An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 30 January 2016 13:20

Suratul Naml Aya Ta 64-69 (Kashi Na 689)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

**************MUSIC********

To madallah masu saurare za mu saurari karatun aya ta 64 a cikin suratul Namli:

 

أَمَّن يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ وَمَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاء وَالْأَرْضِ أَإِلَهٌ مَّعَ اللَّهِ قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ

 

64-Ko kuwa wane ne yake kagar halitta sannan ya dawo da ita bayan mutuwa,kuma wane ne yake arzuta ku ta sama da kasa? Shin wani sarki ne tare da Allah? K ace da su: Ku kawo dalilanku idan kun kasance masu gaskiya.

 

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda ayoyin kur’ani ke mika tambayoyi na hankali da zurfafa tunani kan mushrikai masu bautawa goma kan cewa abubuwan da suke bautawa sune suka fi ko Allah wanda ya halicci dukan halittu da ya hada sammai da kassai da dukan abubuwa masu rai da maras rai  karami da babba da kulak e kula da lamuransu? To wannan ayar da muka saurara ci gaban irin wadannan tambayoyi ne da tambayarsu shi abubuwan da kuke bautawa su ne suka fi ko kuwa Allah da bas hi da abokin tarayya wanda ya kadaita kuma ba wai kawai wanda ya halicci komi da kowa ba  har ila yau shi ne zai tarayar da kowa da komi a gobe kiyama da gurfana a gabansa kuwa Allah abin kadaitawa da bauta shi ne ke arzuta kowa da komi da ni’imtar da mu baki daya. Duk da wannan bayanai idan kun ci gaba da hassashen bayan Allah abin kadaitawa da bauta shi kadai ba tare da abokin taraya ba akwai wasu alloli da suka yi tarayya da shi a halitta da tafiyar da lamura da ke taimaka masa to ku kawo dalilanku na hankali da bayyanawa kowa ya gani da shaidawa.

Daya daga cikin abin da kur’ani ya kebanta da shi wajen fuskantar masu adawa da addinin Allah shi ne bukatar su kawo dalili da hujjoji na hankali amma tun ranar bayyanar manzon rahama (SWA) har duniya ta tashi ba za su kawo ba saboda bas u da wani dalili sai bakar jayayya da kiyayya kawai da izgili da barazana ga ma’abuta imani.

A cikinn wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko:A kullum mu rika fuskantar makiyanmu da dalili da adalci idan suka kawo hujja da dalili na hankali mu karba  ba bakar kiyayya ba wannan ita ce koyarwar addinin musulunci ta karba da aiki da dalilai da hujjoji na hankali.

Na biyu:Allah ya wadatar da mu arziki da duk wani abu da mutum ke bukata hada da ruwa ,iskar shakawa ,haske da ruwan sama da abincin da za su ci da kayan marmari da sauransu.

Yanzu loakaci ne na sauraren karatun aya ta 65 da ta 66:

 

قُل لَّا يَعْلَمُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ

 

65-Ka ce da su: duk wanda yake cikin sammai da kassai in ba Allah ba wanda ya san gaibu,su kuma bas u san lokacin da za a tashe su ba.

 

بَلِ ادَّارَكَ عِلْمُهُمْ فِي الْآخِرَةِ بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ مِّنْهَا بَلْ هُم مِّنْهَا عَمِونَ 

 

66-Shin iliminsu ya kai har ga sanin lahira ne? A’a ,su dai suna cikin kokwanto ne game da ita .A’a ,su dai makafi ne game da ita.

Mushrikan Makka ganin ba su da wani dalili na karyata ranar tashin kiyama  da rayuwa bayan mutuwa sai suka fito ta wata hanya da sabon salon a tambaya kamaar yadda kafirai suka tambayi manzonni da annabawan Allah (AS) cewa yaushe ne ranar tashin kiyama? Ganin manzonni da annabawa (AS) ba su amsa masu ba  sais u kara da cewa: ke nan kuma ba ku da tabbas kan abkuwar kiyama. To wadannan ayoyi da muka saurara su amsa masu wannan tambaya  da fakewar da makiya kafirai da mushrikai suke yi da cewa; wasu lamura sun kebanta da Allah shi kadai hatta mala’iku da manzonni  ba su da masaniya kan su amma kuma rashin sanin lokaci da ranar abkuwar mai abkuwa ba dalili ba ne na rashin abkuwar mai abkuwa ko wani lamari da zai abku.Kamar yadda babu wani mutum da zai san ranar da zai zo duniya ko ranar da zai mutu amma kowa yayi imani da tabbacin zai mutu da barin wannan duniya wata rana mai zuwa babu makawa da hanyar hana abkuwar hakan. To abkuwar kiyama ko badade ko bajima sai ta abku tabbas ko mu so ku muna kiyayya da hakan kuma babu wani da ya san lokacin abkuwar kiyama sai allah masani mabuwayi mai hikima da ya boyewa kansa sani  bugu da kari rashin sani da jahilcinmu ba dalili ba ne na karyatawa ko shakku kan ranar kiyama.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko: Haddasa shaku da kokwanto a cikin abubuwan akida na addini daya daga cikin shiri da tsarin makiya masu adawa da addini da karbar gaskiya kamar yadda suke sa shakku kan abkuwar ranar tashin kiyama sai mu amsa masu cikin sauki da hankali da dalilai na hankali.

Na biyu:Imani da kiyama da tayar da mu a wannan rana yana daga cikin abubuwa na gaibi da ba za a iya ganinsu ko ji ko shafaru ba sai dai fahimta da yarda ta hanyar aiki da hankali da dalilai da hujjuji na hankali.

******************MUSIC************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 67 zuwa aya ta 69:

 

وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَئِذَا كُنَّا تُرَابًا وَآبَاؤُنَا أَئِنَّا لَمُخْرَجُونَ

 

67-Wadanda suka kafirta ,kuma suka ce :Yanzu bayan mun zama kasa mu da iyayenmu,ashe za a sake fito da mu?

 

لَقَدْ وُعِدْنَا هَذَا نَحْنُ وَآبَاؤُنَا مِن قَبْلُ إِنْ هَذَا إِلَّا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ

 

68-Hakika an yi mana alkawarin irin wannan mu da iyayenmu tun da can,wannan ba komai ba ne face tatsuniyoyin  mutanen da.

 

قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ

 

69-Ka ce da su : ku yi tafiya a cikin kasa za ku ga yadda karshen kafurai ya kasance.

Ci gaban ayoyi bayan da mushrikai da kafirai suka sanya shakku da kokwato kan ranar tashin kiyama saboda manzonni bas u amsa masu tambayarsu ba kan ranar abkuwar kiyama to wadannan ayoyi na bayani ne cewa; bayan wannan shaku sai kuma suka ci gaba da tambayar cewa a tsawon tarihi manzonni n ace masu kiyama za ta zo  gashi uwaye da kakanninsu sum utu sun zama kasa da turba hatta bulbudin jikinsu ya bat aba komi kuma har yanzu wannan alkawali na abkuwar kiya ya kasa tabbata  bayan haka muma  za mu mutu mu zama turba babu abin da zai yi saura daga jikinmu kuma bayan haka k ace za a tayar da mu. To Allah y aba su amsa cikin sauki a bayyanai  a cikin wadannan ayoyi na kur’ani da cewa: da farko Allah ya halicce ku ne daga kasa kuma za ku koma zuwa cikin kasar don haka babu wani abu da zai hana Allah ya sake tayar da ku daga kasar a wata duniyar. Na biyu jayayya da bakar adawar da kuke yi da bayanin gaskiya na manzonni  shi ne dalili da kuka fada cikin azaba a wannan duniya kafin ranar kiyama kamar yadda sauran kafirai suka aikata a baya Wasu al’ummomin zamaninsu bai yi nisa da ku ba kuma sun rayu a kusa da inda kuke rayuwa me yasa ba za  ku yi nazari da daukan darasi kan mummunar makomarsu ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :

Na farko: Duk mai karanta kur’ani mai girma yana karanta tarihin makiya kafirai da yadda mummunar makomarsu ta kasance  a tsawon tarihi amma kash wasu cikin jahilci da rashin sani wasu kuma cikin ganganci na maimaita abin da suka aikata da tabewa.

Na biyu: Kur’ani na gayyatar mu zuwa ga  karanta tarihin mutanan da al’ummomin da suka gabata da yin bulaguron guraren da suka rayu a bangarori daban daban na duniya ta haka za mu dauki darasi da samin tsira.

Na uku:ajiyar abubuwan tarihi na taimakawa da amfanar al’ummomi masu zuwa.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ………………..

Add comment


Security code
Refresh