An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 31 January 2016 04:59

Suratul Naml Aya Ta 76-81 (Kashi Na 691)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 76 zuwa 79 a cikin suratul Namli:

 

إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَقُصُّ عَلَى بَنِي إِسْرَائِيلَ أَكْثَرَ الَّذِي هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ 

76-Hakika wannan Alkur’ani yana labarta wa Bani-Israila mafi yawan abin da suke sabani a cikinsa.

 

وَإِنَّهُ لَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ

 

77-Hakika kuma shi Alkur’ani lallai shiriya ne kuma rahama ce ga muminai.

 

 إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُم بِحُكْمِهِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ

78-Lallai Ubangijinka zai yi shari’a a tsakaninsu da hukuncinsa. Shi kuwa Mabuwayi ne Masani.

 

فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ إِنَّكَ عَلَى الْحَقِّ الْمُبِينِ

 

79-To ka dogara ga allah ,Lallai kai kana kan gaskiya mabayyaniya.

A cikin shirin da ya gabata ayoyin da muka saurara na bayani da Magana kai tsaye da mushrikai  da ke musanta ranar tashin kiyama ta hanyoyi daban daban na kawo dalilai na rashin hankali da fakewa da izgili kan yuyuwar tayar da wadanda suka mutu da azabtar da wadanda suka aikata sabo da kuma sakawa wadanda suka yi imani da aikin alheri sakamako na alheri da gidan aljanna.To wadannan ayoyi da muka saurara suna Magana ne kan yahudawa da ke zaune a yankin jazirar larabawa da kuma suka bijirewa kiran alkur’ani da karbar addinin musulunci.Yahudawa nada sabani kan Isa almasihu da imamin karshe da zai yantar da duniyar nan daga zaluncin karshen zamani da bayanansu ya zo a cikin attaura kamar yadda suke da sabani a tsakaninsu a cikin hukumce-hukumce na addini to wadannan ayoyi na cewa;idan kun amince kur’ani littafi ne sabkekke daga sama zai warware maku dukan sabanin da kuke da su a tsakaninku hatta canfe canfe da keke da su a tsakanin yahudawa da kiristoci bayan zuwan Annabin musa da Isa (AS) da kuka kirkiro. Abin da ya kamata ku fahimta addinin musulunci addini tsarkakekke ba a raba gurbatacciyar akida da son rai da wani abu da bai da ce ba da shi.Ci gaban ayar na Magana ne da manzon Rahama (SWA) da kuma mumunai da cewa: dangane da kiyayyar da ma’abuta littafi yahudawa da kiristoci ke nuna maku ku yi tawakkali da Allah da kuma ilimi da kudurarsa maras karewa da riko da hanyar Allah  kuma ku sani ku ne ke kan gaskiya kuma hanayr gaskiya it ace abin riko da ba ta katseyewa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko:falala da albarkar kur’ani magance matsala da sabanin tunani tun daga tushe ,kur’ani na samar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin dukan al’ummomi ba musulmi kadai ba har da sauran mabiya addinai.
Na Biyu:Hidaya babbar ni’ima ce da Allah yayi mana karakshin rahama da lutifinsa.

Na uku:Tawakkali da Allah daya daga cikin hanyar nasara ce ga mutum tare da rungumar hanyar gaskiya.

 

**************MUSIC*************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 80 da ta 81 a cikin wannan sura ta Namli:

 

 إِنَّكَ لَا تُسْمِعُ الْمَوْتَى وَلَا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاء إِذَا وَلَّوْا مُدْبِرِينَ

 

80- Hakika kai ba ka iya jiyar da matattu,ba kuma ka iya jiyar da bebaye kira lokacin da suka juya suna masu ba da baya.

 

 إِنَّكَ لَا تُسْمِعُ الْمَوْتَى وَلَا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاء إِذَا وَلَّوْا مُدْبِرِينَ

 

81-Kuma sannan kai ba za ka iya shiryar da makafi daga batansu ba, ba wanda kake iya jiyawa sai mai ba da gaskiya da ayoyinmu,sannan wadannan su ne Musulmi.

Ayoyin da suka gabata na cewa; gaskiya a fili take karara suma wadannan ayoyi da muka saurara sun bayyana cewa;masu adawa da addini da kur’ani  da dalilin karbar gaskiya ya samo tushe ne daga son rai da ya toshe zucciya da hankalinsu ba don ba za su iya karbar gaskiyar ba da yin imani da kur’anin ba. Duk wanda ke da bakar jayayya da kiyayya ido rufe da ta’assubanci da biyayya ta jahilci da tabewa. Ida nana gaya masu gaskiya da bayani na shiriya k ace tamkar ana gayawa gawa ce  da ba ta ji da amsawa ko kurman mutum da bay a ji  sais u ci gaba da yin riko da hanyar tabewa da bata.Ko makaho duk kiran da z aka yi masa ta baya baya gani to haka kafirai masu bakar kiyayya da addini da jayayya da manzon Rahama (SW) suke ba su sauraren gaskiya ko ganin gaskiya balantana su bita.

A fili yake duk mai son shiriyar Kur’ani da Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da farko dole na nuna da’a da kaskantar da kai wajen saurare da fahimtar gaskiya ,na biyu yin imani da abin da ayoyin kur’ani ke bayani kansu ma’ana duk wand aba a shirye yake ba ya gaskata ayoyi kur’ani idan ya fahimci gaskiya ba zai taba yin imani da Kur’ani ba. Dukan wadannan abubuwa nada alaka da ruhi da tunanin kowane mutum  kuma duk wanda yake da riko da kabilanci  ba a shirye yake bay a saurari gaskiya da yin imani da ita ko da ya saurara zai fake da wani abu maras tushe. Daga karshe rashin yin imanin kafirai da sakon annabwa da manzonnin Allah ba daga sako ne baa a yana tattare da jayayya da kiyayyarsu idan mutum ba a shirye yake ya karbi gaskiya komin abin da ka yi da shi ba zai fahimta da yin imani ba ,tamkar kwan fitar da yam utu ne idan ka sanya shi a wutar lantarki ba zai bada haske ba har abada.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:rayuwa da mutu a mahangar kur’ani akwai ta zahiri da kuma ta ma’anawiya.Wanda yaki karbar gaskiya da yin imani da gaskiya tamkar macecce ne wanda kuma ya karbi gaskiya da aiki da ita rayayye ne kamar yadda wanda yayi shahada rayayye ne na rayuwa da samin arzikinsa a gurin Allah ko da a zahiri muna ganinsa a matsayin wanda ya mutu.

Na biyu:Kasancewa tare da kunne,da ido da hankali bas u wadatarwa abu mai muhimmanci  samin ruhim karba da aiki da gaskiya .Duk wanda ya rasa wannan ko ya saurara ba zai ba zai jib a ko ya gani ba zai gani ba.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh