An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 30 January 2016 13:11

Suratul Naml Aya Ta 61-63 (Kashi Na 688)

Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu  dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

 

3**************MUSIC********

To madallah masu sauraren za mu bude shirin nay au da sauraren karatun aya ta 61 a cikin suratul Namli:

 

أَمَّن جَعَلَ الْأَرْضَ قَرَارًا وَجَعَلَ خِلَالَهَا أَنْهَارًا وَجَعَلَ لَهَا رَوَاسِيَ وَجَعَلَ بَيْنَ الْبَحْرَيْنِ حَاجِزًا أَإِلَهٌ مَّعَ اللَّهِ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ 

 

61-Ko kuwa wane ne ya sanya kasa wurin rayuwa,ya kuma sanya koramu a tsattsakinta,kuma ya sanya mata turaku,kana kuma ya sanya shamaki tsakanin kogunan nan biyu na ruwan dadi da na ruwan zartsi? Shin wani sarki ne tare da Allah? A’a yawancinsu dai bas a ganewa ne.

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda kur’ani mai girma  yayi mana bayani kan gurbacewar tunani a tabewar masu bautawa gumaka mushrikai inda Kur’ani ke tambayarsu a duk lokaci da wata ni’ima ko yanayi ya faru a wannan duniya ake tambayarsu gumakansu ne ko Allah abin kadaitawa da bauta ya halicce wannan? To wannan ayar da muka saurara ci gaban ayar da ta gabata a shirin da ya gabata ne da ke bayani kan abubuwa na zahirin rayuwa da yanayi a wannan duniya da hakan ke nufi da bayani kan hikima a kudurar Allah a cikin halittar wannan duniya da abubuwan da ke cikinta masu kyau da birgewa da cewa:Allah madaukakin sarki ya haliccin wannan duniya da muke rayuwa cikin nucuwa da tsari idan wata girgizar kasa da ambaliyar ruwa ta abku a wani lokaci ko a wani yanki na wannan duniya ko zaezayewar kasa don a fadakar da mu ne na  sani da fahimtar babbar ni’imar da Allah yayi mana ta kwanciyar hankali da nucuwa da sulhu. Duwatsu da tekuna da kogina da ruwa masu gudana masu dadin dandano da wasu masu gishiri da rayuwa cikin kyau da inganci da tsari da ci gaban ilimi da bunkasar  mutum a gefen teku da sauransu ,abin mamaki ne Mushrikai masu bautawa gumaka a maimakon su yi godiya da bautawa Allah shi kadai sais u hada shi da waninsa a bauta da tafiyar da wannan duniya ,to wannan Magana ta yi girma da muni. Kuma ya dace su yi tunani da nazari kan dacewa da hanya madaidaiciya.

A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:Rayuwa cikin sauki da nucuwa a wannan duniya da tsari ta kai hatta mutum yana zaton wannan duniya a tsaye take guri guda ba ta motsi alhali kuwa tana juyawa  da kuma kewaya rana cikin sauri amma cikin ikon Allah babu wani da ke ji ko fahimtar hakan.

Na biyu: Tushen kafirci da shirka akwai rashin nasi daa fahimta ta hakika wani lokaci kuma akwai ganganci da bakar jayayya da kin karbar gaskiya wani lokaci kuma akwai rashin sani don haka nauyi ne kan mu mu yada addini da fadakarwa  da haskaka masu tunani.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren aya ta 62:

 

أَمَّن يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاء الْأَرْضِ أَإِلَهٌ مَّعَ اللَّهِ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ

 

62- Ko kuwa wane ne yake amsa wa mabukaci lokacin da ya roke shi ,yake kuma yaye duk wani bala’I,yake kuma sanya ku halifofi a bayan kasa? Shin wani sarki ne tare da Allah?Kadan ne kwarai kuke wa’azantuwa.

Wannan ayar na bayani ne kan hanyar sanin Allah mahalicci a rayuwarmu ta yau da cewa; idan mutum ya fuskanci wata matsala da tsanani ko kana kokarin nucewa a cikin teku da hallaka z aka rika neman wanda zai cece ka da kubutar da kai da maida lamarinka baki daya dari bisa dari ga wanda ya halicce ka da neman taimakonsa? Shin wannan da zai taimaka maka gumaka ne da abubuwan da kuke bautawa ba Allah ba za su iya kubutar da ku ? Za su iya yaye maku wannan matsalar da bala’I tsakaninka da Allah z aka Ambato su kuma za su iya amsa maka  a wannan lokaci?

A wasu ayoyin na kur’ani sun yi nuni da imani da hakika da ke tare da duk wani mutum a doran kasa da nuni da cewa duk mutuman da ya samu kansa a cikin jirgin ruwa ko kwalokwalo sai ya fuskanci igiyar ruwa a tsakiyar teku da fuskantar hallaka a zahiri a gabansa babu wani abu da zai nemi taimakonsa da neman ya kubutar da shi face Allah abin kadaitawa da bauta.wasu masu bin zahirin rayuwa da masu adwa da addini bas u Ambato da neman taimakon Allah sai idan sun fada cikin matsala da tsanani sais u rungumi Allah da neman taimakonsa.Amma shi mutum mumuni a gaskiya ba wai sai yana cikin matsala da tsanani ba yake neman taimakon Allah a kullum a wannan rayuwa tunaninsa yana tare da mahaliccinsa da neman taimakonsa bay a sha’afa da Allah tamkar yaro karami da a kullum yana tare da ma’aifansa wato mammarsa da babansa da neman taimakonsu a lokacin bukatar hakan. Kuma ko shakka babu za su taimaka masa a cikin tsanani ko cikin wadata da walwala to Allah ya zarta haka a tsakaninsa da halittunsa  baki daya. Abin da muke neman taimakonsa da rungumarsa dari bisa dari kuma zai taimaka mana Shi ne Allah.

A cikin wannan aya zamu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:daga cikin hanyoyin sanin Allah akwai lokacin da mutum ya fuskanci matsala ko kunci a rayuwa yana komawa ga Allah.

Na biyu:Allah ya bawa mutum dama da ikon sarrafa wannan duniya wasu abubuwa a cikinta da amfanu da ni’imomin da ke cikin wannan duniya.

*****************MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 63 a cikin wannan sura ta Namli:

 

أَمَّن يَهْدِيكُمْ فِي ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَمَن يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ أَإِلَهٌ مَّعَ اللَّهِ تَعَالَى اللَّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ

 

63-Ko kuwa wane ne yake shiryar da ku a cikin duffan tudu da na kogi,kuma wane ne yake sako iska tana mai bushara gabanin saukar rahamarsa? Shin wani sarki ne tare da Allah? Allah ya daukaka daga abin da suke tara shi da shi.

Wannan ayar ci gaban ayar da ta gabata ce da ke fadakar da mu sani da ilmantar da mu Allah abin kadaitawa da bauta ta hanyar tambayoyi da cewa: a lokacin da muke cikin bulaguro a sarari ko a tekuna a cikin dare da  yaya muke mu gano hanya ? shin tarmamu ne ke taimaka mana sanin hanyoyi da haskaka mana to gumakai da ba su da rai da amfanar kansu da waninsu ne suka halitta ko Allah da ba shi misali ya halice su?.

Iska da ke tafiyar da gajimaredaga teku da isar da shi zuwa wani bangare ko yanki na wannan duniya da ake butar ruwan sama wani ne ya umarce su yin hakan  ba Allah ba ? Me yasa kuke bautawa gumaka maras amfani a maimakon Allah mai karfi da kudura da tafiyar da wannan duniya da abin da ke cikinta.

A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu;

Na farko:Duk wani abu da ke wannan duniya da tafiyar da lamarin yana hannun Allah mai hikima da kudura da tsari.

Na biyu:wani wani abu a wannan duniya da matsayinsa ko sunansa yayi daidai da sunan Allah Allah Shi ne sama da komi da kowa a wannan duniya da sauran duniyoyi.

Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin an yau a madadin dukan wadanda suka hada mana sauti da taimakawa a cikin shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shira kuma na gabatar na ke cewa wassalam ……………….

Add comment


Security code
Refresh