke tabbatar da samuwarsa, da ku mu’ujiza da annabawan Allah suke bayyanawa da ke tabbatar da gaskiyarsu, amma wadanda suka yi nisa cikin bata wannan ba zai iya canja su daga kan matsayinsu na kafirce ma ayoyin Allah da karyata manzanni ba.

Allah madaukakin sarki yana ba su domin su aikata abin da suka ga dama, amma kuma zai kama su da hujja, ranar da uzurinsu ba zai amfanar da su da komai ba.

Daga wadannan ayoyi za mu iya daukar darussa kamar haka:

1 – Kafin tashin kiyama akwai “Raj’a”

2 – Kada mu karyata duk abin da ya zo mana kafin sanin hujja a kan hakan.

3 – Masu zalunci suna da sakamako na abin da suka aikata da kuma karyata ayoyin ubangiji da mazanninsa.

 

Da wannn muka kawo karshen shirin na yau, sai Allah ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani jigon, kafin lokacin nake yi fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah. 

Add comment


Security code
Refresh